BBC Hausa of Thursday, 22 June 2023

Source: BBC

Alhazan da ke jiran a kwashe su daga Najeriya zuwa ƙasa mai tsarki

Hoton alama Hoton alama

Kwana uku gabanin hukumomi a Saudiyya su rufe filayen jirgin saman ƙasar, har yanzu akwai dubban maniyyatan da ke jiran a kwashe su zuwa Ƙasa mai Tsarki daga Najeriya.

Duk da haka, hukumar aikin hajji ta ƙasar ta ce tana da ƙwarin gwiwar kwashe dukkan maniyyatan da suka rage.

Ya zuwa ranar Talata da yamma, hukumar ta ce ta yi nasarar kwashe mutum 67,000 zuwa Saudiyya.

Daraktan sashen gudanarwa na hukumar, Dr Ibrahim Sodangi ya ce mafi yawan alhazan da suka kwashe ya zuwa jiya Talata suna birnin Makkah.

Jami'ai a hukumar sun ce Saudiyya ta keɓe wa Najeriya kujerun maniyyata 95,000 don aikin hajji a bana.

Bisa wannan ƙididdiga, akwai maniyyata kimanin 28,000 da suka rage a ƙasa, suna jiran a kwashe su zuwa Saudiyya a faɗin Najeriya.

Sai dai Dr Sodangi ya faɗa wa manema labarai cewa:"Abin da ya rage mana a cikin allocation ɗinmu na mahajjata 95,000 mu kammala, na mahajjatan jihohi guda shida, shi ne 6,000," in ji Dr Sodangi.

Bai dai fayyace ko adadin maniyyata 95,000 ɗin ya haɗa har da masu bin jiragen yawo na 'yan kasuwa ba, ko kuma na hukumarsu ne gaba ɗaya.

Bayanai sun ce an gaza kwashe wasu maniyyatan zuwa Ƙasa mai Tsarki ne, saboda ƙalubalan da aka sha fuskanta irin na soke tashin jiragen sama.

Haka zalika, jami'ai a wasu jihohin sun buƙaci wasu alhazan, su koma gida bayan sun kwashe makonni suna zaman jira a sansanonin alhazai.

Kwamishinan tsare-tsare na hukumar Hajji ta ƙasa, Sheikh Suleiman Momoh dai ya ce daga ɓangarensu, sun yi nasarar kwashe kashi 90% a cikin adadin maniyyatan bana.

A Najeriya dai, maniyyata aikin hajji na biyan kuɗin zuwa Ƙasa mai Tsarki ne ta hannun hukumar alhazai ko kuma ta hannun 'yan kasuwa da aka fi sani da suna jirgin yawo.

Dr. Ibrahim Sodangi dai ya ɗora alhaki kan hukumomin jin daɗin alhazai na jihohi a kan duk wata gazawa ta kwashe maniyyatan bana zuwa Saudiyya.

Ya zargi wasu jihohi da karɓar kuɗaɗen aikin hajji fiye da adadin kujerun da aka keɓe musu.

"Kaman ire-iren wannan, tun da ba su yi musu biza ba, ba su ba su travelling arrangement ba, ai ba za a zo a ce an ba ka an ba ka (kujeru) 500, ka je ka karɓi 700. Ya za ka yi da wa'yannan 200?" Sodangi ya tambaya.

Ya ce dole ne a samu irin wannan ƙorafi, saboda waccan matsala.