You are here: HomeAfricaBBC2024 01 10Article 1910588

BBC Hausa of Wednesday, 10 January 2024

Source: BBC

Alexander-Arnold zai yi jinyar makonni saboda rauni a gwiwa

Ɗan bayan Liverpool, Trent Alexander-Arnold Ɗan bayan Liverpool, Trent Alexander-Arnold

Ɗan bayan Liverpool, Trent Alexander-Arnold ya ji rauni a gwiwa, don haka zai yi jinyar tsawon makwanni.

Ɗan ƙwallon tawagar Ingilan, mai shekara 25, ya ji rauni ne a FA Cup karawar zagaye na uku da Liverpool ta fitar da Arsenal ranar Lahadi.

Don haka, ba zai buga wa Liveerpool wasan Carabao Cup a karawar daf da ƙarshe da Fulham ranar Laraba a Anfield ba.

Haka kuma ƙungiyar da Jurgen Klopp ke jan ragama za ta kara da Bournemouth a Premier League ranar 21 ga watan Janairun.

Daga nan Liverpool za ta ziyarci Craven Cottage, domin buga wasa na biyu a Carabao Cup kwana uku tsakani.

Sai kuma Liverpool ta je ta fafata a FA Cup, karawar zagaye na huɗu ko dai da Norwich City ko kuma da Bristol Rovers a ranar 27 ga watan Janairu.

Liverpool za dai ta kammala wasan ƙarshe a watan Janairu ne da karawa da Chelsea a Premier League ranar 31 ga watan Janairu.

Alexander-Arnold, wanda aka bai wa muƙamin mataimakin kyaftin ɗin Liverpool a bana ya buga karawa 25 a duk wasannin kulob ɗin, kuma ya ci ƙwallo biyu.

Tuni dai Liverpool ke buga wasanni ba tare da Mohamed Salah ba, wanda ya je buga wa Masar gasar kofin Afirka da za a fara 13 ga watan Janairu a Ivory Coast.

Shi kuwa Wataru Endo zai buga wa Japan Asia Cup da Qatar za ta karbi bakunci daga 14 ga watan Janairu.

Ana sa ran Andy Robertson da kuma Kostas Tsimikas za su koma yin atisaye a karshen wattan nan.

Har yanzzu Dominik Szoboszlai na jinya, yayin da kyaftin, Virgil van Dijk zai fuskanci Fulham ranar Laraba, bayan rashin lafiya da ya yi fama.

Liverpool tana matakin farko a teburin Premier League, sannan ta kai zagaye na biyu a Europa League.