Akwai mutane da dama da ke fama da matsalar ƙarancin jini, ba a Bangladesh ba kaɗai. Amma mutane da dama ba su fahimci alamomin matsalar ba.
Misali, mutane ƙalilan ne suka san irin matsalolin da ƙarancin jini ke haifarwa.
Amma me ya sa mata suka fi fuskantar ƙarancin jini? Me ya sa ba ta fiya shafar maza ba?
Me ne ne ƙarancin jini?
Rashin isasshen jini ba wai yana nufin rasa jini bane amma idan ƙwayoyin halitta na jini ba su kai adadin da ake so ba, shi ne ake samun ƙarancin jini.Mutumin da ke fama da ƙarancin jini na nufin jikinsa ba ya samun jinin da ke da isasshiyar iska.
Rashin isasshen jini babbar matsala ce da ta addabi lafiyar al'umma. Yara da mata ne suka fi fama da wannan matsala a faɗin duniya.
Akasari matsalar ta fi shafar matasa da ƴan mata da mata masu jinin al'ada da mata masu juna biyu da matan da suka zo haihuwa.
A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya, kashi 40 cikin 100 na yara ƴan watanni shida zuwa watanni 59, sai kashi 37 cikin 100 na mata masu shekara 15 zuwa 49 suna fama da rashin isasshen jini a faɗin duniya.
Me ya sa ake samun cutar ƙarancin jini?
A cewar asibitin Mayo, babbar cibiyar kula da lafiya a Amurka, rashin isasshen jini na faruwa ne sakamakon rashin isassun ƙwayoyin halitta na jini. Hakan na iya faruwa idan:- Jiki ba ya iya samar da isassun ƙwayoyin halitta na jini
- Rashin jini na janyo ƙarancin ƙwayoyin halitta na jini kafin a yi aiki
- Jiki na lalata ƙwayoyin halitta na jini
Saboda haka nan jiki ba ya iya samar da isassun ƙwayoyin halittar jini saboda rashin sinadarin.
Akwai dalilai da dama da ke haifar da matsalar rashin isasshen jini amma muhimmin abin da ke janyo matsalar shi ne ƙarancin sanadarin iron a jiki.
Sai dai baya ga rashin jini sanadiyyar sanadarin iron, akwai wansu nau'ukan cutukan ƙarancin jinin, waɗanda suka haɗa da:
1. Ƙarancin jini sanadiyyar ƙancin sanadarin vitamin
2. Ƙarancin jini sanadiyyar kamuwa da ƙwayoyin cutuka
3. Ƙarancin jini mai kashe ɓargo
4. Ƙarancin jini mai ƙona jini
5. Amosanin jini na cutar sikila
Alamomin karancin jini
Da zarar aka samu karancin sanadarin ‘hemoglobin’ a cikin jini, mutum zai fara jin gajiya a tattare da shi.Daga nan kuma za a ji ba a jin cin abinci.
Hukumar kula da lafiya ta Birtaniya ta bayyana wadannan abubuwa da za a ambata a kasa a matsayin alamomin karancin jini:
1. Kasala
2. Saurin gajiya
3. Saurin bugun zuciya da yin haki cikin kankanin lokaci
4. Wasu alamomin karancin jinin kuma su ne numfashi sama-sama, sanyi a tafin hannu da tafin kafa, zafi a cikin kirji da kuma yawan ciwon kai.
Haka nan wasu kan fuskanci matsaloli kamar na zazzabi da kuma gudawa.
Abin da ya sa mata suka fi fuskantar ƙarancin jini
Cibiyar nazari kan lafiyar zuciya da huhu da kuma jini ta Amurka, wasu mutanen sun fi wasu shiga cikin haɗarin kamuwa da lalurar ƙarancin jini sanadiyyar tsarin rayuwarsu, Misali -Mata sun fi maza shiga haɗarin samun ƙarancin jini musamman sa'ilin da suke fama da wasu nau'uka na rashin lafiya.
Hakan na faruwa ne sanadiyyar halittarsu.
Mata kan fuskanci fitar jini daga jikinsu a kowane wata sanadiyyar jinin al'ada.
Wasu lokuttan jinin kan zuba fiye da kima ko kuma ya daɗe yana zuba fiye da yadda aka saba.
Kuma ɗaya daga cikin abubuwan da ke haifar da cutar rashin jini shi ne fitar jini da ga jiki.
Baya ga jinin al'ada, sai kuma shayarwa da ɗaukar ciki.
Mata kan rasa jini ta hanyar jinin al'ada da lokacin haihuwa yayin da suke rasa sanadarin iron a lokacin shayarwa, in ji farfesa Alam.
Wani abu da ke sanya ƙarancin jini shi ne tsutsar ciki.
Mutane da dama ba su kula da tsaftar jiki kamar wanke hannu kafin cin abinci ko kuma tsaftar abincin.
Sanadiyyar haka sukan haɗiyi ƙwayayen tsutsotsi waɗanda kan rayu a cikinsu.
A lokacin da tsutsotsi suka sha jinin ɗan'adam hakan kan kawo raguwar yawansa da kuma haifar da ƙarncin sanadarin iron, wanda hakan zai haifar da lalurar ƙarancin jini.
Abun da ya kamata ku ci don kauce wa karancin jini
Domin kauce wa cutar karancin jini, ya kamata a rika cin abinci mai kunshe da sanadarin iron.Daga cikin irin wannan abinci akwai alayyahu, da wake da ayaba da hanya da kifi da madara da kwai da kuma nama.
Idan ya kasance abincin da mutum ke ci ba ya da yawan sanadarin iron, kuma aka rika shan ganyen shayi da yawa, hakan zai haifar nakasu ga jiki wajen zumar sanadarin na iron.
Haka nan idan nau’ukan abinci masu dauke da sanadarin iron suka gaza wajen magance karancin jini, to hakan zai sa a bukaci amfani da magungunan da akan bayar da za su cike gurbin sanadaran.
Farfesa Alam ya kuma ce wani lokaci yakan kai ga sai an yi karin jini.
Sai dai a cewar sa ya kamata duk wani mataki da za a dauka ya kasance likita ne ya bukaci a yi hakan.
Babban abin da ya kamata a yi a lokacin da mutum ke fama da karancin jini shi ne a gano abun da ya haifar da haka sannan a dauki matakin magancewa.