Tottenham za ta mayar da hankali don cimma yarjejeniyar ɗauko ɗan wasan gaba na Wales da ke taka leda a Nottingham Forest, Brennan Johnson, mai shekara 22, bayan Brighton ta sha gabansu wajen ɗaukar aron Ansu Fati, ɗan ƙwallon gaba mai shekara 20 daga kulob ɗin Barcelona na ƙasar Sifaniya. (Standard)
Ƙungiyar mai inkiyar Spurs, na duba yiwuwa a ƙarshen hada-hadar ‘yan ƙwallo kan yunƙurin ɗauko ɗan wasan gaban Chelsea na Ingila, Conor Gallagher, mai shekara 23. (Telegraph)
Kulob ɗin Al-Ittihad na Saudiyya a shirye yake ya biya fam miliyan 150 a kan ɗan ƙwallon gaban Liverpool na ƙasar Masar, Mohamed Salah, mai shekara 31. (Telegraph)
Fulham ta yi watsi da tayin farko da Bayern Munich yi wa ɗan ƙwallonta na tsakiya daga ƙasar Portugal mai shekara 28, Joao Palhinha. (90min)
Fulham ɗin kuma ta tuntuɓi Manchester United a kan yiwuwar cimma wata yarjejeniya don ɗan wasan tsakiya na Scotland, Scott McTominay, mai shekara 26, yayin da suke ƙoƙarin neman wanda zai maye gurbin Palhinha. (Sky Sports)
Ɗan wasan tsakiyar Tottenham na ƙasar Denmark, Pierre-Emile Hojbjerg, mai shekara 28, shi ma Fulham tana kallon sa a matsayin zaɓin da zai iya maye Palhinha, tuni dai ta taya shi fam miliyan 60. (Standard)
Haka zalika, Fulham dai a shirye take ta yi wa Nottingham Forest shigar sauri, a kan ɗan ƙwallon tsakiyar Monaco daga Faransa, Youssouf Fofana, mai shekara 24. (Football Insider)
Bayern Munich ta janye daga tattaunawa da Chelsea a kan Trevoh Chalobah, mai shekara 24, bayan ƙungiyar mai inkiyar Blues ta ƙi rage farashin fam miliyan 50 da ta yi wa ɗan ƙwallon bayan na Ingila. (90min)
An samu ci gaba a tattaunawar da Manchester United ke yi don cimma yarjejeniyar aro sannan su sayi ɗan ƙwallon tsakiyar Fiorentina daga ƙasar Moroko, Sofiyan Amrabat mai shekara 27. (90min)
Wolves ta yi tuntuɓa a kan ɗan wasa Harrison Reed, mai shekara 28, sai dai Fulham ta ƙi amincewa, saboda tana alla-alla ta riƙe ɗan ƙwallon tsakiyar da wata sabuwar yarjejeniya. (Athletic)
Brentford ta gabatar da tayi mafi tsada da ta taɓa sayen wani ɗan wasa na fam miliyan 34, ga ɗan ƙwallon gaban PSV Eindhoven daga ƙasar Belgium, Johan Bakayoko, mai shekara 20. (90min)
Tottenham ta yi watsi da wani tayi daga Burnley a kan ɗan wasan bayanta na ƙasar Ingila mai shekara 29, Eric Dier. (Football Insider)
Ɗan ƙwallon gaba na Ingila Keinan Davis, mai shekara 25, ya kusa kammala yarjejejniyar komawa kulob ɗin Aston Villa a matakin dindindin daga Udinese, (Nicolo Schira)
Duk da sha’awar da ƙungiyoyin Real Betis da Besiktas suka nuna, ɗan wasan gaban Aston Villa na ƙasar Brazil Philippe Coutinho, mai shekara 31, har yanzu ya fi son tafiya ƙungiyar Al-Duhail ta ƙasar Qatar. (Fabrizio Romano)
Ɗan bayan Italiya, Leonardo Bonucci, mai shekara 36, ya cimma yarjejeniyar fatar baki don shiga kulob ɗin Union Berlin a kan kwanturagin dindindin daga Juventus. (Fabrizio Romano)
Wolves na sha’awar ɗauko ɗan wasan gaban Southampton na ƙasar Scotland Che Adams, mai shekara 27, suna kuma tunanin yin yunƙuri don ɗaukar ɗan ƙwallon gaban Leicester City daga Najeriya Kelechi Iheanacho, mai shekara 26, a ƙoƙarin ƙarfafa zaɓin da suke da shi na gwanayen kai hari a ‘yan wasansu. (Mail)
Yunƙurin AC Milan na ɗaukar ɗan wasan gaban Porto daga ƙasar Iran Mehdi Taremi, mai shekara 31, ga alama ya tashi a tutar babu lokacin da aka gabatar da wani ejan a cikin harkar bayan tun farko ƙungiyoyin sun amince da cinikin a kan farashin fam miliyan 12.8. (La Gazzetta dello Sport )
Nottingham Forest sun farfaɗo da tattaunawa da PSV Eindhoven don kammala wata yarjejeniya a kan ɗan ƙwallon tsakiyar Ivory Coast Ibrahim Sangare, mai shekara 25. (Mail)
Fulham ta koma kan teburin tattaunawar ciniki da Chelsea a kan Callum Hudson-Odoi, ɗan wasa mai shekara 22, a daidai lokacin da Nottingham Forest ke gab da cimma yarjejeniya a kan ɗan ƙwallon gefen na Ingila. (Evening Standard)
An yi wa Hannibal Mejbri, ɗan shekara 20, alƙawarin wani muhimmin matsayi a Manchester United, matuƙar ya yarda ya ci gaba da zama a kulob ɗin, duk da yake hankalin ɗan ƙwallon tsakiyar na Tunisya, ya tafi Sevilla da Anderlecht da ke nuna sha’awa kansa. (Mirror)
Southampton ta amince da cinikin da zai iya ƙaruwa zuwa fam miliyan 12 a kan ɗan wasan gaban Sunderland daga Scotland Ross Stewart, mai shekara 27. (Athletic)