Real Madrid za ta kara da Liverpool ranar Laraba a wasa na biyu a Champions League, zagayen 'yan 16 a Santiago Bernabeu.
Ranar 21 ga watan Fabrairu, Real ta ci Liverpool 5-2 a wasan farko a Anfield a gasar zakarun Turai ta bana.
Liverpool ce ta fara zura kwallo biyu a raga ta hannun Darwin Nunez da Mohamed Salah a Anfield.
Daga baya Real ta ci biyar ta hannun Vinicius Junior da ya zura biyu a raga da Eder Militao mai daya da kuma Karim Benzema da shima ya ci biyu.
A bara Real ta doke Liverpool 1-0 a Faransa ta dauki Champions League na 14 jimilla, karo na biyu da ta dauki kofin a kan Liverpool a tarihi.
A kakar 2017/18, Real ta ci Liverpool 3-1 a Lisbon ta lashe Champions League.
Sun yi wasa 10 a tsakaninsu, Real ta ci shida, Liverpool ta yi nasara a uku da canjaras daya.
Real Madrid tana mataki na biyu a teburin La Liga da tazarar maki tara tsakaninta da Barcelona ta biyu a bana.
Ita kuwa Liverpool tana ta shida a Premier League da maki 42, bayan da Arsenal ke jan ragama mai maki 66, bayan wasan mako na 27.
Tuni Carlos Ancelotti ya bayyana 'yan wasan da zai fuskanci Liverpool a Santiago Bernabeu.
'Yan wasan Real Madrid:
Masu tsaron raga: Courtois, Lunin and Luis López.
Masu saron baya: Carvajal, E. Militão, Vallejo, Nacho, Odriozola, Lucas V., Rüdiger and Mendy.
Masu buga tsakiya: Kroos, Modrić, Camavinga, Valverde, Tchouameni and D. Ceballos.
Masu cin kwallaye: Hazard, Benzema, Asensio, Vini Jr., Rodrygo, Mariano and Álvaro.
Jerin wasa da aka buga tsakanin kungiyoyin biyu:
2022/2023 Champions League
- Liverpool 2 - 5 Real Madrid
- Liverpool 0 - 1 Real Madrid
- Liverpool 0 - 0 Real Madrid
- Real Madrid 3 - 1 Liverpool
- Real Madrid 3 - 1 Liverpool
- Real Madrid 1 - 0 Liverpool
- Liverpool 0 - 3 Real Madrid
- Liverpool 4 - 0 Real Madrid
- Real Madrid 0 - 1 Liverpool
- Liverpool 1 - 0 Real Madrid
Henderson bai da lafiya, shi kuwa matashi mai shekara 18 ya ji rauni ne.
Liverpool na bukatar kai wa zagayen gaba a kakar nan, bayan da ta kasa daukar Carabao Cup an fitar da ita a gasar FA Cup a bana tana ta shida a Premier.
Idan har ba ta yi da gaske ba, za ta kare kakar bana ba tare da daukar kofi koda na shayi ba, sannan ta rasa gurbin shiga Champions League na badi.
A bara Liverpool ta dauki Carabao da FA Cup, sannan ta yi ta biyu a Premier League ta kuma je wasan karshe a Champions League.