An shafe tsawon dare ana kokarin ceto wadanda suka tsira da rai da kuma zakulo gawarwaki a jihar Kerala da ke kudancin India bayan wani kwale-kwale dauke da masu yawon bude idanu ya kife.
Akalla mutum 22 ne suka hallaka yayin da kwale-kwalen mai bene ya yi hadarin a tsakiyar kogi.
Wadanda suka ga yadda hadarin ya faru sun ce an shirya jigilar mutanen masu yawon buda idanu a wannan jirgin ruwa mai bene ne da maraice saboda cincirundo na yawan masu zuwa shakatawa bakin teku.
‘Yan sanda sun ce bincike ya nuna cewa jirgin ya kife ne sakamakon yawan da mutanen ciki suka yi, inda yake dauke da wajen mutum 50, wanda hakan ya ninka yawan mutanen da ya kamata ya dauka biyu.
Biyar daga cikin wadanda suka mutu yara ne da mata, wadanda ke hutun makaranta.
Wasu daga cikin wadanda aka ceto suna cikin mawuyacin hali.
Wadanda suka tsira sun bayyana cewa da yawa daga cikin mutanen da ke cikin jirgin ba sa sanye da rigar fito a lokacin da hadarin ya faru.
Kuma har yanzu ba a ga wasu mutanen ba, yayin da ake ci gaba da aikin ceton.
Ba a san ainahin yawan wadanda ba a gani ba, yayin da hukumomi ke kara gudanar da bincike kan abin da ya janyo hadarin.
yanzu ana kokarin janyo shi daga cikin tabo inda hadarin ya faru.
A wani sako da ya sanya a Twitter, Firaminista Narendra Modi ya yi ta’aziyya ga wadanda suka rasu, tare da fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata, yana cewa ya kadu da wannan asarar rayuka da aka yi.