You are here: HomeAfricaBBC2024 01 06Article 1908536

BBC Hausa of Saturday, 6 January 2024

Source: BBC

Za a yi karon batta tsakanin Arsenal da Liverpool a FA Cup

Hoton Arsenal da Liverpool Hoton Arsenal da Liverpool

Arsenal za ta karɓi bakuncin Liverpool a wasan zagaye na uku a FA Cup ranar Lahadi a Emirates.

Liverpool tana matakin farko a kan teburin Premier League da maki 45, Arsenal mai maki 40 tana ta huɗun teburin.

Ƙungiyoyin biyu sun kara a bana a Premier League ranar 23 ga watan Disambar 2023, inda suka tashi 1-1 a Anfield.

Abin da ya kamata ku sani kan wasan Arsenal da Liverpool a Anfield

Tun bayan da Arsenal ta yi rashin nasara a wasan karshe a 2001 a Cardiff, Gunners ta yi nasara a kan Liverpool a wasa uku baya da cin 1-0 a Highbury a 2002 da 3-1 a Anfield a 2007 da kuma 2-1 a Emirates a 2014.

Manchester United ce ke kan gaba a fitar da Liverpool daga FA Cup sau 10, sai Gunners mai takwas, yayin da Liverpool ta fitar da Arsenal daga gasar karo biyar.

Wasa uku Arsenal ta yi rashin a gida a FA Cup, shi ne 1-0 da Blackburn Rovers a 2013 da 2-1 a wasa da Watford a 2016 da kuma 3-1 a hannun Manchester United a 2019.

Wasa ɗaya aka yi waje da Liverpool a FA Cup a irin wannan matakin a kaka 12, shi ne 2-1 da Wolverhampton ta yi nasara a 2019.

Gabriel Jesus yana da hannu a kwallo 16 a wasa 20 a FA Cup, wanda ya ci kwallo 10 ya bayar da shida aka zura a raga.

Wasan baya-bayan nan da ya buga a gasar shi ne da Liverpool, wanda ya bayar da kwallo aka zura a raga a fafatawar da Manchester City ta yi nasara 3-2 a daf da karshe a 2022.

Alkalin da zai busa wasan:

John Brooks

Duk da busa wasa kaka uku baya a Premier League, John Brooks ne zai busa wasa tsakanin Arsenal da Liverpool a karon farko.

Wasa 12 Brooks ya ja ragama a kakar nan kawo yanzu, ya bayar da jan kati huɗu da busa bugun fenariti huɗu.

Ya busa wasan Liverpool huɗu, duk a kakar nan ta 2023.

Shi ne ya busa wasan da Liverpool ta yi nasara a kan Newcastle United 2-1 a cikin watan Agusta da wasan da Bournemouth ta kara a League Cup.

Wasan karshe da aka fafata a FA Cup tsakanin Arsenal da Liverpool a cikin Fabrairun 2014, inda Red Alex Oxlade-Chamberlain da Lukas Podolski suka ci wa Gunners kwallayen a Emirates da ta kai quarter-finals.

Wasannin da za a buga ranar Lahadi:


  • Manchester City da Huddersfield Town
  • Luton Town da Bolton Wanderers
  • West Ham United da Bristol City
  • Peterborough United da Leeds United
  • Shrewsbury Town da Wrexham
  • West Bromwich Albion da Aldershot Town
  • Nottingham Forest da Blackpool
  • Arsenal da Liverpool