BBC Hausa of Wednesday, 13 December 2023

Source: BBC

Abu biyar da ke da ɗaure kai a rikicin siyasar Rivers

Tsohon gwamnan Rivas, Nyesom Wike Tsohon gwamnan Rivas, Nyesom Wike

Rikicin siyasar jihar Rivers, ta yankin Neja Delta mai arziƙin man fetur a kudancin Najeriya, na ci gaba da tayar da ƙura da jan hankula a faɗin ƙasar, watanni ƙalilan bayan kammala babban zaben 2023.

Da yawa na kallon rikicin a matsayin wata gwagwarmayar ƙwatar iko tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara na jihar, da kuma ubangidansa Minista Nyesom Wike, wanda aka yi imani shi ne ya ɗora Fubara a kan karagar mulki.

Akasarin abin da ke bakunan mutane, shi ne ya yi wuri a ce rikicin siyasa mai zafi irin wannan ya ɓarke, jim kadan da fara sabon wa'adin mulki.

Kuma tsananin balbalowar da wutar rikicin ta sake yi kwanaki ƙalilan bayan wani yunkurin sasantawa da Shugaba Bola Tinubu ya yi, ya jefa 'yan Najeriya cikin kakabi da rike haɓa cikin mamaki.

Mun duba wasu muhimman abubuwa guda biyar da za su taimaka muku kara fahimtar wannan rikici:

Ayyana korar 'yan majalisa 25

Batu na baya-bayan nan shi ne korar 'yan majalisar dokokin jihar ta Ribas guda 25, bayan majalisar dokokin ɓangaren Gwamna Siminalayi Fubara ta ayyana kujerunsu a matsayin wadanda babu kowa a kai.

Shugaban majalisar Onarabul Edison Ehie ne, ya bayyana haka yayin wani zama da sauran 'yan majalisa huɗu suka gudanar a gidan gwamnati.

Matakin na zuwa ne kwana ɗaya bayan 'yan majalisar dokokin jihar 27 sun bayyana sauya sheƙa daga jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya, zuwa jam'iyyar APC mai mulki.

Kwanan baya, ƙurar rikicin ta yi sama, lokacin da 'yan majalisar suka yi yunƙurin tsige Gwamna Fubara daga kan mulki.

Ana kallon 'yan majalisar dokokin 27, a matsayin masu biyayya ga ministan Abuja, Nyesom Wike, wanda ya kammala mulkin jihar ranar 29 ga watan Mayu, kafin Siminalayi Fubara ya dare kan karagar.

Onarabul Edison Ehie ya ce daukar matakin korar 'yan majalisa 25 da suka yi, ya dace da tanadin tsarin mulkin Najeriya wanda in ji shi, ya ce duk ɗan siyasar da ya sauya sheƙa daga jam'iyyar da ya ci zabe, to sai ya bar kujerar da aka zabe shi.

Yanzu dai, da wuya cikin hanzari a iya sanin makomar kujerun 'yan majalisar da aka kora. Shin waɗanda aka kora ɗin da kuma tsohon ubangidan Gwamna Fubara, za su haƙura su ajiye makamansu. Ko kuma za su koma su sake lale, ta hanyar ɗaukar wani mataki ƙila har da na zuwa kotu, don samun fashin baƙi.

Sannan ko hakan zai kawo ƙarshen rikicin, ko kuma zai sake ɓallo wata sabuwar balahira ne kawai?

Kudurin kasafin kuɗi ga majalisa mai mutum hudu

Da safiyar Laraba ne, Gwamna Siminalayi Fubara ya gabatar da kudurin kasafin kuɗin jihar na 2024, gaban majalisar dokokin Ribas mai mutum huɗu.

Majalisar wadda ta kunshi bangaren da ke biyayya ga Fubara, ta gudanar da zama ne a gidan gwamnati, mai yiwuwa saboda samun tabbacin tsaro.

Rahotanni sun ce 'yan majalisa huɗu zuwa biyar ne a cikin 32 suka halarci zaman na ranar Laraba.

Matakin na zuwa ne bayan gwamnati ta rusa ginin majalisar dokokin Ribas.

Masana shari'a dai sun ce bisa tanadin tsarin mulkin Najeriya, sai kashi daya cikin uku na daukacin 'yan majalisa ne za su iya gudanar da halartaccen zaman muhawara. Ko da yake, sun ce akwai togaciya.

Gwamna Fubara ya gabatar da kudurin kasafin kudin na naira biliyan 800 ne, mai yiwuwa domin nuna cewa aikin majalisar dokokin jihar ta Ribas bai tsaya ba, duk da wutar rikicin da ke ci gaba da turnuke siyasar Ribas.

Kila, gwamnan ya yi hakan ne a wani bangare na ci gaba da fito da tasirinsa, kwana guda bayan rinjayen 'yan majalisar masu biyayya ga Minista Nyesom Wike sun sauya sheka.

Lalubo hanyoyin da 'yan majalisa guda huɗu na bangaren gwamnan, za su ci gaba da aiki, duk da karancin adadinsu, zai ba da hasken cewa kada mage ba yanka ba ne.

Rushe ginin majalisar dokoki

Mai yiwuwa wannan mataki, zai shiga kundin tarihin siyasar Najeriya, a matsayin ɗaya daga cikin rikice-rikicen siyasa mafi zafi da kasar ta taba gani.

Rahotanni sun ce motocin rusa gini da ake kira mai loma guda biyar ne, aka girke cikin rakiyar jami'an tsaro don rugurguza ginin zauren majalisar.

Masu aiko da rahotanni daga Ribas sun ce an rushe ginin majalisar ne babu zato ba tsammani, don haka ba a fitar da kayayyakin da ke cikin ginin ba.

Kwamishinan yada labaran jihar Ribas, Mista Joe Johnson daga bisani ya yi bayani ga manema labarai cewa gwamnatin jihar ce ta dauki matakin rushe ginin.

A cewarsa, matakin ya zo ne bayan shawarwarin da kwararru suka bai wa Gwamna Siminalayi Fubara cewa ginin na da hatsari ga 'yan majalisar dokokin su ci gaba da shiga don gudanar da harkokinsu.

Gwamnati ta kafa hujjar cewa ginin ya samu matsala ne sanadin gobarar da ta tashi ranar 30 ga watan Oktoba, bayan fashewar wasu abubuwa.

Sai dai wasu na da ra'ayin cewa matakin rushe majalisar, zai sake kassara bangaren Nyesom Wike, ta hanyar kara hana su damar samun halartaccen wurin da za su gudanar da zaman yin muhawara.

Barazanar tsigewar da Gwamna Fubara ya fuskanta a baya-bayan nan, ta isa rikita duk wani dan siyasa, har ya yi nazarin matakan da za su fisshe shi a wannan fage.

Yayin da wasu ke cewa matakin rusa ginin wani bangaren gwamnati mai ikon cin gashin kansa da aka gina da dukiyar al'umma, wani karan tsaye ne ga dimokradiyya, kuma rashin fifita muradin al'ummar jihar a kan na kashin kai.

Hukuncin kotu

Duka wadannan matakai da suka faru ranar Laraba sun auku ne bayan wani umarnin babbar kotu a Ribas da ta hana bangaren da aka yi imani yana biyayya ga Nyesom Wike karkashin jagorancin Martins Amaewhule yin amfani da karfi wajen shiga ginin majalisar jihar.

Sabon shugaban majalisar dokokin Ribas Edison Ehie ne ya garzaya gaban kotun, inda ya nemi ta bayar da wannan umarni.

Tun farko dai, Gwamna Fubara ya ce bai kamata a shiga ginin majalisar ba saboda ana gudanar da gyare-gyare a ciki.

Umarnin na kotun Mai shari'a Monina Danagogo ya yi gargadi a kan amfani da 'yan banga da 'yan sanda wajen shiga harabar majalisar ta karfi da yaji.

Rahotanni sun ce matakin shi ne ya share fage ga 'yan majalisar dokokin jihar hudu zuwa biyar su gudanar da zaman majalisa ba tare da katsalandan ba.

Me APC da PDP suka ce

Jam'iyyar PDP ta Gwamna Siminalayi Fubara dai ta fitar da wata sanarwa da yammacin Laraba, inda ta sanar da cewa tuni ta nemi Inec ta gudanar da zabuka a cikin lokacin da tsarin mulkin Najeriya ya kayyade, don cike gibin da ta ce an samu a majalisar dokokin Ribas.

Ta ce bayan ayyana kujerun 'yan majalisar dokokin jihar 25 a matsayin babu kowa a kansu, PDP ta umarci mashawarcinta na kasa kan harkokin shari'a ya fara daukan duk matakan da suka dace na shari'a, don tabbatar da ganin an yi sabon zaben cike gibi a Ribas.

Zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a ji wani martani a kan balahirar da ta faru ranar Laraba a jihar Ribas daga jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ba.

Sai dai, tun ranar Talata shugaban kwamitin riko na APC a Ribas ya soki lamirin umarnin kotun da ake ganin ya bai wa bangaren Gwamna Fubara, damar da suka nema.

Mista Toni Okocha ya soki Mai shari'a Monina Danagogo da goyon bayan wani bangare a wannan rikici, har ma ya yi barazanar kai korafi game da alkalin ga Majalisar kula da Alkalai ta Kasa.

A cewarsa, “Muna sani wannan wata makarkashiya ce da aka shirya don a bai wa Gwamna Fubara damar gabatar da kasafin kudi gaban zauren majalisar dokoki mai mutum hudu kuma ba za mu zauna, mu bari hakan ta faru ba”.