You are here: HomeAfricaBBC2024 01 10Article 1910576

BBC Hausa of Wednesday, 10 January 2024

Source: BBC

Za mu iya daidaita alaƙa da Isra'ila amma bisa sharaɗi - Saudiyya

Tutar Saudiyya Tutar Saudiyya

Jakadan Saudiyya a Birtaniya ya ce ƙasarsa tana sha'awar daidaita dangantaka da Isra'ila bayan kammala yaƙi a Gaza, sai dai duk wata yarjejeniya da za a ƙulla, sai ta kai ga kafa ƙasar Falasɗinawa.

Yarima Khalid bin Bandar ya faɗa wa BBC ana "daf da" da cimma yarjejeniya lokacin da Masarautar ta dakatar da tattaunawar da Amurka ta shiga tsakani bayan miyagun hare-haren da Hamas ta kai wa Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoba.

Sai dai har yanzu Saudiyya tana da imanin cewa ƙulla dangantaka da Isra'ila abu ne mai yiwuwa duk da yawan "alla-wadai" na mutanen da aka kashe a Gaza, in ji shi, sai dai hakan ba za ta tabbata ba ta hanyar "sarayar da haƙƙin al'ummar Falasɗinawa".

Jakadan ya kuma yi gargaɗin cewa akwai "gazawar jin ƙan ɗan'adam game da batun Gaza, inda al'ummar duniya ta kasa yin isasshen abin da ya dace don kawo ƙarshen yaƙin.

Ya kuma ce zai so ganin Birtaniya ta "saisaita matsayinta" kuma "ta tafiyar da Isra'ila kamar yadda take tafiyar da kowa". "Kafar da ake amfani da ita wajen kare Isra'ila ba shakka matsala ce saboda ta ba da kafar tokare zaman lafiya<" ya ƙara da cewa.

  • Shugabannin Musulmai sun ce laifin Yamma ne ƙuncin da Gaza ke ciki
  • Bayani kan iyalan da ke riƙe da rigar Annabi Muhammad a Turkiyya


  • Saudiyya ita ce jagora ga ƙasashen Larabawa da kuma na Musulmin duniya. Ba ta taɓa amincewa da Isra'ila ba a ƙa'idance, tun da aka kafa ta cikin 1948, don haka duk wata yarjejeniyar ƙulla dangantaka za ta kasance wata gagarumar nasara ga ƙasar ta Yahudawa.

    A ƙarshen watan Samtumba ne, jagoran da ke riƙe da iko a Saudiyya ya ayyana yayin hirar talbijin a Amurka cewa "kullum muna daɗa kusantar" cimma wata yarjejejniya.

    Yayin da Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman ya ce batun al'ummar Falasɗinawa na da "matuƙar muhimmanci" kuma duk wata yarjejeniya da za a cimma "tabbas sai ta kawo sauƙi ga rayuwar Falasɗinawa", amma bai ayyana cewa sai ta dogara a kan ƙoƙarin cimma muradun kafa wata ƙasar Falasdinawa mai zaman kanta ba.

    Matsayin jama'a na shugabannin Falasɗinawa shi ne za su yi watsi kwata-kwata da wata yarjejeniya, matuƙar ba za ta bar su su kafa ƙasa ba.

    Sai dai a farkon wancan wata, jami'ai sun ce a keɓe suna neman ƙarin kudaɗe da kuma iko na filayen Gaɓar Yamma da ke ƙarƙashin mamaya a maimakon haka za su yi aiki da yarjejeniyar daidaita tsakanin Saudiyya da Isra'ila wadda Amurka ke marawa baya.

    An ba da rahoton cewa jami'an Saudiyya sun nemi Amurka ta dakatar da tattaunawar ɓangare uku kwanaki ƙalilan bayan hare-haren 7 ga watan Oktoba, waɗanda suka yi sanadin kashe mutum 1,300, yayin da ɗaruruwan 'yan bindigan Hamas waɗanda suka yi kutse daga Gaza zuwa cikin matsugunnan kudancin Isra'ila suka yi garkuwa da mutum 240.

    Ma'aikatar lafiyar Gaza da ke ƙarƙashin ikon Hamas ta ce an kashe mutane fiye da 23,200 a yankin a lokacin hare-haren sojoji waɗanda Isra'ila ta ƙaddamar daga bisani da nufin tarwatsa Hamas.

    Bayan ganawarsa da Yarima mai jiran gado Mohammed Bin Salman a ranar Litinin, sakataren wajen Amurka Anthony Blinken ya faɗa wa manema labarai cewa ya bijiro da maganar ƙulla dangantakar.

    "Akwai sha'awa ƙarara a nan ta bin wannan muradi," ya ce. "Sai dai za ta buƙaci sai an kawo ƙarshen yaƙi a Gaza, kuma ƙarara za ta buƙaci cewa sai an samar da wani tsari na zahiri da zai kai ga kafa ƙasar Falasɗin."

    Yayin zantawa da shirin BBC a Yau ranar Talata, jakadan Saudiyya a London ya tabbatar da cewa "ba shakka akwai muradi" a tsakanin shugabannin ƙasar na ganin an cimma wata yarjejeniya.

    "An kusa cimma [wata yarjejeniya] babu ko tantama. A gare mu, matakin ƙarshe haƙiƙa sai ya haɗar da wani abu da bai gaza ƙasar Falasɗinawa mai 'yancin kanta ba. Don haka, yayin har yanzu muke ci gaba da tafiya gaba bayan harin ranar 7 ga watan Oktoba - da imanin ƙulla dangantaka, hakan ba zai sarayar da haƙƙin al'ummar Falasɗinawa bae," in ji Yarima Khalid.

    Ya ƙara da cewa: "Mun kusa daidaitawa, don haka daf ake da samun kafuwar ƙasar Falasɗinu. Ɗaya ba zai faru ba, sai da ɗayan. Jerin, yadda lamarin zai kasance, shi ne abin da ake tattaunawa a kai."

    An tambaye shi ko Saudiyya tana kallon Hamas - wadda Isra'ila da Amurka da Birtaniya da sauran ƙasashen Yamma suka ayyana, a matsayin ƙungiyar ta'addanci - za ta kasance wani ɓangare na ƙasar Falasɗinawa ta gaba, Yarima Khalid ya ce hakan na "buƙatar tunani mai zurfi".

    "A kullum damar canzawa idan akwai kyakkyawan fata da buri. Amma idan ana rikici, abu na farko da ake iya fahimta shi ne kowanne ɓangare ya yi asara," ya ƙara da cewa.

    "Matsalar da muke da ita a yau da gwamnati mai ci ta Isra'ila, shi ne akwai tsattsauran ra'ayi da kuma hange irin na tuwona-maina wanda kuma ba ya biyan buƙata wajen samun sassauci, don haka ba za a taɓa kawo ƙarshen rikici ba."

    Bai dai faɗaɗa bayani ba, sai dai Amurka ta yi tir da wasu ministocin Isra'ila biyu masu matsanancin ra'ayi, waɗanda a baya-bayan nan suka yi kiran a mayar da Falasɗinawa wani wuri da ke wajen Gaza.

    Yarima Khalid ya kuma yi gargaɗim cewa akwai kasadar ƙeƙashewar zukata sanadin yaƙi, wanda ba kawai ya zama dalilin mutuwar dubban fararen hula a Gaza ba, ya kuma haddasa tagayyara da gagarumar matsalar ayyukan jin ƙai.

    "Ƙazaman ayyukan tarzomar da ba a taɓa ganin irinsu ba da kowanne ɓangare ya aikata - amma musamman daga abin da ya kamata ya kasance ƙasa da ta san ciwon kanta daga sashen Isra'ila - a cikin wata uku da ya wuce, ba na jin na taɓa ganin wani abu mai kama da haka a rayuwata," in ji shi. "Yawan mutanen da aka kashe abin alla-wadai ne, gaba ɗaya abin a yi tir da shi ne."

    "Hakan zai iya haifar da yanke ƙauna ba kawai a tsakanin al'ummar Falasɗinawa ba, har ma a tsakanin mutanen da ke da rashin gamsuwa cikin zukatansu [a faɗin duniya]. Duka suna ganin akwai gazawar jin ƙan ɗan'adam ga abin da ke faruwa, saboda babu wanda ya yi wani yunƙuri na ganin ya dakatar da hakan. Ana ƙoƙari, amma dai bai isa ba."