A yau ne za a fara muhawara a shari'ar dan sandan nan farar fata Derek Chauvin, wanda ake zargi da kashe bakar fata George Floyd, a Minneapolis a Amurka a shekarar da ta wuce.
Ana dai tuhumar Mr Cahuvin da laifin kisa ba da niyya ba da kuma tuhuma biyu ta kisan kai.
An dauki hoton bidiyo a lokacin da dan sandan ya kashe Mr Floyd, aka kuma yada shi a duniya, abin da ya haddasa zanga-zangar yaki da nuna wariyar launin fata a Amurkar da ma fadin duniya.
Kusan dukkanin wadanda za su taimaka wa alkali yanke hukunci a shariar, sun ga hoton bidyon da aka dauka na kama George Floyd, wanda ke nuna karar yadda dan sanda farar fata, Derek Chauvin ya kafa guiwarsa a wuyan bakar fata George Floyd, hannunsa daure a baya da ankwa, kwance a kasa, tun yana iya Magana, har ya kasa yana kakari, har ma daga karshe ya kasa, ya kuma mutu a haka , kafin Chauvin ya cire guiwarsa daga wuyan.
A zaman muhawarar na yau, masu taimaka wa alkalin za su fara dubawa su gani ko abin da ya faru ya kai a dauke kisan kai da niyya.
Mutanen da sun kunshi jinsin farare da bakar fata, wadanda aka zaba bayan wani mataki na dogon lokaci da aka dauka, saboda yadda duniya ta sa ido a kan lamarin.
Sai dai masu taimaka wa alkalin za su yi la'akari ne kawai da abin da aka gabatar a gaban alkali ne kawai. Amma kuma duk da haka abin da shari'ar za ta mayar da hankali a kai shi ne batun mutuwar George Floyd din.
Ana sa ran lauya mai kare wanda ake tuhuma zai tsaya kai da fata cewa mutumin yam utu ne a sakamakon kwaya da ya sha ko ya yi amfani da ita da ta wuce ka'ida, da kuma wasu matsaloli na rashin lafiya da yake da su, amma ba wai don dan sanda Chauvin ya yi masa abin da ya yi masa na hana shi numfashi.
Yawanci dai a Amurka ba kasafai ake kama 'yan sanda ko dora musu alhaki kan yadda suke amfani da karfi ba.
Sai dai wannan shari'a za ta kasance tamkar zakaran-gwajin dafi da masu fafutulka da dama za su ga ko al'amura sun sauya a Amurka ko kuma suna nan jiya i yau.
Kuma duniya gaba daya za ta zuba ido ta ga yadda za ta kasance.