Yayin da mutane da dama suke burin sirancewa, akwai waɗanda suke rayuwa cikin ƙunci saboda rama da rashin ƙiba.
Masana lafiya sun bayyana cewar rama ba matsala ba ce, sai idan ta danganci yanayi irin na tsananin rashin son cin abinci da kuma cutar raunin ƙashi.
Abinci mai ɗauke da sindarai masu inganci
Ana samun ƙiba ba tare da yawaita shan abubuwan sha masu ɗauke da sukari da sindarai ba, da kuma rungumar ciye-ciyen kayan ƙwalan da maƙulashe.Masana abinci da lafiya sun bayar da shawarar yin tsari mai inganci don samun ƙibar da za ta yi daidai da tsayi da nauyin jikin mutum.
Farfesa Linda Bobrof ta Jami'ar Florida, ta shaida wa BBC cewar cin abinci sau uku a rana tare da haɗawa da cin kayan ƙwalama ne hanya mafi sauƙi ta samun ƙiba.
Farfesa Bobrof ta ƙara da cewar:
“Abincin da ke da adadin kuzari da sinadirai masu yawa shi ma yana ɗauke da kitse, amma abu mai muhimmanci shi ne a zaɓi nau'in maiƙon da ya dace.”
Gyaɗa da riɗi da yalo da man kwakwa suna da maiƙo na ƴaƴan itatuwa wanda ke ƙunshe da sanadarai da kitse mai amfani ga jiki.
Kitsen dabbobi yana bayar da sinadirai kwatankwacin wadanda ake samu a jikin ƴaƴan itatuwa, sai dai yana da maiƙon da zai iya cutar da lafiyar jiki.
Muhimmin abu shi ne, zaɓin abinci mai ɗauke da sinadaran gina jiki.
Tara ƙwanjiDalilan da suke sa wasu mutane su buƙaci ƙiba sun haɗa da sha'awar tara ƙwanji don wasannin motsa jiki da kuma maye gurbin rashin cin abinci da kuma samun siffa irin ta lafiyayyun mutane.
Gavin Allinson ƙwararre a fannin abincin masu motsa jiki, ya bayyana naman kaza da kuma kifi a matsayin abubuwan da masu son tara ƙwanji za su riƙa ci.
''Kuna iya haɗa nama da kifi da shinkafa ko sauran abinci mai sanya kuzari.''
Mutanen da ke yawan motsa jiki kuma ba sa son yin ƙiba, su mayar da hankali ga yawan cin abinci da kayan ƙwalama don samun ƙarin ƙarfin jiki.
Damuwar da marasa ƙiba ke fama da itaA duniyar da sama da rabin al'ummar ƙasashen Yamma ke da ƙiba, siraran mutane na fama da damuwa saboda wahalar da suke fuskanta yayin da suke ƙoƙarin ƙara ƙiba.
Michelle Salem ƴar wasan ninƙaya a Miami Beach, ta bayyanawa BBC yadda siranta da rashin ƙiba ke hana ta sanya kayan da take so.
“Samun kayan da suka yiwa jikina daidai yana yi min wahala, sai na je layin kayan ƙananan yara ko matasa, wani lokacin likitoci suna zargin ina ɗauke da cutar Anorexia,”
A wannan gaɓa, Liliana Carvajal ta faɗi yadda jama'a ke yi mata kallon maras lafiya ko yar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi.
"Ana kira na da maras lafiya, wadd ke ta'ammali da kayan maye ko kuma lalurar anorexia. A wasu lokutan mutane za su dinga kiranka da sunaye kamar ramammiya, idan ba ka sani ba kuma ka gamsu da nauyin jiki da kamanninka.