BBC Hausa of Saturday, 30 September 2023

Source: BBC

An daina jin ɗuriyar kumbon sama jannati da Indiya ta tura duniyar wata

Tutar Indiya Tutar Indiya

Ana ci gaba da cire rai da cewa kumbon sama jannati da Indiya ta tura duniyar wata zai ci gaba da aiko da saƙonni bayan sandarewa da ya yi sanadiyyar dare mai sanyi da aka yi a duniyar wata kamar yadda masana kimiyyar sararin samaniya daga kasar suka shaida wa BBC.

Amma sun ce za su ci gaba da ƙoƙari har zuwa ƙarshen rana ɗaya ta duniyar wata.

Kwana ɗaya a duniyar wata daidai yake da kimanin kwana 14 a duniyarmu.

A ranar Juma'ar da ta gabata, hukumar kula da sararin samaniyar Indiya, Isro ta ce tana ƙoƙarin tuntuɓar na'urorin da kumbon ya kai duniyar wata, wato Vikram da Pragyaan, sai dai har yanzu ba ta samu wasu bayanai ba.

Kumbon dai ya isa duniyar wata ne a watan Agusta. Kumbon ya kwashe mako biyu yana tattara bayanai da hotuna, inda daga bisani aka kashe na'urorin a lokacin da dare ya yi aduniyar ta wata.

Hukumar Binciken Sararin Samaniya ta Indiya (Isro) ta ce ta yi tsammanin baturan kumbon za su yi caji kuma na'urorin za su sake farfaɗowa domin ci gaba da aiki da zarar rana ta fito a duniyar watan a ranar 22 ga Satumba.

A ranar Juma'a, hukumar ta wallafa a dandalin sada zumuntanta na X (tsohon Twitter) cewa "za su ci gaba da ƙoƙarin tura saƙonni zuwa kumbon". Babu dai wani martani da aka samu daga kumbon zuwa yanzu.

A safiyar ranar Litinin, tsohon shugaban hukumar, AS Kiran Kumar ya shaida wa BBC cewa "kullum tunanin cewa kumbon zai farfaɗo na ƙara dushewa".

Damar kumbon na Indiya da sake farkawa na raguwa saboda tsananin sanyi a duniyar wata, tare da yanayin zafi a maƙurar duniya ta kudu ya ƙaru daga 200C zuwa 250C.

Tsohon shugaban Hukumar nazarin sararin samaniya ta Indiya, ISRO ya yi bayanin cewa kumbon Chandrayaan-3 na da na'urori har da na tura saƙonni da yawa waɗanda wataƙila ba su tsira daga tsananin sanyin duniyar watan ba, in ji Kumar.

Wane muhimmanci wannan shiri na zuwa duniyar wata ke da shi ga Indiya?

Indiya ta kafa tarihi lokacin da kumbon da ta aika ya sauka a maƙurar duniyar wata ta kudu.

Ƙasar ta kuma shiga cikin manyan kasashe da suka samu nasarar sauka a maƙurar duniyar wata ta kudu, bayan Amurka da tsohuwar Tarayyar Soviet da China.

An shirya saukar kumbon na Indiya a daidai farkon rana a duniyar wata, yadda Vikram da Pragyaan za su sami hasken rana na makonni biyu don yin aiki.

Hukumar ta sararin samaniya ta samar da bayanai a kai-a kai kan motsinsu da bincikensu da kuma raba hotunan da suka ɗauka.

Masana sun bayar da misali da kumbon Chang'e4 na kasar China da kuma Yutu2 rover wanda ya farfaɗo a karo da dama bayan fitowar rana.

Amma Isro ta ce idan Vikram da Pragyaan ba su farka ba za su ci gaba da zama a duniyar wata a matsayin jakadun Indiya a duniyar wata".