BBC Hausa of Monday, 11 December 2023

Source: BBC

Abin da ya sa muka sadaukar da albashinmu ga mutanen Tudun Biri — Ndume

File foto of Nigerian Senate File foto of Nigerian Senate

'Yan Majalisar dattawan Najeriya 109 sun sanar da sadaukar da albashinsu na wata guda ga dangin mutanen da harin kuskuren da rundunar sojin Najeriya ta kai garin Tudun Biri, da ke karamar hukumar Igabi, a jihar Kaduna ya yi ajalinsu.

'Yan Majalisar sun ce za a yi amfani da kudin, da yawansu ya kai Naira miliyan 109, wato miliyan guda daga kowanne sanata domin hidimtawa mutanen, da zummar rage masu radadin halin da suke ciki.

Sanata Ali Ndume, mai tsawatarwa a majalisar dattawan Najeriyar, wanda kuma ke cikin 'yan Majalisar da suka ziyarci jihar ta Kaduna a ranar Lahadi don jajantawa mutanen, ya shaida wa BBC cewa, an riga an yi asarar rai, amma akwai bukatar a taimaka wa iyalan mamatan.

Ya ce, “ Za a ba wa gwamnan jihar Kaduna kudin, domin ko da muka kai masa ziyarar jaje mun fahimci cewa shi ma ya damu kwarai da gaske a kan taimakon da yakamata a yi wa irin wadannan mutanen.”

‘Yan majalisar sun kuma nanata aniyar ganin an gudanar da sahihin bincike, don gano yadda lamarin ya faru, da kuma hukunta waɗanda bincike ya tabbatar da akwai hannunsu.

Ya ce,”Mun amince a binciki yadda wannan hari ya faru, domin ni a iya sanina irin wannan kuskuren kai wa mutanen da ba su ji ba su gani ba hari da sojojin Najeriya suka yi ya kai 16.

"A jihata Borno, an sha samun irin wannan harin," in ji shi.

Sanata Ali Ndume, ya ƙara da cewa irin wadannan hare hare sun zamo abin damuwa domin ba sau daya aka taba samun irin haka ta faru ba, kuma mutanen da aka kashe a irin wadannan hare haren kuskuren jimillarsu ya kusa kai wa 500, a cewarsa.

“Don haka bai kamata a ci gaba da kai irin wadannan hare hare ba, saboda jami’an tsaro an san aikinsu shi ne tabbatar da tsaro da kare rayukan al’umma, amma kuma su zo suna kai irin wadannan hari, zai zama ke nan kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba aikin da suke ke nan.”

Ndume ya ce, “ Ina tabbatar da cewa mu ‘yan majalisa za mu yi iya bakin kokarinmu don ganin an binciki wannan lamari da kuma tsayar da shi saboda gaba.”

Ya ce binciken da ya kamata a yi tare da bayar da shawarar ɗauko masu bincike masu zaman kansu kuma kwararru su gudanar da bincike a kan harin, sannan a yi binciken da wuri kuma a gani a kasa.