BBC Hausa of Monday, 26 June 2023

Source: BBC

'Abin da ya sa na tuba da shan miyagun ƙwayoyi'

Hoton alama Hoton alama

Sha da kuma safarar miyagun ƙwayoyi matsala ce da ta addabi duniya baki ɗaya, musamman a ƙasashe masu tasowa kamar a nahiyoyin Afirka da Amurka.

Hakan ya sa Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta ware kowace ranar 26 ga watan Yuni a matsayin Ranar Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi ta Duniya ko kuma Ranar Ƙwayoyi ta Duniya.

Taken ranar ta wannan shekara shi ne: "Rayuwar mutane a farko: daƙile tsangwama da nuna wariya, da tsaurara ɗaukar matakai".

Domin yaƙi da matsalar, ƙasashe da dama na ɗaukar matakai masu tsauri, ciki har da hukuncin kisa ga masu safarar ƙwayoyin.

Albarkacin wannan rana, wasu da suka yi mu'amala da miyagun ƙwayoyin a baya kuma suka tuba sun faɗa wa BBC Hausa dalilin da ya sa suka tuba.

'A da ni nake taimaka wa wasu abokaina kafin na fara shan ƙwaya'

Dan Malam Mai Caji matashi ne da ya tashi a ƙwaryar birnin Kano kuma cikin sa'a, kamar yadda bayyana, abokai suka jefa shi cikin harkar shaye-shaye.

Matashin mai shekara 29 a yanzu, ya tsinci kansa cikin ƙwaya tsamo-tsamo ne a lokacin da ya fara aikin gini.

"To idan muka je sai a ce mana idan muka sha wannan ƙwayar ba za mu gaji ba, duk simintin da za mu ɗauka ba za mu ji shi a jikinmu ba," in ji matashin mazaunin unguwar Ƙoƙi.

Ya ƙara da cewa kyauta aka riƙa ba su ita a lokacin amma daga baya abin ya zame musu jiki, inda suka fara sayen ta da kuɗinsu.

To ko ya aka yi Ɗan Malam ya tuba daga shan ƙwaya?

"Dalili gaskiya shi ne [kare] mutunci da kuma abokaina da kuma taso da su," a cewarsa. "Da ni nake kare wa wasu faɗa, ni nake yi musu wasu abubuwan ma na rayuwa.

"Amma tun da na shiga wannan hali [shan ƙwaya] idan mutane suka gan ni sai su dinga ƙyamata ta. In na yi magana ma sai a ce illar ƙwaya ce.

"Ina so na shiga cikin 'yan uwana na jini amma sai su dinga ƙyamata ta saboda halin da na jefa kaina a ciki."

Ɗan Malam ya ce yanzu haka shirin aure yake yi.

'Bibiya da iyayena ke yi ce ta sa na tuba'

Shi kuwa wani matashi da ya nemi a ɓoye sunansa ya bayyana cewa abokai ne suka tsunduma shi cikin ta'ammali da miyagun ƙwayoyi.

Ya ce yankin da ya taso a birnin Kano ya taka muhimmiyar rawa a rayuwarsa, yana mai cewa ba zai iya kauce wa lamarin ba a lokacin da yake yaro.

"Idan za mu je filin wasan ƙwallo ko kuma gidan dambe da abokai ake tafiya, abokinka zai miƙo maka kuma dole ka karɓa," in ji shi.

"Mu a da abubuwan da ake sha ba su fi sholi ba, ko madarar sukudaye, amma daga baya sai ƙwayoyi suka fito."

Cikin dalilan da suka sa ya tuba akwai bibiya da 'yan uwansa suka dinga yi game da rayuwarsa da kuma makarantar Islamiyya, wadda bai daina zuwa ba duk da shaye-shayen da yake yi.

"Bibiya da iyayena ke yi da kuma 'yan uwa ce ta sa na daina. Kuma Allah ya sa ba na ƙin karatu, ina zuwa makarantar Islamiyya da ake yi da dare."

Haka nan, ya ce daina shiga cikin mutanen da ke shaye-shaye ma ya taimaka masa.

Rahoton cibiyar Harm Reduction International (HRI) ya nuna cewa zartar da hukuncin kisa kan laifukan da suka shafi miyagun ƙwayoyi ya ƙaru da fiye da kashi ɗaya cikin huɗu a 2022.

Aƙalla mutum 303 aka yanke wa hukuncin kisa a ƙasashen duniya 18, wanda ƙarin kashi 28 ne cikin 100 a kan adadin na 2021.

Ya ƙara da cewa ya zuwa watan Maris na wannan shekarar, akwai mutum 3,700 da ke tsare a faɗin duniya saboda laifukan ta'ammali da miyagun ƙwayoyin.

"Ba wai Allah ne ke jarrabar mutum da shan ƙwaya ba, mutum ne ke jefa kan sa ciki," in ji Ɗan Malam Mai Caji.