You are here: HomeAfricaBBC2024 01 06Article 1908560

BBC Hausa of Saturday, 6 January 2024

Source: BBC

'Dakatar da digirin Kwatano bai dace ba mun sha wuya mun yi karatunmu'

Hoton alama Hoton alama

Wasu 'yan Najeriya da ke karatu a Jamhuriyar Benin, sun ce matakin hukumomin ƙasar na dakatar da shaidar karatun digiri daga jami'o'in Benin da Togo, ba shi ne mafi dacewa da zai hana sayen takardun ilmi na bogi ba.

Sun yi kiran a gudanar da bincike, domin gwamnati ta san jami'o'in da ke sayar da digirin bogi.

Matuƙar kuma ba haka ba, in ji su, ɗumbin waɗanda ba su ji ba, ba su gani ba, za su cutu sanadin mummunar harƙallar wasu ta sayen abin da a baya-bayan nan ake kira 'digiri ɗan Kwatano' .

Wata ɗaliba, Alberty Oluwatoyosi da ke karatun aikin jarida a jami'ar Estam ta Benin, ta shaida wa BBC Pidgin cewa matakin dakatar da karɓar digirin Benin da Togo, ya sosa musu rai, ganin yadda aka yi wa dukkan jami'o'in ƙasashen kuɗin goro, lamarin da ka iya taɓa ƙimarsu.

Ta ƙara da cewa sun biya kuɗin makaranta, kuma suna raba dare suna karatu ka'in da na'in, don haka ba su cancanci wannan hukunci ba.

Oluwatoyosi ta ce ba ta damu da batun samun aiki nan gaba idan ta kammala karatu ba, ta yi imanin tana da basirar da za ta yi amfani wajen sama wa kanta madafa nan gaba a rayuwa.

Ta ce dakatartwar da gwamnati ta yi, ba shi ne maganin matsalar ba, maimakon hakan kamata ya yi a gudanar da bincike.

“Ina gab da kammalawa, na tafi bautar ƙasa, saboda iyayena suna fatan na yi hidima, amma tun da gwamnati ta dakatar da digirin irin nawa, ba lallai hakan ta samu ba, amma ina fatan za su ɗage wannan haramci.

“Ba sabon abu ba ne a ce jami'a na sayar da shaidar karatun digiri, kuma ba a Jamhuriyar Benin kawai ake yin hakan ba, ko jami'o'in Najeriya ana samun irin wannan badaƙala,” in ji Oluwatoyosi.

Ta ce ya dace a gudanar da bincike a Jamhuriyar Benin da Togo, domin kaucewa zaluntar 'yan ba-ruwanmu.

Shi ma wani ɗalibi mai suna Akerele Olawale, da ke karatu a tsangayar nazarin wasannin kwaikwayo a Jami'ar Benin, ya ce damuwarsa ta ƙaru saboda hakan zai shafi samun damarsa ta zuwa hidimar ƙasa a Najeriya, da kuma samun aikin yi.

Wannan al'amari dai, in Akerele ya dugunzuma shi, kuma har yana neman haddasa masa rashin lafiya.

"Damuwa za ta yi min yawa, kawai ina tunanin ta yadda zan samu aiki mai kyau. Na damu matuƙa," in ji shi.

"Ban taɓa ganin inda ake sayar da shaidar digiri ba, kuma jami'ar da na yi ba sa yin haka, ban taɓa ganin wanda ya yi ba."

Abin da ya sa Najeriya ta dakatar da digirin Kwatano

Tuni dai Najeriya ta bayyana dakatar da karɓar shaidar digiri daga ƙasashen Togo da Benin.

Ma'aikatar ilmi ta ƙasar ce ta fitar da wata sanarwa, wadda a ciki ta sanar da hakan ranar 2 ga watan Janairun 2024.

Sanarwar ta ce matakin ya zama dole, bayan wani ɗan jarida ya ɓad-da-kama inda ya sayi shaidar karatun digiri daga wata jami'a ta Benin a cikin mako shida, ba tare da ya taɓa tsallaka kan iyakar Najeriya ba.

A ƙa'ida dai ana shafe tsawon shekara huɗu ana karanta fannin da ɗan jaridar na Daily Nigerian ya saya ne, bisa tanadin manhajar ilmi.

Rahoton da jaridar Daily Nigerian ta wallafa ranar 30 ga watan Disamban 2023, mai taken ''Bankaɗa'', ya yi bayani dalla-dalla a kan yadda wakilinta ya samu takardar digiri a cikin mako shida, har ya samu damar tafiya aikin bautar ƙasa.

Rahoton dai ya tayar da ƙura sosai a Najeriya, lamarin da ya janyo aka fara nuna yatsa ga ɗaliban da suka yi karatun jami''o'i daga ƙasashen da ake yi wa kallon suna tafka almundahana.

"Daga nan kuma su yi amfani da takardun digirin wajen samun aiki,'' in ji sanarwar ma'aikatar ilmin Najeriya.

Ko mai digirin Benin da Togo zai iya zuwa hidimar ƙasa?

Sai dai waɗanda suka yi karatu a jami'o'in ƙasashen Benin da Togo sun nuna damuwa, musamman waɗanda ke daf da tafiya aikin hidimar ƙasa.

Tambayar da kowa ke yi, ita ce ko za su samu damar shiga aikin hidimar ƙasa, wanda ke ba da damar samun aikin yi a hukumomi da kamfanoni a Najeriya?

Sashen BBC Pigin ya miƙa wannan tambaya ga mai magana da yawun ma'aikatar Ilmi ta Najeriya, Benjamin Gong.

Ga kuma abin da ya shaida wa BBC "Ma'aikatar ilmi ta kafa wani kwamiti da zai yi bincike, da tantance waɗanda za su tafi aikin hidimar ƙasa wato NYSC, da binciken ƙwaƙwaf kan shaidar digirinsu".

"Kwamitin zai sa ido yadda ya dace domin kauce wa ganin an yi kitso da kwarkawata."

Ga waɗanda suka yi aikin hidimar ƙasar da takardun digirin bogi kuwa, Gong ya ce a ƙarkashin dokokin Najeriya, an yi tanadin cewa duk wanda ya ɗauke su aiki, amma daga bisani aka gano takardunsu na bogi ne to suna da damar korar irin waɗannan mutane daga aiki nan take.

"Dokar ta shafi ko ma a ina ɗalibi ya yi karatu, matuƙar dai shaidar digirinsa ta bogi ce. Don haka ko a Najeriya ne ko a wata ƙasar ne, kai ko ma a ina ne, matuƙar dai shaidar karatun bogi ce, to mutum zai rasa aikinsa.''

Gong ya ce abin da ɗaliban Najeriya ke yi bai dace ba, kasancewar yana zubar da ƙimar ƙasar a idon duniya.

" Kafin kowanne dalibi ya nemi gurbin karatu a jami'ar ƙasar waje, dole sai ya zo ma'aikatar ilimi domin tantance takardun karatunsu da buga hatimi.

Sannan alhakinmu ne duba ingancin jami'ar da za su je karatu, domin tabbatar da cewa gwamnati da ma'aikatar ilmin Najeriya sun amince da su.

Amma ba za su yi haka ba, sai sun je sun kammala bilinbituwa sun dawo sun je hidimar ƙasa, sannan suke zuwa nan ma'aikatar ilmi.''