You are here: HomeAfricaBBC2024 01 10Article 1910534

BBC Hausa of Wednesday, 10 January 2024

Source: BBC

Kotun koli za ta raba gardama a shari'a tsakanin Abba da Gawuna a ranar Juma'a

Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf da Nasiru Yusuf Gawuna na APC Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf da Nasiru Yusuf Gawuna na APC

Kotun koli a Najeriya ta sa ranar yanke hukunci kan zaben gwamnan Kano tsakanin Abba Kabir Yusuf na NNPP da kuma Nasiru Yusuf Gawuna na APC.

Sakon kotun da ya bayana a daren wannan Talatar na tabbatar da cewa za a yanke wannan hukunci ne a ranar Juma'a 12 ga watan Janairu.

Tun bayan daukaka wannan shari'a a gaban kotun koli da kammala sauraron korafin da kowanne ɓangare ya shigar ake ta dakon wannan rana.

Shari'ar Kano ta kasance abin da ke jan hankali inda mutane suka zura ido domin ganin yadda za ta kaya tsakanin ɓangarori jam'iyyun biyu.

Lauyoyin bangarorin biyu da BBC ta tattauna da su, Barrista Adamu Fagge na APC da kuma Barrister Bashir Tundun Wuzirci na NNPP, duk sun tabbatar da karban sakon kotu, da ranar yanke wannan hukunci.

Lauyoyin kowanne jam'iyya dai na da kyakyawan fata na nasara a wannan sharia'a da za ta kawo karshen gardama da jam'iyyun biyu suka shafe watanni suna yi a kan wannan shari'a.

Kafin a je gaban a kotun daga-ke-sai-Allah-ya-isa, an yi hukuncin kotunan biyu da suka suka soke nasarar NNPP a zaɓen gwamnan Kano na watan Maris tare da bai wa Nasiru Gawuna nasara a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan Kano.

An ga yadda 'yan siyasar suka fara rige-rige wajen gudanar da yanke-yanke da salloli don neman nasara a shari'ar ta kotun ƙoli.

Kazalika, 'yan siysar NNPP da na APC na jefa wa juna zargin bai wa kotuna cin hanci don a murɗa hukuncin ya dace da kowannensu, duk da cewa suna musantawa.

Babu abin da aka fi tattaunawa a kai tsakanin mutane a wuraren zama kamar yanayin siyasar da jiharsu ke ciki, inda wasu ke tausaya wa NNPP wasu kuma ke goyon APC.

Gwamna Abba Kabir Yusuf, da kotun ɗaukaka ƙara ta soke zaɓensa, ya ce har yanzu yana da ƙwarin gwiwar cewa Kotun Ƙolin Najeriya, za ta dawo masa da nasararsa.

Hakazalika bangaren Gawuna a ta bakin, Shugaban Jam’iyyar APC na Kano, Abdullahi Abbas, nada kyakyawan fatan za su dara a wannan shari'a ta karshe.