You are here: HomeAfricaBBC2024 01 06Article 1908542

BBC Hausa of Saturday, 6 January 2024

Source: BBC

Barcelona ta gabatar da sabon ɗan wasanta Vitor Roque

Vitor Roque Vitor Roque

Barcelona ta gabatar da sabon ɗan kwallon tawagar Brazil, Vitor Roque da ta ɗauka a Janairun nan a gaban magoya bayanta ranar Juma'a.

Mai shekara 18 ya fara taka leda a Cruzeiro daga kakar 2021–2022 daga nan Athletico Paranaense ta ɗauke shi daga 2022–2024.

Ranar 12 ga watan Yulin 2023 Barcelona ta sanar da ɗaukar ɗan kwallon zuwa karshen kakar 2030/31.

Tuni Barcelona ta gindaya Yuro miliyan 500 ga duk ƙungiyar da ke son sayen ɗan wasan, idan yarjejeniyarsa ba ta kare ba.

Ranar 27 ɗan wasa Rogue ya je Barcelona inda aka auna koshin lafiyarsa daga nan ya gana da 'yan jarida, sannan aka ba shi riga mai lamba 19.

Ranar 4 ga watan Janairun 2023, Roque ya fara buga La Liga, wanda ya canji ɗan kwallo a karawar da Barcelona ta doke Las Palmas 2-1 ranar Alhamis.

Haka kuma ya fara yi wa Brazil wasa ranar 3 ga watan Maris karkashin koci, Ramon Menezes a wasan sada zumunta da Morocco.

Bayan da Barcelona ta gabatar da ɗan kwallon ranar Juma'a nan da nan ya shiga ya sauya kaya, yayi shigar kayan da Barcelona ke sawa da riga mai lamba tara.

Daga nan ya yi wasa da tamaula, sannan aka ɗauki hotuna don tunawa da tarihi.