BBC Hausa of Monday, 13 February 2023

Source: BBC

Abubuwa biyar da gwamnoni suka ce kan wa'adin tsofaffin kuɗin Najeriya

Hoton alama ta sabobin naira Hoton alama ta sabobin naira

A ranar Asabar ne gwamnaonin Najeriya suka gudanar da taro domin tattaunawa kan halin da al'ummar ƙasar ke ciki.

Ɗaya daga cikin abubuwan da gwamnonin suka mayar da hankali a kai shi ne batun sauya fasalin kuɗin Najeriya.

Bayan kammala taron, gwamnonin sun fitar da sakamakon abin da suka cimma ta hannun shugaban ƙungiyar gwamnonin na Najeriya Aminu Waziri Tambuwal.

Wasu daga cikin muhimman bayanai da sanarwar ta ƙunsa su ne:

'Babban Bankin Najeriya na yi wa al'umma ƙwace'

Takardar ta ce "muna da yaƙinin cewa abin da Babban Bankin Najeriya ke yi a yanzu shi ne yi wa al'umma ƙwace, ba musayar kuɗi ba kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada."

Bayanin ya ƙara da cewa dalilin gwamnonin na faɗin haka shi ne kuɗaɗen da ake yarda mutane su cira daga asusunsu bayan sun mayar da tsofaffin kuɗaɗensu banki ba su taka kara sun karya ba.

Hakan na faruwa ne a cewar bayanin, ta hanyar ƙayyade kuɗaɗen da mutane da za su iya cirewa.

Take ƴancin al'umma

Sanarwar ta ƙara da cewa hanyar da Babban Bankin na Najeriya (CBN) ke bi wajen aiwatar da wannan tsari na sauya fasalin kuɗi na haifar da damuwa kan take ƴancin al'umma na samun kuɗi da kuma amfani da su ta yadda suka ga dama.

Rashin fahimtar girman kasuwanci da ba a yi wa rajista ba

Sanarwar ta ce idan aka kwatanta yawan hada-hadar kuɗi da ake yi maras rajista, da kuma ƴan kuɗaɗen da babban bankin ya saki, hakan ya nuna cewa CBN ɗin bai fahimci irin maƙudan kuɗaɗen da ake buƙata domin hada-hada da su ba.

Haɗarin faɗawa cikin durƙushewar tattalin arziƙi

Sanarwar ta ƙara da cewa ƙarancin isassun sababbin kuɗin da al'umma za su yi hada-hada da su na da matukar illa ga tattalin arziƙin ƙasar.

Ta ce hakan zai haifar da "sabuwar kasuwar musayar kuɗi ta bayan fage, da tsananta tashin farashin kayan masarufi, da wanzuwar dogayen layuka da cunkoson mutane a cibiyoyin cire kuɗi na ATM.

"Hakan na da haɗarin jefa ƙasar cikin durƙushewar tattalin arziƙi wadda Babban Bankin Najeriya ya haddasa."

Ya kamata gwamnati ta saurari ƙorafin al'umma

Sanarwar ta ce duk da cewa Ministan Shari'a na Najeriya, Abubakar Malami ya ce gwamnati za ta yi biyayya ga hukuncin kotu, har yanzu ba a ga wani sauyi a harkar kuɗi na ƙasar ba.

Saboda haka, a cewar sanarwar ya kamata gwamnati ta bi umurnin kotu, ta kuma saurari kiraye-kirayen al'umma da sauran masu ruwa da tsaki, ciki har da na majalisar magabatan ƙasar.