You are here: HomeAfricaBBC2024 01 06Article 1908554

BBC Hausa of Saturday, 6 January 2024

Source: BBC

Kotun Ƙolin Amurka za ta yanke hukunci kan takarar Donald Trump

Tsohon shugaban Amurka, Donald Trump Tsohon shugaban Amurka, Donald Trump

Kotun kolin Amurka ta amince ta yanke hukunci cewa ko ya dace a hana tsohon shugaban kasar Donald Trump tsayawa takarar shugaban kasar.

Jihohi biyu na Amurkar ne zuwa yanzu suka cire sunansa daga takardar zaben fid da da gwani, bisa dalilinsu na cewa a matsayinsa na mai tayar da zaune tsaye, kundin tsarin mulkin kasar ya haramta masa tsayawa takara.

A halin dake ciki kuma Shugaban Amurkar Joe Biden ya yi jawabin yakin neman zabensa na farko a shekaran nan, inda ya yi mummunar suka kan Donald Trump, yana mai gargadin cewa tsohon shugaban na son yin amfani da tashin hankalin siyasa don cimma burinsa.

Ana ganin wannan shari’a za ta iya kasancewa daya daga cikin mafiya daukar hankali da kasancewa zakaran-gwajin dafi a siyasance a tarihin kotun kolin Amurka.

Donald Trump ya garzaya gabanta ne domin ta yanke hukunci kan cewa ko ya cancanta ya tsaya takarar shugabancin kasar.

A watan da ya gabata ne jihohi biyu na kasar, Colorado da Maine, suka yanke hukuncin haramta wa tsohon shugaban na Amurka tsayawa takara a zaben fitar da gwani na jam’iyyarsa ta Republican.

A bisa tanadin kundin tsarin mulkin Amurka, duk wanda ya kasance dan tawaye ko ya yaki hukuma to ba zai rike wani mukami ba.

A kan hakan ne jami’an jihohin biyu suka ce ya haramta Trump ya nemi wani mukami saboda rawar da ya taka a kutsen da aka yi wa zauren majalisun dokokin Amurka shekara uku da ta wuce.

To amma jami’ai a wasu jihohin bas u yarda da hakan ba, suka kuma soko matakin hana shi takarar a matsayin wanda ya saba wa dumukuradiyya

Ana ganin hukuncin da kotun kolin za ta yanke kan wannan batu zai iya haifar da wasu batutuwan ga gwagwarmayar zaben shugaban kasar da za a yi a watan Nuwamba, kuma duk yadda ya kasance zai sa a zargi alkalan kotun da goyon bayan wani bangare.

Donald Trump ya kasance babban abin da Shugaba Biden ya mayar da hankali a kansa a jawabinsa na farko na yakin neman zabe na shekara.

A jawabin wanda ya gabatar a Pennsylvania, daya daga cikin jihohi mafiya muhimmanci a zaben shugaban kasar wadda kuma ya samu anasarca a 2020, ya yi gargadi na gaske kan hadarin da ya ce dumukuradiyyar Amurka na ciki saboda Trump wanda y ace zai yi wa dumukuradiyya karan-tsaye domin kawai ya samu mulki.

Biden ya yi jawabin ne a jajiberin shekara uku da kutsen da magoya bayan Trump suka yi wa zauren majalisun dokokin Amurka, Capitol, don neman sauya sakamakon zaben 2020.

Mista Biden ya ce ba za lamunta da tashin hankalin siyasa ba a Amurka inda ya ce:

''Gungun Trump ba masu zanga-zangar lumana ba ne, tarzoma ce, ‘yan tawaye ne, ba masu kishin kasaba ne. Ba su mutunta kundin tsarin mulki ba. Sun je ne domin su watsa tsarin mulki. Trump ba zai yi abin da Shugaban Amurka ya wajaba ya yi ba.''

Sai dai yayin da Shugaba Biden din ke kaddamar da yakin neman zabensa, alkaluman baya-bayan nan na kuriar jin ra’ayin jama’a ba abin da zai so ba ne domin kusan kashi 70 cikin dari na Amurkawa na ganin a shekara 81 ya yi tsufa ainun ya zama shugaban kasa.