BBC Hausa of Wednesday, 18 January 2023

Source: BBC

Abin da ya kamata ku sani kan wasan Palace da Man United

Crystal Palace za ta karbi bakuncin Manchester United Crystal Palace za ta karbi bakuncin Manchester United

Crystal Palace za ta karbi bakuncin Manchester United a kwantan wasan mako na bakwai a gasar Premier da za su kara a Selhurst Park ranar Laraba.

Palace tana ta 12 da maki 22 a teburin Premier, United tana ta hudu da maki 38 iri daya da na Newcastle ta uku da tazarar maki daya tsakani da Man City ta hudu.

Sai dai mai tsaron bayan Palace, Joachim Anderson ba zai yi wasan ba, sakamakon raunin da ya ji a karawa da Chelsea ranar Lahadi.

Hakan ne ya sa James Tomkins zai maye gurbinsa.

Dan wasan da United ta dauka aro Wout Weghorst ya shirya buga karawar, sai dai United na auna koshin lafiyar Anthony Martial da Marcus Rashford.

Diogo Dalot da kuma Jadon Sancho na ci gaba da jinya, yayin da saura kati daya ya rage na gargadi ga Casemiro da Fred daga nan su yi hutun hukunci.

Karawa tsakanin Palace da United

Crystal Palace ta ci Manchester United 1-0 a wasan karshe a bara, nasarar farko da ta samu kan United a gida tun bayan 1991.

Palace na fatan cin United karo biyu a jere a karon farko a tarihin haduwarsu a wasannin tamaula.

United ta yi rashin nasara a haduwa uku daga shida baya a karawa da ta yi da Palace.

Crystal Palace

Palace ta yi rashin nasara a karawa hudu daga Premier League biyar baya da kasa cin kwallo ko daya a fafatawar.

Watakila Palace ta kara rashin nasara ta uku a jere karkashin Patrick Vieira:, bayan da ta taba yin haka tsakanin Nuwamba zuwa Disambar 2021.

Palace ba ta ci wasa tara da ta yi a lik da kungiyoyin da ke goman farko teburi ba a kakar nan, wadda ta yi canjaras uku aka doke ta shida.

Ta kuma yi rashin nasara a wasa hudu a gida kawo yanzu kamar yadda ta yi a bara. Kuma a wasannin hamayya da kungiyoyin Landan ta barar da makin.

Wasa 13 Palace ta yi rashin nasara a Premier League da ta buga ranar Laraba, tun bayan da ta doke Aston Villa a Fabrairun 1993, kenan ta yi canjaras bakawi ta kuma ci shida.

Watakila Wilfred Zaha ya buga wasa na shida a jere a Premier League ba tare da ya ci kwallo ba a karon farko tun rashin kokari tsakanin Janairu zuwa Afirilun 2021.

Zaha ya ci United kwallo uku a wasa uku da ya buga a baya da ya fuskanci tsohuwar kungiyarsa.

Manchester United

Idan United ta yi nasara zai zama na 10 a jere a dukkan fafatawa, wasa 14 a jere United ta ci shekara 14 baya a tarihi karkashin Sir Alex Ferguson.

Manchester United ta yi nasara a wasa biyar a jere a Premier League.

United ce kadai da ta lashe dukkan Premier League idan ta fara zura kwallo a raga a kakar nan, wasa daya ne ta raba maki a irin wannan kwazon shi ne wanda ta yi 1-1 da Southampton cikin watan Fabrairun 2022.

Wannan shi ne wasan farko da United za ta buga a waje a 2023, wasa biyar da ta yi nasara a waje a kakar nan da 1-0 ne tazata da ta yi nasara.

Marcus Rashford ya zura kwallo a wasa bakwai a jere a dukkan karawa, na farko a United mai wannan bajintar tun bayan Cristiano Ronaldo a Afirilun 2008.

Sai dai kuma Rashford ya kasa cin kwallo a wasannin waje a Premier League 25 tun bayan 2-2 da Leicester City ranar 1 ga Kirsimetin 2020.

Dan wasan Argentina, Lisandro Martinez, wanda ya lashe kofin duniya a Qatar na bikin cikar ranar haihuwarsa ranar Laraba, mai shekara 25.