BBC Hausa of Thursday, 20 October 2022

Source: BBC

An mayar da rigar da Maradona ya buga Kofin duniya da ita Argentina

Rigar Maradona a hagu Rigar Maradona a hagu

Argentina na murnar dawo mata da rigar gwarzon dan kwallon kafarta Diego Maradona wadda ya buga wasan karshe da ita na gasar Cin Kofin duniya. Shekara 36 kenan bayan da Argentina ta samu nasara kan Jamus a wasan karshe ka Kofin duniya a 1986, rigar da Maradona ya sanya a minti 45 din farko na wasan aka mayar wa hukumar kwallon kafa ta Argentina AFA. Tsohon dan wasan tsakiya na Jamus Lothar Matthaus, wanda suka yi musanye rigar da Maradona ne ya mayar wa da mutanen Argentina rigar. Hukumar kwallon kafar ta yi masa godiya kan wannan gagarumin aiki da ya yi. A farkon shekarar nan ne aka sayar da wata rigar ta Maradona, wadda ya sa a wasan da ya ci Ingila da hannu a dai gasar ta kofin Duniya na 1986, kan kudi fan miliyan 7.1. Tsohon dan wasan tsakiya an Ingila Steve Hodge ne ya yi gwanjon rigar. Duk da irin yadda aka sayi rigar da ya buga wasan Ingila da ita kan kudi masu tsada, Lothar Matthaus ya ce bai taba tunanin sayar da rigar ta Maradona ba. A watan Agusta ne dan wasan ya mika wa mutanen Argentina rigar a ofishin jakadancinta a Madrid, yana cewa, "Diega wani abin koyi ne a Argentina, shi yasa yake da muhimmanci a bai wa muatnensa wannan rigar. Za a ajiye rigar ne a gidan tarihi domin a rika tunawa da gudunmuwar da dan wasan ya bayar a kasarsa.