You are here: HomeAfricaBBC2024 01 10Article 1910585

BBC Hausa of Wednesday, 10 January 2024

Source: BBC

Real Madrid za ta ɗauki Alphonso Davies daga Bayern Munich

Alphonso Davies Alphonso Davies

Real Madrid na shirin sayen ɗan ƙwallon tawagar Canada da Bayern Munich, Alphonso Davies a karshen kakar bana.

Davies, mai shekara 23, yana da ƙunshin yarjejeniyar da Bayern Munich da za ta kare a karshen watan Yulin 2025.

Wasa daya ne kacal bai yi wa Bayern Munich ba a Bundesliga, ya buga mata dukkan karawa shida a Champions League a kakar nan.

Kociyan Real Madrid, Carlo Ancelotti na amfani da ƴan wasa biyu a gurbin mai tsaron baya daga hagu, tsakanin Ferland Mendy mai shekara 28 da Fran Garcia mai shekara 24

A watan jiya Ancelotti ya saka hannu kan ci gaba da horar da Real Madrid zuwa Yunin 2026, duk da cewar tawagar Brazil ta yi zawarcinsa.

Kociyan ɗan kasar Italiya na kokarin hada ƴan wasan Real Madrid, domin kara karfin ƙungiyar, wadda ta ɗauki Copa del Rey kadai a bara.

Haka kuma Real Madrid na fatan ɗaukar ɗan ƙwallon Paris St-Germain, Kylian Mbappe, amma tafi son fara daukar Davies da fatan za ta cimma yarjejeniya da Bayern Munich, idan an kammala wasannin bana.

Kafin fara kakar nan, ƙungiyar Santiago Bernabeu ta ɗauki ɗan ƙwallon Ingila, Jude Bellingham, bayan da ta sayar da Karim Benzema ga Al-Ittihad ta Saudi Arabia.

Davies, wanda aka haifa a sansanin ƴan gudun hijira a Ghana a 2000, ya koma Bayern daga Vancouver Whitecaps a Janairun 2019.

Ya buga wa Bayern Munich wasa 176 da lashe kofi 13 har da na Bundesliga biyar da Champions League a 2020.

Davies ya fara buga wa Canada tamaula yana da shekara 16 da haihuwa, wanda kawo yanzu ya yi mata karawa 44 da cin kwallo 15.