You are here: HomeAfricaBBC2024 01 06Article 1908539

BBC Hausa of Saturday, 6 January 2024

Source: BBC

Brazil ta kori kocinta Fernando Diniz

Brazil ta raba gari da kociyanta, Fernando Diniz Brazil ta raba gari da kociyanta, Fernando Diniz

Brazil ta raba gari da kociyanta, Fernando Diniz yanzu tana neman wanda za ta bai wa aikin jan ragamar tawagar.

Diniz, wanda ya ya yi aikin kaka ɗaya ya ja ragamar wasa shida a fafatawar neman shiga gasar cin kofin duniya da cin karawa biyu da canjaras ɗaya da rashin nasara uku.

Brazil tana mataki na shida a teburin Kudancin Amurka a neman shiga gasar kofin duniya da za a yi a Amurka da Mexico da kuma Canada.

Diniz ya gudanar da aikin tare da na horar da Fluminense, wadda ta ɗauki Copa Libertadores.

Brazil ba ta da kocin din-din-din tun bayan gasar kofin duniya a 2022 a Qatar, bayan da Tite ya yi murabus, bayan da Croatia ta doke su a zagayen quarter finals.

Daga baya kociyan matasan tawagar ƴan ƙasa da shekara 20, Ramon Menezes ya karɓi aikin rikon kwarya daga baya Diniz ya maye gurbinsa.

Tun cikin watan Yuli aka yi ta jita-jitar cewar Carlo Ancelotti zai karɓi aikin horar da Brazil daga Diniz a bana - sai dai a watan jiya mai shekara 64 ya saka hannu kan ci gaba da jan ragamar Real Madrid har zuwa karshen watan Yunin 2026.