Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya, Malam Mustapha Baba Illela, ya bayyana cewa daga farko ya ki mayar da hankali wajen aikin gwamnati duk kuwa da cewa yana da damar yin hakan saboda yana da burin ya bayar da gudunmawa ga al'umarsa domin su amfana daga dan karatun da Allah ya hore masa.
Malam Mustapha ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da BBC a cikin shirin Ku San Malamanku, inda ya ce yana godiya ga Allah da ya sa karatun Alkur'ani mai girma shi ya haife shi, ya haifi iyayensa, ya kuma haifi kaka da kakanninsa, kana duka 'yayansa mahaddatan Alkur'ani ne.
Wanene Malam Mustapha Baba Illela?
Malam Mustapha Baba Illela shi ne shugaban Hukumar Shari'ar Muslunci ta jihar Bauchi, kuma shugaban Kwamitin Musabaqa na jihar.
An kuma haife shi a cikin garin Bauchi a wata unguwa da ake kira Illela da ke kusa da fadar mai martaba sarkin Bauchi a shekarar 1968.
Mahaifinsa shi ne Shu'aibu wanda aka fi sani da Baba Illela, malamin addinin Musulunci ne mai karantar da Alkur'ani da abin da ya shafi littafai, irin karatun Fiqihu da Tauhidi da sauran ilimomi irin na karatun zaure.
Malamin ya shaida wa BBC cewa ya fara karatun sanin farilla da sunna a wajen mahaifiyarsa marigayiya Rukayyatu, inda daga bisani ya saka littattafai a gaban mahifinsa, kuma bayan da ya sauke wasu littafan ne sai mahaifinsa ya dauke shi ya kai shi gaban wasu malamai a garin na Bauchi.
"Na jima a gaban malam Ahmadu Makaman Liman a Unguwar Jaki ina karatun litattafa na dukkanin fannonin Tauhidi, da Fiqihu, da Hadisai, tarihi da kuma ilimin ka'idar lugga da aka sani da Nahawu. Na kuma karu da karantarwarshi da dabi'unshi, mutum ne da ya kware a bangaren tafsiri, idan yana tafsiri kai ka ce kamar shi ya rubuta," in ji malam Mustpha.
Malamin ya kara da cewa ya yi karatu a wajen daya daga cikin abokan mahaifinshi wato marigayi Malam Shehu Illela, sannan ya yi karatu wajen marigayi malam Ahmadu na bayan Fada wanda duka Allah ya yi musu rauswa. Kana malamin ya yi karatu kan abin da ya shafi adabin Larabci a wajen daya daga cikin yayyensa malam Muhammd Shu'aibu Arab.
Bayan karatun litattafa irin na zaure, ya tafi jihar Gombe inda ya yi karatu a Kwalejin Horon Malamai ta Arabic Teachers College ta jihar Gombe inda ya samu takardar shaidar karatu ta Grade 2, kana daga baya ya koma ya yi difiloma a fannin koyar da Larabci ga wadanda harshensu ba yaren Larabcin ba ne.
Bayan ya koma Bauchi a shekara ta 1990 ya fara aiki da wata makaranta mai zaman kanta yana aikin koyarwa daga baya ya koma makarantar Hayatul Islam mai zaman kanta da ke garin na Bauchin.
"Lokacin ina da damar kama aikin gwamnati amma sai ya zama ina da burin na bayar da gudunmawa ga al'ummata su amfana daga dan karatun da Allah ya hore min, wannan shi ne ya sa ban kai hankalina kan aikin gwamnati ba," in ji malamin.
Daga bisani ne ya ce mijin yayarshi mai suna Bababa Ahmed ya sama masa aiki a karamar hukumar Bauchi, inda bayan nan ya fara aiki da Hukumar Shari'ar Musulunci a shekarar 2007 lokacin mulkin Gwamna Isa Yuguda, kuma aka ba shi mukami a matsayin Kwamishina mai kula da harkokin Shari'a da wayar da kan jama'a inda ya shafe shekaru hudu a kan wannan mukami.
Bayan da aka sake zabe ne da gwamnatin ta Isa Yuguda ta sake komawa sai aka sake dawo da malamin a Hukumar Shari'ar Musulunci a matsayin Kwamishina mai kula da Da'awa da ilimin addinin Musulunci.
A shekarar 2012 ne kuma aka ba shi mukamin shugabancin hukumar har ya zuwa 2014 sai aka yi zabe aka samu canjin gwamnati shi ne tun daga nan ya sake komawa abin da malamin ya ce ya fi shaa'wa a rayuwarshi ya ci gaba da karantarwa a zaure har ya zuwa yau din nan.
Ya ci gaba da karantarwa a wata makaranta mai suna Madarasatul Miftahu Sa'ada wacce daya daga cikin almajiran mahaifinsa Farfesa Yakubu Mahmud ya bude ya kuma umarce shi da ya jagorance ta.
"Akwai sassa daban-daban da ke karantar da ilimin addini da na boko a tsawon sati, na kuma cigaba da rike wannan makarantar har ya zuwa yanzu, ina yi ina hadawa da karatun zaure, ban da harkar da'awa da wasu rubuce-rubuce da karance-karance da nake yi a masallaci da ke nan unguwarmu da kuma a wasu wurare idan an gayyace ni," in ji shi.
Abubuwan ban mamaki biyu da 'ba zan manta da su ba'
Malam Mustapha Baba Illela ya kuma yi wa BBC bayanin wasu abubuwan ban mamaki da al'ajabi da ya ce ba zai taba mantawa da su ba a yayin yake gudanar da ayyukansa, na farko a lokacin yana cikin ofis aka kawo masa rahoton cewa ga wani bawan Allah ya yi wa wata gawa aure da wani mutum da ke raye.
A cewarsa: "Wata baiwar Allah ce ta rasu da ana shirya mata likkafani sai mahaifiyarta ta leko ta cewa limamin yarinyar nan ta bar wasiyya cewa ko ta mutu a daura mata aure da saurayinta, kuma ta bar wasiyyar cewa in an daura mata auren sadakinta a yi mata sadaka da shi."
Malamin ya ce wannan abu ya yi matukar ba shi mamaki da kuma takaicin irin jahilcin da ya sa za a aikata hakan, da sai da ya fadakar da limamin sharudan da suka shafi matakan daura auren.
Malam Mustapha Baba Illela ya ce abu na biyu shi ne na lokacin da aka kawo masa wata karamar yarinya da ba ta fi shekara shida ba cewa iyayenta ba su yarda ta kwana a gidansu ba saboda an shigar da ita harkar maita kuma ta ci mutum biyu, kana akwai 'yar uwarta da ta saka ta a ciki ita kuma ta ci mutum bakwai tana shirin cin na takwas kuma ta ce yau wani zai mutu a cikin gidan.
"Wato kafin ka ce kwabo sai kafar daya daga cikin magidantan ta kumbura suntum ya gagara tashi sai aka kamata aka dake ta, sai ta ce a kawo ruwa a baho ta ce a saka a karkashin gadon da yake kwance, bayan an yi hakan sai kafar ta fara sacewa, shikenan sai ya tashi ya samu lafiya'', to daga nan sai suka ce yarinyar baza ta sake zama da su ba sai dai a mayar da ita can wajen kakanninta a Nasarawa" in ji malamin
Ya kara da cewa ''Alhamdulillahi lokacin ne na tayar da wani dan agajina mai tawakkali ya dauke ta ya tafi da ita can Nasarawar ya mika ta ga kakanninta".
Abin farincikin da ba zai manta dashi ba
Babban abin da malamin ya ce ba zai taba mantawa da shi ba na farin cikin shi ne lokacin da aka ce zai je aikin Hajji, na biyu kuma lokacin da Allah ya kaddara masa ya yi auren fari.
A cewarsa: "Kasan wani abu ne da dole mutum ya yi farin ciki da shi, yau shekara ashirin da kadan muna tare, da ina da mata uku amma daya daga cikin su malama Zainab Allah ya karbi ran ta watanni bakwai da suka wuce bayan ta haihu da sati biyu, amma dan da ta bari Muhammad Nasir yana raye cikin koshin lafiya."
Ya kuma ce ''Alhamdulillahi ina godiya ga ubangiji da karatun Alkurani shi ya haife ni ya haifi iyayena, ya haifi kakanni da kakannina, tun zamanin sarkin Bauchi Yakubu kakaninmu suka zo garin Bauchi da nufin karatun Alkur'ani ya tarbe su ya ba su masauki a unguwar Zannuwa ya gina masallaci ya tona musu rijiya. "
Malamin ya ce a gaskiya karatun Allkur'ani shi yake so, kuma hatta 'yayansa ma a kan haka "na dora su."
"Yanzu dai mata biyu da 'ya'ya 14, kuma akwai mahaddatan Alkur'ani a ciki maza da mata, idan na wayi gari kuma na tuna wasu ayyukan alkairi da na yi yana sa ni farin ciki," in ji shi.