BBC Hausa of Wednesday, 19 April 2023

Source: BBC

An binne dalibin da aka harbe a harabar jami’ar Sudan

Hoton alama Hoton alama

An halaka wani dalibi a Jami’ar Khartoum bayan da wani harsashi ya same shi yayin da ake ci gaba da gwabza kazamin fada a babban birnin kasar Sudan.

Wani bayani da aka wallafa a shafin Facebook, da BBC ta tantance ya nuna cewa an binne gawar a cikin harabar makarantar bayan da ba a samu tabbacin tsaron fita waje ba.

Sudan ta fada cikin tashin hankali tun bayan rashin jituwar da ta kunno kai tsakanin rundunar sojin kasar da kuma dakarun rundunar sojojin sa-kai.

Gomman dalibai ne da lamarin ya ritsa da su suka makale a ƙasar.

"Mun binne abokinmu bayan samun amincewa daga danginsa da kuma hukumar makaranta. Muna shirin zuwa samo wa sauran dalibai abinci ne,’’ wani dalibi mai karatun lauya, da ke zaune a wani gini a kusa da makarantar ya shaida wa BBC.

"Mu uku ne, sai kawai harsashi ya same shi a kirji. Ba mu iya taimaka masa ba. A yayin da muke kokarin binne abokin namu kuma daya daga cikinmu shi ma harsashin ya same shi a hannu.’’

Duka bangarorin na sojin kasar da na kungiyar sojojin sa-kai ta (RSF) na ikirarin karbe ikon muhimman wurare a birnin Khartoum, inda mazauna wurin ke fakewa daga tashin ababan fashewa da kuma bindiga.

"Muna tsoron duka bangarorin biyu, sojoji da kuma mayakan na RSF, idan suka yi harbi a daidai inda muke.’’

Dalibin ya kuma kara da cewa sauran daliban na kwanciya ne a wani masallaci da ke kusa, a lokacin da lugudan wuta ya fada kan ginin tare da jikkata mutum biyu.

"Muna cikin tsakiyar barin mummunan barin wuta. Akwai hare haren makamai a kusa da mu da ke fadawa kan gidaje.

"Daliban sun shafe kwanaki uku a nan ba tare da abinci ko ruwan sha ba. Halin da suke ciki mai munin gaske ne," Mr Sharif ke bayyana wa a wani bidiyon da ya saka a shafin intanet, a yayin da ake ci gaba da barin wuta.

A wani bidiyon na daban da ke yawo a ko ina a shafukan sada zumunta, wani dalibin ya bayyana yadda gomman dalibai ke barci a kasa a wani dakin ajiyar litattafai na makaranta.

"Mu wajen 88 ne da muka hada da ma’aikata 20, wasu sun manyanta. Halin da ake ciki mai munin gaske ne,’’ ya ce.

"Ba ma iya yin komai, bamu da komai kana jiragen sama na ta shawagi a sama. Muna fargabar katsewar wutar lantarki da ruwan sha.’’

Ya kuma ci gaba da cewa abinci da ruwan sha sun fara karanci amma babu wanda ke son jefa rayuwarsa cikin hadari ya fita daga cikin ginin.

Wata dalibar Najeriya a birnin Khartoum, da ba ta so a ambaci sunansa ta shaida wa BBC cewa ta samu ta fita amma ‘’bata taba samun kanta cikin wannan yanayi ba a rayuwarta.’’

"Mun farka da jin karar harbe-harbe, abin na da matukar tsoro, muna cikin fargaba,’’ ta bayyana, a yayin da ta tsere daga inda ta ke da zama, kuma aka fada mata cewa ta shiga cikin wata motar bas da ke makare da mutane zuwa wurin da ya fi samun kariya.

Ta kuma ce ta samu yin magana da iyayenta da ke cikin damuwa.

"Na yi magana da mahaifiyata jiya amma ta rika jin karar harbe-harbe daga cikin wayata.’’

Makarantu da jami’oi na yin kira ga kungiyoyin bayar da agajin jin kai da su taimaka waje kwashe gomman mutane da daliban da suka makale.

Amma Ghazali Babiker, mukaddashin daraktan kungiyar bayar da agaji ta Médecins Sans Frontières a kasar Sudan, ya bayyana cewa su kan su kungiyoyin bayar da agajin an datse musu hanyoyin kai agajin.

"Yanayin yadda wannan yaki ke faruwa, babu wani wanda zai iya fita ya taka a kan titi, Kowa ya makale a inda yake,’’ ya ce.