A karo na farko, an gano wata kada da ta yi wa kanta ciki a gidan namun daji da ke ƙasar Costa Rica.
Dan tayin da ta haifa ya kasance yana da ƙwayoyin halittar gado kimanin kashi 99.9 daidai da na uwarsa.
Akan samu irin wannan lamarin, inda dabbar da ba ta taɓa saduwa ba za ta haihu, wanda ake kira 'virgin birth' a turance.
Sai dai ba a taɓa samun wata kada da irin haka ba.
Masana kimiyya sun ce ana iya gadon irin wannan dabi`ar daga dabbar 'Dinosaur', wato kakannin ƙadangaru, waɗanda su ma ana tunanin za su iya ɗaukar ciki su haihu ba tare da saduwa ba.
Wata kada mai shekara 18 ce da ke Amurka ta nasa ƙwan a watan Janairu na 2018.
Kadar da ta nasa ƙwan an ɗauko ta ne tun tana da shekara biyu, inda aka ajiye ta ita kaɗai a wani ɓangare na wurin ajiye namun daji na 'Parque Reptilania'.
Kadar ta rayu ita kaɗai a tsawon rayuwarta.
Bayan nasa ƙwan ne jami'ai masu kula da dabbobi a wurin da kadar take suka tuntuɓi masana kan haihuwar dabbobi ba tare da saduwa ba daga kwalejin fasaha ta jihar Virginia.
Bayan yin nazari sai suka gano cewar ƙwayoyin halittun gado na jaririn kadan ba su da banbanci da na uwarsa ko kadan, wanda hakan ya nuna cewa jinjirin kadan ba ya da uba.
A wani rubutu da suka yi cikin mujallar 'Royal Society journal Biology Letters sun ce akwai yiwuwar an rinƙa samun irin wannan yanayi tsakanin kadoji, sai dai ba a gane hakan ba saboda ba a mayar da hankali a kai ba.
Sun ƙara da cewa ba sabon abu ba ne a ga namun daji jinsin ƙadangaru suna yin ƙwai koda kuwa sun daɗe ba tare da yin tarayya ba, sai dai sau da dama akan yi watsi da ƙwayayen kan cewa ba za su samar da jinjiri ba. Sai dai wannan abu da aka gano na nuna cewa ya kamata a rinƙa duba irin waɗannan ƙwayaye ko da za a samu waɗanda ke ɗauke da jarirai.
Babu tabbas a kan ko mene ne ke haifar da irin wannan yanayi da dabbobi ke haihuwa ba tare da sun sadu da ƴan uwansu ba.
Sai dai ana ganin cewa an fi samun haka a dabbobi waɗanda ke fuskantar barazanar ƙarewa.