You are here: HomeAfricaBBC2024 01 06Article 1908563

BBC Hausa of Saturday, 6 January 2024

Source: BBC

Yadda za ku inganta rayuwarku a 2024 a kimiyyance

Hoton alama Hoton alama

A yayin da aka shiga sabuwar shekara, za ka iya hakaito abubuwan da kake son cimmawa da matakin da kake son kai wa nan da wata 12 masu zuwa.

So dai mafi yawa daga cikinmu da muka kuduri cimma burikanmu a shekarar 2024, kafewa a kan burikan namu ne babbar matsala.

A shekarun da suka wuce, bincike ya nuna cewa kashi 17 zuwa 45 daga cikinmu kan watsar da aniyarsu cikin watan farko na sabuwar shekarar.

Inda mafi yawan mutane kan watsar da kudurorinsu a tsakiyar shekarar, kamar yadda wani bincike ya nuna. (Duk da cewa binciken baya-bayan nan da YouGov ya fitar ya nuna cewa Amurkawa sun fi kafiya kan kudurorinsu a shekarar da ta gabata, inda mutanen da suka watsar da kudurorinsu suka tsaya a kashi 16 kafin karshen shekarar).

Rashin kafiya kan kudurorin da muka kudurta kan haifar da abin da masana abi'ar an'adam suka kira da ''fatan karya na shekara''. A maimakon haka ya kamata mu mayar da hankali wajen kudurce burikan da za mu iya cimmasu.

Bincike ya nuna cewa burikan cimma wani abu, wanda yake na zahiri, kuma na musamman wadanda ake iya auna nasararsu, an fi cimma su fiye da wadanda ke muradin barin wata dabi'a ko wani abu da aka saba yinsa kamar shaye-shaye.

Daukara mataki game da abin da za ka mayar da hankali a kai, zai iya zama mai wahala.

Domin taimaka wa kanka wajen kudurce abin da za ka cimma a sabuwar shekara, ga wasu abubuwa bakwai da za ka mayar da hankali a kai a makon farko na sabuwar shekara.

Ranar farko: Mayar da hankali kan barci

Bayan bata daren farko na sabuwar shekara ana ta murna, yana da kyau ka mayar da hankalai wajen biyan bashin barcin da ka dauka a wannan dare.

A wannan lokaci na farkon sabuwar shekara ba a son barci ya ya fi karfinka, musamman a a lokacin nan na hunturu.

Masana kimiyya na cewa yana da kyau mu rika samun barci mai yawa a lokacin hunturu.

Bincike ya nuna cewa mutane kan furkanci sauyi a barcinsu saboda tasirin yanayi, ma'ana sukan bukaci lokacin hutu mai yawa a lokacin hunturu, fiye da kokacin bazara.

Wani bincike da ka gudanar a Jamus ya nuna cewa mutane kanyi barci a watan Disamba, kasa da sa'a guda kan yadda suke yinsa a watan Yuni.

Domin inganta barcinka a lokacin hunturu, ka kwanta da wuri, sannan ka kauce wa haske sa'a biyu kafin lokacin kwanciya, sannan ka duba wayarka kafin kwanciya barcin.

Binciken baya-bayan ya nuna cewa samun wadataccen lokacin barci zai taimaka mana wajen inganta lafiyarmu.

Rana ta biyu: mayar da hankali kan jikinmu

Idan kai mutum ne mai motsa jiki, to lokaci ya yi da zaka inganta shi tare da karfafa shi, musamman mutanen da ke motsa jikin ba tare da ma sun sani ba, kamar motsa giwwa da lankwasa 'yan yatsu da sauran abubuwa duk suna taimaka wa wajen kona maiko tare da rage damuwa.

A yayin da iskar hunturu ke kadawa, yana da kyau ka samu lokacin da za ka rika motsa jikinka, wanda zai taimaka wa lafiyarka tare da karfafa kwayoyin garkuwar jiki da kuma rage nauyi ta hanyar mayar da fararen kwayoyin halittar kitse zuwa ruwan kasa.

Haka kuma yana da kyau mu rika gwada tafiya da bai-bai. Domin tafiya da bvai-bai ya fi kona maiko a jikin mutum fiye da tafiya ta gaba, sannan kuma yakan karfafa tsokokin dan'dam na bayansa.

Ana kuma bukatar mutanen da ke da matsalar gwiwwa da su rika gwada irin tafiyar, saboda tana rage matsalolin gwiwwa, haka kuma yana bunkasa kwakwalwa.

Sanna yana da kyau mu kula da fatarmu ta hanyar inganta ta yadda ya kamata, dpomin kauce wa cutakan fata

Fata na da matukar muhimmanci wajen inganta lafiyar dan'adam. Bushewa ko lalacewar fata kan haifar da wasu abubuwa, da ka iya haifar da wata matsalar ga wasu sassan jikin kamar kwakwalwa ko zuciya.

Yana da kyau ku rika kula da fatarku ta hanyar amfrani da mayukan da za su inganta fatar domin hakan zai sa ku zama kamar yara.

Rana ta uku: Mayar da hankali kan tunani

Yin magana ga mutanen da ba ka sani ba, kasancewa cikin yanayi mai kyau kan taimaka wajen sanya mutum ya zama cikin yanayi na murna, juriya da rashin damuwa, kamar yadda binciken kimiyya ya nuna. Haka kuma za ku iya fara wani abu sabo.

Ku rika kalubalantar kawunanku ta hanyar koyon sabbin dabaru don kara wa kwakwalenku karfi, don taimaka musu wajen sabawa da sabbin abubuwa.

Idan kuna jin karfin jikinku, kuna iya yunkurin aiwatar da wasu abubuwa.

Haka kuma yana da kyau ka samu lokaci domin motsa jikinka, tare da aiwatar da wasu abubuwa da za su bunkasa lafiyarmu.

Idan hakan ya yi maka tsauri, yana da kytau a koyaushe ka rika daukar kanka a matsayin yaro.

Bincike ya nuna cewa idan ka dauki kanka a matsayin yaro, za ka iya tsawon kwana.

Yana kuma da kyau ka rungumi dabi'ar yin abubuwan ban mamaki, kamar hawa tsaunuka da kallon teku ko kuma kallon sararin samaniya.

Gano sabbin abubuwa kan rage damuwa tare da bunkasa kwakwalwa da bayar da damar sanin sabbin abubuwan duniya da ke zagaye da kai.

Bincike ya kuma gano cewa motsa jiki kan rage damuwa da bakin ciki tare da rage hawan jini, haka kuma zai taimaka maka wajen samun nagartaccen barci.

Rana ta hudu: mayar da hankali kan alaka

Samun abokai abu ne mai kyau a gareka, za su iya karfafa maka garkuwar jiki tare da lafiyar zuciyarka, da kuma sanya ka samun farin ciki.

Idan ka hada lokacin da kake bata wa da abokanka da irin hirarrakin da kake yi da su za su taimake ka wajen sanya ka jin dadi.

A lokuta da dama mukan dauki sabbin abubuwa daga mutanen da muke mu'amala da su. Kuma abubuwan kan yi matukar tasiri a rayuwa da dabi'armu.

Idan kana neman wani abu karami wanda ya fi abota, za ka iya yin abubuwa da dama fiye rungumar abubuwan da ka saba yi.

Sauyi a tufafin da muke sanyawa da abinci da ra'ayoyinmu kan zama abubuwan jan hankali.

Sabawa da mabambantan dabi'u da yafewa juna, kan taimaka wajen inganta al'amura da dama na rayuwarmu.

Duk da cewa an saba jina ina cewa ''Na yafe maka'', kuma har zuciyata, zai taimaka wajen rage mana damuwa, samar mana da kudi tare da inganta lafiyarmu a lokacin da muke tsufa.

Rana ta biyar: Mayar da hankali kan abin da muke ci

Watan Disamba galibi lokaci ne na daidait irin abincin da muke ci, don inganta lafiyarmu.

A yayin da bukukuwa suka karade watan, ya kasance watan da ake samun ciye-ciyen mabambantan abinci - musamman a lokutan bukukuwan kirsimeti - da za su iya ruda maka ciki.

Ba abin mamaki ba ne mafi yawan mutane kan fara sabuwar shekara da abincin da muke son ci a rayuwarmu.

Idan akwai abincin da ka rage a lokutan bukukuwanb, cin su, maimakon jefar da su ya fi amfani da sauyin yanayi.

Dumama abincin a lokacin da za mu ci yana da mutukar muhimmanci wajen farfado da sinadaran da ke jikin abincin.

Kuma babau wata illa tattare da hakan (sai dai akwai bukatar kauce wa amfani da roba wajen dumama abincin, musamman a na'urar dumama abinci ta microwave)

Cin daidaitaccen abincin da ke kunshe da na'ikan abinci abu ne mai kyau a kowane lokaci na shekara, to amma ya fi kyautuwa a farkon shekarar

Bincike na nuna cewa abincin da ke da maiko da yawa ko suga a cikinsa idan aka ci su da rana, za su iya zama masu illa a zuciya fiye da gangar jiki.

Idan aka zo bangaren 'ya'yan itatuwa da ganyayyaki, binciken ya nuna cewa cin mabambantan wadannan dangi na abinci kan taimaka wajen inganta lafiya tare da rage hatsarin kamuwa da cutar zuciya.

A yayin da ake fara sabuwar shekara a watan Janairu bai kamata ku yi watsi da koffe ba. Bincike ya nuna cewa wadanda ke shan koffi suna da karancin damar hatsarin mutuwa daga cutar bugun zuciya, cutar zuciya da kansa kamuwa da cutar.

To sai dai yana da matyukar muhimmanci mu daidaita yawan koffin da muke sha.

Rana ta shida: Mayar da hankali kan inganta lafiya

A yayin da yin tafiyar kafa zai taimaka wajen habaka karfinka, tare da kona maiko da kuma inganta lafiyar kwakwalwa.

Masana sun ce taku 10,000 a kowace rana kan taimaka wajen rage kitse da maiko a jikin dan'adam, sai dai wani binciken ya ce taku 5,000 ma kawai zai taimaka matruka wajen habaka lafiyar dan'adam.

Idan kuyna son samun ingantuwar lafiyarku, to ku gudanar da motsa jiki akalla sau shida a kowace rana wanda zai taimaka wajen habaka iskar da muke shaka, tare da auna lafiyarmu, da kuma karfin jikinmu domin kona maikon da ke tattare a jikinmu.

Wani bincike kan masu wasan ninkayan gasar Olympic ya nuna cewa motsa jiki da yamma ya fi muhimmanci fiye da na safe.

Rana ta bakwai - Mayar da hankali kan abubuwan da kake jin dadin yinsu

Duk da cewa lokutan nishadi kan bai wa zuciya damar yin tunanin abubuwan mamaki, wasu mutanen kan yi wasa da lokutansu na nishadi

Mutanen da ke shiga yanayin rashin nishadi da wuri kan shiga wani hali da kan tilasta musu shiga wani yanayi na damuwa tare da matsalar kwakwalwa.

Samun sabon abin da kake jin dadin yin sa, zai taiamaka wajen inganta lafiyar kwakwalen yara, da inganta basirarsu.

Karin garabasa: Mayar da hankali kan rayuwar jima'i

Wani abu da ke sa a dauki dabi'ar "son jima'i" shi ne ta hanyar habaka alaka, don haka dole a rage alaka idan ana son rage karuwar jima'i cikin jama'a.

A yanzu akwai manhajoji masu yawa da ke bai wa mutane damar tayar da sha'awarsu ta hanyar amfani da wayoyinsu domin ganin abubuwan da ke tayar da sha'awa.

Ga wadanda ke jin fargabar hira da kananan yaransu a wannan shekara. Bincike ya nuna cewa amsa wa kananan yara tambayoyi cikin gaskiya zai sa su samu kwarin gwiwar yin tambayoyi game da abubuwa masu sarkakiya a nan gaba.

Haka kuma hana yada zantuka da ke da alaka da jima'i tsakanin kananan yara zai taimaka.

Ga wasu matan da dama, rasa budurci na sanya su fushi da takaici da zafin ciwo ko bacin rai, saboda tunani irin na mutanen da.

Koyon yadda ake amfani da wadannan abubuwa, tare da sauya lafazin da ake amfani da shi wajen bayyana shi, kan taimaka wajen inganta jima'i.