BBC Hausa of Saturday, 30 September 2023

Source: BBC

An kama wasu mutane da ake zargin masu garkuwa ne a Taraba

Hoton alama Hoton alama

Rundunar 'yan sandan Najeriya, ta ce ta sami nasarar damƙe wasu mutane da ake zargin masu garkuwa ne don neman kuɗin fansa a sassa daban-daban na jihar Taraba.

Mutanen da adadinsu ya kai ashirin, an cafke wasu daga cikinsu ne yayin da suke ƙoƙarin karɓar kuɗin fansar wasu mutane da suka sace, kuma suka yi garkuwa da su.

A wata tattaunawa da ya yi da BBC mai magana da yawun rundunar 'yan sandan ta jihar Taraba SP Usman Abdullahi Jada, ya ce koken al'umma da rundunar ta riƙa samu lokacin bayan lokaci, yasa Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Yusuf A Sualaiman ya haɗa wata runduna ta musamman domin kawo ƙarshen lamarin.

Lamarin a cewar SP Usman ya fi ƙamari ne a Jalingo babban birnin jihar da ƙauyukan da ke kewaye da shi.

"Mun samu nasarar kama mutum 20 cikin masu garkuwa da mutanen a sassa daban-daban na wannan jiha ta Taraba.

"Akwai waɗanda muka daɗe muna fako da muka kama a birnin Jalingo da suka yi shuhura wajen garkuwa da mutane a yankin unguwannin Mayo dasa da Bayan Sitadiyom da Gunum da dai sauran wurare," in ji SP Usman.

Kazalika ya ce sun kama wasu da ke irin wannan aiki a yankin unguwar Kurmi ɓangaren Ba'isa a wani ƙauye da ake kira Didan.

Ya ce a tsakanin Wukari da Ibbi an kama irin waɗannan mutane da dama in ka gansu ba su yi kalar masu aikata muggan laifuka ba.

"Cikin waɗannan mutane babu wanda aka kama bisa kuskure wanda ba ya da hannu cikin irin wannan mugun aiki, dukkansu masu aikata garkuwa ne.

"Wasu an kama su a daidai lokacin da aka je ba su kuɗin fansa ne. Wasu kuma da bakinsu suka amsa cewa aikinsu kenan: fashi da makami zuwa garkuwa.

"An samu bindigogi masu yawa tare da wasunsu, wasu kuma harsasai da sauran miyagun kayan aiki," in ji SP Usman.

Da yawa daga cikin waɗannan mutane sukan amsa cewa wannan shi ne karon su na farko ko kuma na biyu ko na uku, kamar yadda ya yi bayani.

Amma wasu bayanan da suka bayar na waɗanda suka yi garkuwa da su da kuma yadda suka yi garkuwa da su da kuɗaɗen da suka amsa ne ya ba da hasken da aka gano an shafe tsawon lokaci ana nemansu ruwa a jallo.

'Muna aikin haɗin gwiwa da 'yan banga'

A wani ƙoƙari na ganin an ci gaba da samun irin waɗannan nasarori a faɗin jihar Taraba, kwamshinan 'yanda ya ƙirƙiri wani atisaye na musamman da ya haɗa da 'yan banga da 'yan sanda da kuma jami'an da ke yawon sintiri domin lalubo inda miyagu ke a ko wanne saƙo.

"Akwai wanda muke yi tsakaninmu da sojoji wanda wannan kuma ke ƙarƙashin kulawar gwamnan jihar Taraba Agbu Kefas, in ji SP Usaman, wanda ya ƙara da cewa.

Ya kuma yi kira ga al'ummar gari da su zama ma su bayar da bayanai domin kawo ƙarshen wannan lamari na sata da garkuwa da mutane.

"Yawan bayanan da mutane za su ba mu, adadin sauƙin da za mu riƙa samu wajen daƙile wannan mummunar ta'ada kenan".