BBC Hausa of Wednesday, 26 April 2023

Source: BBC

A bar majalisa ta fitar da shugabanci ba ƙarfa-ƙarfa ba - Kawu Sumaila

Onarabul Abdurrahman Kawu Sumaila Onarabul Abdurrahman Kawu Sumaila

Ƙasa da wata biyu a buɗe Majalisar Tarayya ta 10, ana ci gaba da kiraye-kiraye a Najeriya game da tsarin da ya kamata a bi wajen fitar da shugabanninta.

'Yan majalisa da dama ne tsakanin majalisar dattijai da ta wakila suka ayyana burinsu na samun damar zama mutum na uku da na huɗu mafi girman muƙami a ƙasar.

Sai dai, jam'iyyar APC mai mulki wadda ke da rinjaye a zaurukan majalisar tarayyar ta ce sun yi azarɓaɓi. A cewarta, kamata ya yi su bai wa jam'iyyar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar damar raba muƙaman zuwa shiyyoyin Najeriya.

Amma ana ƙara samun masu kiraye-kirayen cewa a bar dimokraɗiyya ta yi aikinta wajen fitar da shugabancin majalisa ta 10, maimakon fifita muradin wata jam'iyya.

Cikin masu wannan kira, har da zaɓaɓɓen ɗan majalisar dattijai na jam'iyyar adawa ta NNPP, Onarabul Abdurrahman Kawu Sumaila.

A cewar ɗan majalisar mai wakiltar mazaɓar Kano ta Kudu 'yan majalisar dokoki, al'ummar ƙasa suke wakilta, ba shugaban ƙasa ko jam'iyyarsa ba.

Don haka ya ce kamata ya yi a bar musu wuƙa da nama, su zaɓi shugaban da suke so.

Shugabancin Majalisun dokoki

Abdurrahman Kawu Sumaila ya ce majalisa ta 10 za ta fi duk sauran majalisun da aka yi ba da gagarumar gudunmawa wajen inganta dimokraɗiyya a ƙasar, saboda a cewarsa babu jam'iyyar mai gagarumin rinjayen da za ta iya yin doka ita kaɗai, ba tare da goyon bayan 'yan adawa ba.

Ya ce tsarin mulki ne ya raba iko tsakanin ɓangarorin gwamnati uku, don haka kamata ya yi a bar 'yan majalisar su zaɓi mutanen da suke ganin su ne suka fi cancanta.

"A bar 'yan majalisa su zaɓi mutumin da suke ganin ya cancanta, ba tare da la'akari da jam'iyya ko daga wanne ɓangare ya fito ba, matuƙar zai bayar da gudunmawa wajen haɗa kan 'yan majalisar, da kuma ciyar da ƙasa gaba," in ji shi.

Zaɓaɓɓen ɗan majalisar dattijan ya ce majalisun tarayyar ƙasar biyu duk suna da dokoki da ke musu jagora wajen zaɓar shugabanninsu.

Ya ce "Alal misali a majalisar dattijai an kasa 'yan majalisa gida uku game da haƙƙin (fitar da) shugabanci. Kashi na farko su ne tsofaffin sanatoci da aka sake zaɓarsu, su ne kan gaba''.

''Sai kuma tsoffin 'yan majalisar wakilai waɗanda aka zaɓa zuwa majalisar dattijai, su ma suna da haƙƙi.

Sai kuma sabbin 'yan majalisa waɗanda wannan ne karonsu na farko a majalisun biyu, to waɗannan ba su da haƙƙin shugabancin majalisun'', in ji Kawu Sumaila.

'Ƙaƙaba shugabanci ba ya tasiri'

Zaɓaɓɓen ɗan majalisar dattawan ya ce a baya an taɓa yin irin wannan tsari na ƙaƙaba shugabancin majalisa, amma buƙata ba ta biya ba.

A cewarsa, ƙaƙaba shugabannin kan janyo rashin goyon bayan rinjayen 'yan majalisa, har ta kai ga ana kaɗa ƙuri'a don tsige wani shugaba.

Ya ce a baya, an cire shugabannin majalisa har sau biyu, saboda rashin jituwar da aka samu.

"A baya, mun ga yadda jam'iyya mai mulki da fadar shugaban ƙasa suka zauna suka zaɓi, Patricia Etteh amma daga baya 'yan majalisa suka yi mata tawaye kuma suka sauke ta, inda suka zaɓo Bankole," in ji shi.

'Ba na goyon bayan shiyya-shiyya'

Dangane da rabon muƙaman majalisar zuwa shiyya-shiyya, zaɓaɓɓen ɗan majalisar dattijai ya ce kamata ya yi a samu shugabannin da za su kare martabar ƙasa da 'yan ƙasa.

Ba 'yan amshin-shata ba, in ji shi, waɗanda za a riƙa rubuto abu daga fadar shugaban ƙasa ko ɓangaren zartarwa su riƙa sa hannu kawai, kamar yadda ya faru a baya.

"Domin kuwa an taɓa samun irin hakan a baya, lokacin da aka cire Patricia Etteh aka kawo Bankole, aka cire Okadigbo aka kawo Anyim Pius Anyim.

Haka kuma 'yan majalisa ne suka kawo Ken Nnamani, sannan su ne suka kawo Dogara da Saraki, ba ɓangaren zartarwa ko jam'iyyarsu ba," cewar Kawu.

Ya ce "Jam'iyyar APC a baya, ba ita ta fito da mataimakin shugaban ƙasa Bayarabe daga jihar Legas ba? kuma ta fitar da kakakin majalisar wakilai, shi ma Bayarabe daga jiha ɗaya ba? Sai yanzu ne, ta san a raba muƙamai a kai wannan nan, (a kai wannan can?"

'Bai kamata a sa batun addini ba'

Ya ce babban abin da ya fi muhimmanci shi ne wane ne zai iya, ba maganar addini ko ɓangaranci ba.

"A baya lokacin da Sanata David Mark ke shugabantar majalisar dattijai, Ike Ekweremadu na mataimakinsa, kuma shugaban masu rinjaye Ndoma Egba duka Kiristoci ne," in ji shi.