BBC Hausa of Tuesday, 6 June 2023

Source: BBC

AC Milan ta kori Paolo Maldini

AC Milan ta kori daraktan tsare-tsarenta, Paolo Maldini AC Milan ta kori daraktan tsare-tsarenta, Paolo Maldini

AC Milan ta kori daraktan tsare-tsarenta, Paolo Maldini, bayan shekara biyar yana kan mukamin.

Maldini ya taimaka wa Milan ta lashe Serie A a kakar 2022 na farko tun bayan shekara 11.

A kakar bana, Milan ta kare a mataki na hudu a teburin Serie A, ta kuma kai wasan daf da karshe a Champions League, inda Inter Milan ta fitar da ita daga gasar.

A lokacin da yake aikin daraktan tsare--tsare, Maldini ya bayar da gudunmuwar da kungiyar ta dauko fitattun 'yan wasa da suka hada da Rafael Leao da Theo Hernandez da Fikayo Tomori da kuma Olivier Giroud.

Mai shekara 54 ya kwashe gaba daya shekarun sa na sana'ar tamaula a Milan, wadda ya yi wa wasa 901 da lashe kofi 26, ciki har da Serie A bakwai da kofin zakarun Turai biyar.