BBC Hausa of Monday, 24 October 2022

Source: BBC

Abu biyar kan Ba'indiyen da zai zama sabon firaministan Birtaniya

Rishi Sunak Rishi Sunak

Rishi Sunak ya kasance wanda zai zama firaministan Birtaniya karo na uku a cikin watanni biyu bayan lashe zaben shugabacin jam'iyyar Conservative. Sunak ya yi wannan nasara ne bayan doke Penny Mardaunt wadda ita kaɗai ta fafata da shi a takarar shugabancin jam’iyyar. Sabon firaministan zai jagoranci kasar ne cikin yanayi mai tattare da manyan kalubale na tattalin arziki. Sai dai kuma mene ne asalinsa kuma ya rayuwarsa take kafin wannan lokaci? Mun nazari masu muhimman abubuwa game da rayuwarsa. Asalinsa da na iyayensa An haifi mahaifinsa Yashvir Sunak a kasar Kenya, yayin da aka haifi mahaifiyarsa Usha a kasar Tanganyika. Kakannin Rishi Sunak 'yan asalin yankin Punjab ne da ke kasar Indiya wadanda suka yi ƙaura daga gabashin Afirka zuwa Birtaniya a shekarun 1960. Mahifiyarsa, Usha babbar manajar ce a kamfanin magunguna na Weston Pharmacy a Southampton, a yayin da shi kuma mahaifinsa Yashvir Sunak likita ne. An haifi Rishi Sunak a babban asibitin Southampton ranar 12 Mayun 1980. Iyayensa sun zauna a unguwar Richmond Gardens kafin daga baya su ka koma gida mai daki shida a unguwar Spindlewood, bayan da aka haifi ƙaninsa Sanjay tare da ƙanwarsa Raakhi. Matakin iliminsa Mista Sunak ya halarci makarantar Firamare mai zaman kanta ta Oakmoun da ke Southampton wacce aka rufe ta a shekarar 1989. Daga nan kuma sai ya ci gaba da karatu a makaranar Romsey. Daga nan ya tafi sakandiren kwana a kwalejin Winchester a Hampshire, wadda makarantar kudi ce mai tsadar gaske. Domin kuwa kuɗin makaranta a zangon karatu na 2022/2023 ya kai fam 45,936. Bayan ya kammala sai ya tafi jami'ar Oxford inda ya karanta Falsafa da siyasa da tattalin arziki. Ya kuma samu digirinsa na biyu a fannin kasuwanci a jami'ar Stanford da ke Amurka. Siyasarsa A shekara ta 2015 aka fara zaɓarsa a matsayin ɗan majalisa ƙarƙashin jam'iyyar 'yan ra'ayin rikau ta Conservative da ke wakiltar Richmond a gundumar Yorkshire. Ya zama ƙaramin minista a gwamnatin Theresa May, kafin ya zama babban sakataren baitul-malin kasar a gwamnatin Boris Johnson. A watan fabarairun 2020 aka ɗaga likkafarsa zuwa ministan kuɗi, to sai dai daga baya ya ajiye muƙaminsa yana mai cewa kudurorinsa kan tattalin arziki sun sha bamban da na Firaminista Boris Johnson wanda matsin lamba ya tilastawa sauka daga mulki. Ana tunanin yana ɗaya daga cikin 'yan majalisa mafiya kuɗi a Birtaniya, to sai dai bai taba yin sakaci a bainar jama'a kan yawan dukiyar da ya mallaka ba. Amma ana tunanin cewa daɗewarsa a hakar kasuwanci ta sa ya zama miloniya tun yana ɗan shekaru 20, kafin ya shiga siyasa. A wannan shekarar an zafafa bincike kan harkokin kuɗin Sunak da danginsa, lamarin da ya jefa batun biyan harajin matarsa cikin ruɗani, ko da yake daga bisani ta amince za ta fara biyan haraji ga Birtaniya a kan kuɗaɗen da take samu a ketare, tare da zummar kawar da matsin lambar siyasa a kan mijinta Aurensa A 2009 ya auri matarsa Akshata Murthy, 'yar gidan attajirin kasar Indiya NR Narayana Murthy, mamallakin kamfanin fasaha na Infosys, Inda suka haifi 'ya'ya mata biyu. Yaƙin neman zaɓensa Bayan saukar Boris Johnson daga mulki, mista Sunak ya sanar da yaƙin neman zaɓensa wanda ya yi wa take da 'Rishi ya shirya'. Fafatawar neman ɗarewa kan kujerar firaminstar ta yi zafi ne tsakaninsa da Liz Truss, wadda ta samu nasara da kuri'u masu yawa, inda ta zama Firaminista. Bayan da Liz Truss ta ajiye aiki kwana 45 bayan zamanta Firaminista, a yanzu mista Rishi Sunak ya zama sabon Firaministan Birtaniya. Mista Sunak zai karbi mukamin Firaminista a cikin mawuyacin hali na matsin tattalin arziki.