BBC Hausa of Friday, 14 October 2022

Source: BBC

Abin da 'yan Najeriya ke cewa kan janye yajin aikin ASUU

ASUU ta fitar cewa ta janye yajin aikin da ta kwashe watanni takwas ASUU ta fitar cewa ta janye yajin aikin da ta kwashe watanni takwas

'Yan Najeriya sun soma tsokaci bayan sanarwar da kungiyar malaman jami'o'in gwamnatin tarayyar kasar, ASUU ta fitar cewa ta janye yajin aikin da ta kwashe watanni takwas tana yi. A ranar Juma'ar nan da asubahi ne ASUU ta sanar da janye yajin aikin bayan ta shafe tsawon dare tana ganawa da manyan jami'anta game da batun. ASUU dai ta shiga yajin aikin ne bayan ta zargi gwamnati da kin biya mata bukatun da suka ƙunshi samar da wadatattun kuɗin gudanarwa da alawus-alawus da kuma inganta yanayin karatun dalibai. Yajin aikin ya kassara harkokin ilimi a kasar kuma ya jawo zazzafar muhawara game da ikirarin gwamnati na son ci gaban harkokin ilimi da kuma suka ga malaman jami'o'in kan son kai. Kazalika kungiyoyin dalibai sun gudanar da jerin zang-zanga domin tilasta wa gwamnati da ASUU su shawo kan matsalolin da suka haddasda yajin aikin. Da ma dai 'yan kasar sun yi ta kasa kunne domin jin matakin da kungiyar za ta dauka bayan a watan jiya Kotun Daukaka Kara ta kasar ta umarce ta janye yajin aikin. Da yake yanke hukunci kan bukatar wucin gadi da gwamnatin tarayya ta nema, alkaliin kotun Mai shari'ah Polycarp Hamman ya hana kungiyar ASUU ci gaba da yajin aiki har zuwa lokacin yanke hukunci kan shari'ar. Lamarin dai ya janyo ce-ce-ku-ce tsakanin bangarorin biyu, inda daga bisani ASUU ta ci gaba da ganawar da take yi da shugaban majalisar wakilan kasar Femi Gbajabiamila, wanda shi ma ya dade yana shiga tsakani. Kuma bayan ganawar da suka yi ta karshe a makon jiya, shugaban ASUU Farfesa Victor Emmanuel Osodeke ya shaida wa 'yan jarida cewa nan ba da jimawa ba za su kawo karshen yajin aikin. Hakan ne ya sa 'yan kasar suka bayyana ra'ayoyi daban-daban Shaki iskar 'yanci 'Yan Najeriya da dama sun bayyana jin dadinsu bayana da suka wayi gari da jin labarin janye yajin aikin kungiyar ASUU. Hafizu Balarabe Gusai ya nuna jin dadinsa sannan ya ce da fatan dai ASUU ta samu biyan bukatunta. Shi ma Idriss Najeb ya ce dalibai sun shaki iskar 'yanci bayan da ASUU ta janye yajin aikin, yana mai addu'ar Allah ya sa hakan ba za ta sake faruwa ba. Amma Bawa Abdullahi Maska ya koka kan yadda yajin aikin ya "dakushe harkokin ilmin jami'o'i" duk da yake yana farin cikin janye shi. A nasa bangaren, Sani Mailangelange Yawuri ya yi kira da a ci gaba da fahimtar juna tsakanin ASUU da gwamnatin Najeriya.