BBC Hausa of Monday, 12 April 2021

Source: BBC

An kai wa tashar nukliyar Iran hari

Hoton tashar nukliyar Iran daga cikin iska Hoton tashar nukliyar Iran daga cikin iska

Wani babban jami'in nukliyar Iran ya ce an kai wa wata cibiyar nukliya ta kasar hari kwana daya bayan da ta gabatar da sabbin injina na zamani na uranium.

Bai fadi ko waye ke da laifi ba amma ya yi kira ga kasashen duniya da su magance ta'addancin nukliya.

Kafofin watsa labarai na Israila sun nuna cewa al'amarin ya faru ne sakamakon harin ta intanet da Israilar ta kai.

Al'amarin baya-bayan nan na zuwa ne yayin da ake kokarin farfado da yarjejeniyar nukiliya ta shekarar 2015 ta hanyar amfani da kafar diflomasiyya wadda Amurka ta fice daga ciki karkashin mulkin Trump a shekarar 2018.

A ranar Asabar shugaba Hassan Rouhani na Iran ya kaddamar da sabbin injinan zamani a Natanz, wanda wuri ne mai muhimanci a shirin inganta uranium na kasar, wanda aka nuna kai tsaye a talbijin.

Hakan ya wakilci wani abin da ya sabawa alkawuran kasar a yarjejeniyar 2015, wacce kawai ke ba Iran damar samarwa da adana iyakantaccen uranium din da za a yi amfani da shi don samar da mai na makamashin nukiliyar kasuwanci.