BBC Hausa of Friday, 27 January 2023

Source: BBC

Amurkawa sun harzuka kan kisan da 'yan sanda bakaken-fata da suka yi wa wani bakar-fata

Shugaban Amurka Joe Biden Shugaban Amurka Joe Biden

Shugaba Biden ya roki Amurka su kwantar da hankalinsu, yayinda jami'an tsaro ke shirin wallafa bidiyon da ke nuna yada 'yan sanda suka kashe wani bakar-fata bayan azabtar da shi.

Mahukunta a Amurka dai sun samu jami'an 'yan sandan biyar da aka kora daga aiki, da laifin kisan bakar-fatan kwanaki uku bayan tsayar da shi kan zargin karya dokokin tuki a birnin Memphis.

Tuni dai aka nunawa iyalan Tyre Nicholas mai shekara 29 bidiyon yada abin ya faru kafin a sake bidiyo a yau Juma'a.

Lauyoyi sun ce an rinka bugunsa da kafa da kuma naushi da kuma azabtar da shi da lantarki. Dukkanin jami'an da suka kasance bakaken-fata an koresu daga aiki a makon da ya gabata.

Wannan shi ne cin zarafi 'yan sanda na baya-bayanan daya fusata Amurka.

Batun cin zarafin da ‘yan sanda farar fata ke yi wa bakaken fata a Amurka ba sabon abu ba ne, sai dai wannan karon lamarin ya zo da ban mamaki, ganin ana zargin ‘yan sandan hudu bakar fata da lakadawa dan uwansa bakar fata duka.

An nunawa Iyalan Tyre Nichols mai shekara 29, bidiyon abin da ya faru gabannin nunawa jama'a a wannan juma'ar.

A sanarwar da ya fitar ta kafar bidiyo, magajin garin Memphis Jim Strickland, ya nuna bacin rai da takaicin abin da ya faru, inda ya ce lokaci ya yi da za a tabbatar da hakan ba ta kara faruwa ba.

"Tun bayan samun bayanai kan abin da ya faru, na ke fatan ganin an yi sahihin bincike da adalci, hakkin mu ne tabbatar da iyalan Mr Nichols da mutanenmu an karba musu hakkinsu. 

"Abin da 'yan sandan nan suka aikata abin kunya da takaici ne, babu kuma wanda ya fi karfin doka, dole a hukuntasu, za mu tabbatar da hakan."

Wannan batu dai ya taso da tsohon miki a zukatan wadanda 'yan sanda suka ci zarafi ko hallaka 'yan uwansu.

Lora King ta shaidawa BBC yadda ‘yan sanda farar fata su hudu, suka azabtar da mahaifinta Rodney King a shekarar 1990 a Los Angeles, lamarin da aka nada a bidiyo, amma ba a jima ba aka wanke 'yan sanda tare da sakinsu.

"Ta ce lamarin mai tada hankali ne, na kasa amincewa da hakan, ina ganin abin da ya bambanta wanda ya faru a baya da na yanzu, shi ne kirkirar maudu’I a shafukan sada zumunta na zamani da kuma hoton kamarar CCTV mafi inganci.

"Bai kamata abin ya ci gaba da faruwa ba, ba na fatan wani ya samu kan shi a irin wannan yanayin."

Jami'na tsaro na tsare da 'yan sandan, domin gudanar da bincike.

Rahotanni sun bayyana cewa kowanne a cikinsu ya taka rawa a lokacin azabtar da Tyre Nicholas