BBC Hausa of Tuesday, 13 June 2023

Source: BBC

Abubuwan da ya kamata ku sani kan dokar ba wa ɗalibai bashin karatu a Najeriya

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya saka wa dokar bai wa daliban kasar na manyan makaratun da suka fito daga gidajen masu karamin karfi damar samun rancen karatu maras ruwa daga gidauniyar bayar da bashin karatu ta kasar.

A watan Nuwamban shekarar da ta wuce ne majalisar dokokin kasar ta amince da kudurin dokar, da ke neman kafa wata gidanauniyar za ta rika ba daliban manyan makarantun kasar bashin kudin makaranta.

Sabuwar dokar dai ita ce irinta ta farko a Najeriya kuma in ji Shugaban ma’aikata na Fadar Shugaban Kasar Femi Gbabiamila, wanda shi ne ya kawo kudurin dokar lokacin yana kakakin majalisa, za ta inganta kasar domin babu wani yaron Najeriya da za a hana wa damar samun ilmi mai zurfi saboda rashin kudi.

Gabanin fito da wannan dokar dai, bankuna a kasar kan bayar da bashin kudin karatu ne ga iyayen yara ko shi ma da tsauraran sharudda da kuma takaitaccen lokacin biya.

Da yawa dalibai masu rangwamen gata a kasar kan jingine karatu mai zurfi saboda rashin kudi ko kuma su rika wasu sana’aoi ko ayyukka da ba su kamata a ce suna yi ba a lokacin suke karatu don dai su samu abin biyan kudin karatun.

Abubuwan da dokar ta ƙunsa

1- Karkashin dokar za a kafa Bankin Ilimi na Najeriya, wanda shi ne zai rika tsarawa da sa ido da kuma aiwatar da bayar da bashin karatun.

2-Bisa tanadin sabuwar dokar, dalibi zai iya samun bashin ne ta hannun ma’aikatar ilimi ta kasar, kuma ba zai fara biyan bashin ba sai ya samu aiki bayan kammala karatu da kuma hidimar kasa ta shekara daya (NYSC).

3- Dalibai za su iya neman bashin ta hanyar makarantun da suke, inda makarantun za su shige musu gaba.

4- Za a tantance dalibi a ga ko ya cancanci karbar bashin.

5- Dokar ba za ta amfani duk dalibin da zai yi karatu a wajen Najeriya ba, ko kuma mai karatu a makarantar da ba ta gwamnati ba.

Wanda ya cancanci karɓar bashin

  • Kafin ka cancanci samun rancen sai da farko ka samu gurbin karatu a wata babbar makaranta ta jiha ko ta tarayya - walau jami'a ko kwalejin kimiyya da fasaha( polytechnic ) ko kwalejin ilimi ko kuma makarantar koyon sa'ar hannu


  • Dole ne kudin da kake samu ko kuma iyayenka suke samu ya kasance kasa da naira dubu 500 a shekara.


  • Dole ne dalibi ya gabatar da masu tsaya masa, akalla mutum biyu wadanda za su kasance ma'aikatan gwamnati da suka yi shekara 12 a aiki.


  • Dalibi zai iya gabatar da lauya wanda ya kai shekara 10 da aiki ko kuma wani ma'aikacin shari'a.


  • Idan dalibi a makarantar da ba ta gwamnati yake ba ba zai samu wannan rasnce ba.


  • Babu maganar wariya ko nuna bambanci ga wani dalibi bisa jinsi na mace ko namiji ko addini ko wata nakasa.


  • Bashin zai kasance na biyan kudin makaranta ne kawai.


  • Waɗanda ba za a bashin ba

  • Idana ya kasance ka ci bashin Bankin Ilimin a baya kuma ka ki biya.


  • Idan har wata makaranta ta tabaKo kuma wata kotu ta taba samunka da laifin rashin gaskiya ko zamba, to ba ka cikin wadanda za su ci moriyar tsarin.


  • Idan an taba kama ka da laifin da ya danganci miyagun kwayoyi, wannan ma zai hana ka samun rancen.


  • Idan har wani daga cikin mahaifanka, walau uwa ko uba ba su biya bashin da aka ba su ba na dalibtar to ba za a ba ka ba.


  • Yadda za ka biya bashin

  • Yana daga cikin aikin Bankin Ilimin ya rika bibiyar wanda aka bai wa bashin ya san lokacin da zai gama karatun, da aikin yi wa kasa hidima har zuwa samun aiki domin tabbatar da mutum ya fara biya a lokacin da ya dace.


  • Bankin zai hada kai da inda kake aiki domin tabbatar da ana yankar kudin da ya kamata a rika sanya wa a asusun da ya ba ka bashin.


  • Duk wanda aka bai wa bashin zai fara biya shekara biyu bayan kammala aikin yi wa kasa hidima (NYSC).


  • Za a rinka yankar kashi 10 cikin dari na albashinka ana biya.


  • Idan aikin kanka da kanka kake yi, wato ba a karkashin wani kake aikin ba, to gwamnati za ta rinka karbar kashi 10 cikin dari na yawan ribar da kake samu a duk wata, inda za ka rika kai kudin da kanka bankin; Kwana sittin da zamanka mai sana'ar kai za ka mika bayanan harkokin kasuwanci ko aikin naka, misali bankinka da wajen da kake zaune da abokan sana'ar da wadanda suke da hannun jari a ciki da sauran bayanai.


  • Idan ka ki biyan bashin za a iya yi maka hukuncin daurin shekara biyu a gidan yari ko tarar naira dubu 500 ko kuma a hada wa mutum duka biyu.