Kungiyoyin Premier biyu wato Manchester City da Chelsea za su buga wasan karshe a Champions League ranar Asabar a Porto, Portugal.
Wannan ne karon farko da City wadda ta lashe Premier League ke fatan lashe Champions League a karon farko.
Chelsea kuwa wadda ta kare babbar gasar Ingila ta bana a mataki na hudu, ta taba cin kofin a 2012.
Ana kuma sa ran 'yan kallo 16,500 ne za su shiga filin wasa na Estadio do Dragao domin kallon wasan karshen.
Wannan shi ne karo na hudu da za su kece raini a tsakaninsu a kakar nan.
2020/2021
Premier Leaugueranar Asabar 8 ga watan Mayun 2021
FA CUPranar Asabar 17 ga watan Afirilun 2021
- Premier League ranar Asabar 3 ga watan Janairun 2021
- Chelsea1 - 3 Man City
Sun kuma taba haduwa a gasar zakarun Turai
EURO CUP Winners Cup ranar Laraba 28 ga watan Afirilun 1971
- Manchester City 0 - 1 Chelsea
- EURO CUP Winners Cup ranar Laraba 14 ga watan Afirilun 1971
- Chelsea 1 - 0 Manchester City
Yadda Manchester City ta kai wasan karshe:
Gida - Karawar cikin rukuni Porto 3-1 nasara
Waje - Karawar cikin rukuni Marseille 3-0 nasara
Gida - Karawar cikin rukuni Olympiakos 3-0 nasara
Waje - Karawar cikin rukuni Olympiakos 1-0 nasara
Waje - Karawar cikin rukuni Porto 0-0 canjaras
Gida - Karawar cikin rukuni Marseille 3-0 nasara
Waje - Zagaye na biyu wasan farko Borussia Monchengladbach 2-0 nasara
Gida - Zagaye na biyu wasa na biyu Borussia Monchengladbach 2-0 nasara
Gida - Quarter-final wasan farko Borussia Dortmund 2-1 nasara
Waje - Quarter-final wasa na biyu Borussia Dortmund 2-1 nasara
Gida - Daf da karshe wasan farko Paris St-Germain 2-1 nasara
Gida - Daf da karshe wasa na biyu Paris St-Germain 2-0 nasara
Koci Pep Guradiola na fatan lashe Champions League karo na uku a tarihi, bayan biyun da ya dauka a Barcelona a 2009 da kuma 2011.
Shi kuwa Thomas Tuchel na fatan cin kofin a karon farko. Sai dai a bara ya kai Paris St Germain wasan karshe, inda Bayern Munic ta yi nasara da ci 1-0.
Wannan ne kuma karo na uku da kungiyoyin Ingila ke buga wasan karshe a Champions League, inda Manchster United ta doke Chelsea a 2008
A kuma kakar 2019 an kara tsakanin Tottenham da Liverpool, wanda Liverpool ta yi nasara.
Zai kuma zama karo na 14 da kungiyar Ingila za ta lashe Champions League ko kuma European Cup.
Yadda Chelsea ta kai karawar karshe:
Gida - Wasannin cikin rukuni Sevilla 0-0 canjaras
Waje - Wasannin cikin rukuni Krasnodar 4-0 nasara
Gida - Wasannin cikin rukuni Rennes 3-0 nasara
Waje - Wasannin cikin rukuni Rennes 2-1 nasara
Waje - Wasannin cikin rukuni Sevilla 4-0 nasara
Gida - Wasannin cikin rukuni Krasnodar 1-1 canjaras
Waje - Zagaye na biyu wasan farko Atletico Madrid 1-0 nasara
Gida - Zagaye na biyu wasa na biyu Atletico Madrid 2-0 nasara
Waje - Quarter-final wasan farko Porto 2-0 nasara
Gida - Quarter-final wasa na biyu Porto 0-1 rashin nasara
Waje - Daf da karshen farko Real Madrid 1-1 canjaras
Gida - Daf da karshe na biyu Real Madrid 2-0 nasara
Idan City ta yi nasara za ta zama ta shida daga kungiyoyin Ingila da ta lashe kofin, ba wata kasa da ke da sama da uku.
Olivier Giroud ya ci kwallo shiga a gasar zakarun Turai ta bana, inda dan wasan Borussia Dortmund, Erling Haaland da na Paris St Germain, Kylian Mbappe ke gabansa.
Timo Werner na Chelsea ya ci kwallo hudu a gasar iri daya da wadanda Ferran Torres da kuma Riyad Mahrez suka ci wa Manchester City.
Kungiyar Etihad ta ci kwallo 25 har zuwa wasan karshe, ita kuwa ta Stamford Bridge guda 22 ta zura a raga.