An kama mutum ashirin da biyar a sassa daban-daban na kasar Jamus bisa zargin yunkurin kifar da gwamnati.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu gungun masu ra'ayin rikau da manyan tsofaffin sojoji sun shirya kai hari a ginin majalisar dokokin kasar, Reichstag, domin su kwace mulki.
Wani dan kasar Jamus da ake kira yarima Heinrich XIII, mai shekara 71, ake zargi da shugabantar masu kitsa kifar da gwamnatin.
A cewae masu shigar da kara na gwamnati, yana daya daga cikin mutum biyu na gungun mutanen da aka kama a jihohi 11 da ke fadin kasar.