BBC Hausa of Friday, 2 June 2023

Source: BBC

Abubuwan da suka kamata ku sani kan madugun ƴan adawar Senegal Ousmane Sonko

Ousmane Sonko Ousmane Sonko

Shi ne ya zo na uku a zaɓen shugaban ƙasa na 2019.

Babban ɗan adawa da gwamnatin shugaba Macky Sall, wanda kuma ya so sake tsayawa takara a babban zaɓen shugaban Senegalda za a yi a ranar 25 ga watan Fabrairu, 2024.

A yanzu an yanke masa (Ousmane Sonko) hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari saboda bayan kama shi da laifin 'gurɓata matasa', sannan an kuma yanke masa tarar CFA 600,00.

Ousmane Sonko, wanda shi ne jami`in gwamnati mai kula da haraji da kadarori, ya samu bunƙasa a siyasa cikin ƴan shekaru ƙalilan, bayan an kore shi daga aikin gwamnati, ya zama ɗan majalisar dokokin ƙasar, sannan ya zama magajin garin Ziguinchor.

Me ya sa aka kori Ousmane Sonko daga aikin gwamnati?

Shekaru goma da suka wuce, jama'a ba su wane ne Ousmane Sonko ba.

Korar sa daga aikin gwamnati a ranar 29 ga watan Agustan 2016 ce ta sa ya yi suna.

An kore shi ne daga aikin gwamnati ba tare da biyan sa haƙƙinsa na fansho ba, kuma aka zarge shi da saɓa wa dokar kiyaye sirrin ƙasa.

A lokuta da dama, ya musunta yin almubazzaranci da dukiyar al’umma.

Kuma Ousmane Sonko ya musanta zargin karya dokar bayyana sirrin ƙasa.

Siyasa

Ousmane Sonko shi ne ya kirkiro jam'iyyarsa ta siyasa maio suna African Patriots of Senegal for Work, Ethics and Fraternity (PASTEF) a cikin shekara 2014 a lokacin yana ma'aikacin gwamnati.

Amma soke rajistar ta da aka yi a shekarar 2016 ne ya taimaka masa shiga fagen siyasa.

A shekara ta 2017, ya shiga cikin zaɓen 'yan majalisa kuma aka zabe shi mataimaki shugaban majalisar dokoki ta kasa.

Shekaru biyu bayan haka, a cikin 2019, Ousmane Sonko ya gabatar da takararsa ta neman shugaban ƙasa.

Ya zo a matsayi na uku, inda ya samu kashi 15.76 cikin ɗari na kuri'un da aka kada, inda shugaban Macky Sall ya lashe zaɓen a karo na biyu.

Domin samun kuɗin gudanar da ayyukan jam'iyyarsa, Mista Sonko ya rinƙa yin gangamin tara kudade, wanda shi ne ya zama babban kamfen da aka yi a tsakiyar watan Janairu, ya tara sama da kuɗi CFA miliyan 300 a cikin sa'o'i 24.

A yanzu dai, Ousmane Sonko ya bayyana takararsa a zaben shugaban kasa da ake shirin gudanarwa a 2024, sai dai ana iya samun cikas.

An yanke masa hukuncin daurin shekaru 2 a gidan yari bayan samun sa da laifin "gurɓata matasa"

Ousmane Sonko ya ƙi bayyana a gaban shari’ar da ake masa na fyade da aka yi a ranar 23 ga Mayu, 2023.

Ya yanke shawarar yin zaman sa a kudancin Senegal, a Ziguinchor, birnin da shi ne magajin gari.

Daga karshe dai kotu ta yanke hukunci a ranar ɗaya ga watan Yunin 2023.

An yanke wa Ousmane Sonko hukuncin ɗaurin shekaru biyu a gidan yari saboda "gurɓata matasa" tare da cin tarar kuɗi CFA 600,000.

Kwanakin baya da suka wuce, Mista Sonko ya sanar da komawarsa Dakar. Ya ƙaddamar da wani abin da ya kira ayarin ‘yanci, abin da zai dauke shi daga Ziguinchor zuwa Dakar ta hanyar wasu manyan biranen kasar.

Jami’an tsaro su ne suka katse tattakin bayan da aka samu arangama tsakanin FDS da magoya bayanta.

An kama Ousmane Sonko na ɗan lokaci sannan aka sake shi daga baya.