BBC Hausa of Sunday, 7 March 2021

Source: BBC

An kashe ƙasurgumin ɗan fashi a Kaduna, an yi wa Buhari rigakafin korona

'Yan bindiga sun sace mutum 60 sun kona garin Ruwan Tofa a Zamfara 'Yan bindiga sun sace mutum 60 sun kona garin Ruwan Tofa a Zamfara

A cikin wannan maƙala, mun duba muhimmai daga cikin labaran da muka wallafa a makon da muke bankwana da shi kamar yadda aka saba.

Jami'an tsaron Najeriya sun yi nasarar kashe ƙasurgumin ɗan fashi mai suna 'Rufai Maikaji' tare da jama'arsa da dama a Jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Wannan ya biyo bayan luguden wutar da dakarun tsaro suka yi wa 'yan fashin dajin a yankin Ƙaramar Hukumar Igabi ta jihar, kamar yadda Samuel Aruwan, Kwamishinan Tsaro na Kaduna, ya sanar ranar Alhamis.

Mista Aruwan ya ce an kashe Maikaji ne da kuma gwammman 'yan tawagarsa a Dajin Malul a ƙarshen watan Fabarairu da ya gabata bayan sun kai hari ƙauyen Anaba, inda suka ƙona gidaje tare da kashe mutane.

Kwamishinan ya ce bayanai sun nuna cewa ƙasurgumin ɗan fashin ne ke aikata ta'asa a ƙananan hukumomin Giwa da Igabi da Chikun.

A cewar Aruwan, garuruwan da suka fi addaba sun haɗa da Iyatawa da Garke da Kumfa da Bakali da Karau-Karau da Galadimawa da Anaba da Kerawa da Hashimawa da Sabon Birni da kuma Buruku.

"An ce 'Rufai Maikaji' ya fara ayyukansa ne a matsayin ɗan aiken wasu manyan 'yan fashi a yankin Sabon Birni na Igabi, inda daga baya ya zama gawurtaccen ɗan fashi," in ji shi.

Yajin aikin 'yan kasuwar Arewa ya tashi farashin kaya a KuduYajin aikin kwana uku zuwa huɗu da 'yan kasuwa masu fataucin kayan gwari zuwa kudancin Najeriya suka yi ya tashi farashin kayayyaki a jihohin kudancin.

Rahotanni sun ce wasu kasuwannin a Jihar Legas sun zama kufai baya ga tashin farashin kayayyaki kamar na hatsi da dabbobi.

Haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu safarar kayan gwari da sauran abinci ta shiga yajin aiki ne don nuna rashin jin dadinta kan rainin da ta ce ana nuna wa 'ya'yanta.

Ƙungiyar ta janye yajin aikin ne bayan ta ce gwamnati ta yi mata alƙawarin biya mata buƙatun nata, inda Gwamnan Kogi ya shiga tsakani domin sasantawa.

Lamari na baya-bayan nan dai shi ne rikicin ƙabilanci na Sasa a jihar Oyo wanda ya kai ga salwantar rayuka da lalata dukiya.

An yi wa Buhari da Osinbajo allurar rigakafin Korona

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya karɓi allurar rigakafin korona a ranar Asabar.

Likitan shugaban ne Dr Shu'aibu Rafindadi ya yi wa shugaban allurar misalin ƙarfe 11:53 a fadarsa a Abuja.

An kuma yi wa mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo allurar bayan yi wa shugaba Buhari.

An kuma gabatar da katin shaidar karɓar allurar ga shugaban da kuma mataimakinsa.

A jawabinsa bayan karɓar allurar, shugaba Buhari ya yi kira ga ƴn Najeriya su fito domin a yi masu allurar.

An sako 'yan matan sakandare ta Jangebe

Gwamnatin jihar Zamfara a Najeriya ta tabbatar da sakin ƴan matan makarantar Jangebe da ƴan fashin daji suka sace.

Gwamnatin ta ce ƴan matan su 279 da aka sace sun shaƙi iskar ƴanci bayan ƙoƙarin da aka yi na ganin sun kuɓuta sannan dukkansu suna cikin ƙoshin lafiya.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne ƴan fashin daji suka kutsa cikin makarantar tare da sace su.

Da sanyin safiyar Talatar nan BBC ta tattauna da gwamna Bello Matawalle na jihar ta Zamfara kuma ga ƙarin bayanin da ya yi:

"Alhamdu lillahi, mun ci nasara ga su an sako su dukansu. Dama guda 279 ne, kuma ga shi yanzu suna shigowa, yanzu muke karbar su da ni da mai dakina. Ga su suna shiga gidan gwamnati yanzu ga baki ɗaya."

Babu jirgin da zai kara sauka ko tashi a Zamfara - Buhari

A ranar Talata, Gwamnatin Tarayya ta sanar da haramta hakar ma'adanai a Zamfara tare da kuma haramta tashin jiragen sama daga cikin jihar.

Mai bai wa shugaban kasar shawara kan harkokin tsaro Babagana Monguno ne ya sanar da hakan lokacin da yake tattauanwa da manema labarai bayan kammala tattaunawar Majalisar tsaro ta kasar a Abuja.

"Shugaban kasa ya amince bisa shawarwarin da muka ba shi, na haramtawa tare da hana duk wasu ayyuka na hakar ma'adanai a jihar Zamfara nan take, har sai baba ta gani.

"Kuma ya umarci ministan tsaro da mai ba da shawara kan harkokin tsaron kan cewa su kai sojoji masu yawa yankin domin dawo da al'amura kamar yadda suke a baya.

"Haka kuma ya amince babu wani jirgi da zai kara tashi daga cikin jahar ta Zamfara, nan take ba tare da wani jira ba."

Kotu ta dakatar da yin muƙabalar Sheikh Abduljabbar da Malaman Kano

Wata kotu a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta dakatar da yin muƙabala tsakanin Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara da malaman Kano da aka shirya yi.

Kotu ta dakatar da yin muƙabalar Sheikh Abduljabbar da Malaman Kano

A ranar Juma'a ne Mai Shari'a Muhammad Jibrin na Kotun Majistire da ke Gidan Murtala, ya yanke hukuncin sakamakon buƙatar da wani lauya mai zaman kansa Barista Ma'aruf Yakasai ya shigar gabanta.

Barista Yakasai dai ya buƙaci a dakatar da gwamnati daga yin muƙabalar ne, saboda hakan ya ci karo da umarnin da kotun ta bayar tun da fari na hana Sheikh Abduljabbar karatu da kuma saka karatukansa a daukacin kafofin yada labaran jihar.

Sai kuma bukatarsa ta biyu da yake son ya shiga cikin waɗanda gwamnatin Kano take ƙara, sai dai ba a amince da wannan ba har sai an sanar da Abuljabbar da kwamishinan ƴan sandan jihar a cewar kotun.

Gwamnatin Kano ta tabbatar da cewa za ta bi wannan umarni na kotu, inda Kwamishinan Shari'a Barista Musa Lawan ya yabbatar da cewa babu muƙabala a ranar Lahadi mai zuwa.

DSS sun sako Salihu Tanko Yakasai, Ganduje ya kore shi daga aiki

A ranar Litinin ne rundunar 'yan sandan farin kaya ta DSS ta sako tsohon mai bai wa gwamnan Kano shawara kan kafafen yaɗa labarai wato Salihu Tanko Yakasai, wanda aka fi sani da Ɗawisu a shafukan zumunta.

An kama shi ne 'yan sa'o'i bayan ya yi kira ga gwamnatin jam'iyyar APC ƙarƙashin shugabancin Buhari da ta "kawo ƙarshen matsalolin tsaro ko kuma su sauka daga mulki".

A gefe guda kuma, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya tuɓe Salihun daga muƙamin mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai bayan waɗncan kalaman nasa.

Wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai Mohammed Garba ya fitar ta ce gwamnan ya ɗauki matakin ne saboda "kalaman rashin kan gado" da yake yi.

"Ya (Salihu) kasa tantancewa tsakanin ra'ayi na ƙashin kansa da kuma ra'ayin gwamnati kan abubuwan da suka shafi al'umma, saboda haka ba za a bar shi ya ci gaba da aiki da gwamnatin da ba ya goyon baya ba," sanarwar ta ambato Mohammed Garba yana cewa.

Ya ƙara da cewa korar ta fara aiki nan take.

An nada sabon Sarki 'Mai Tangale' a Gombe

Gwamnatin jihar gombe da ke arewa maso gabashin Najeriya ta naɗa sabon sarki Mai Tangale na ƙaramar hukumar Ɓilliri.

Malam Danladi Sanusi Maiyamba shi ne ya zama sabon Mai Tangalen kamar yadda wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na gwamnatin jihar Isma'ila Uba Misilli ya fitar a ranar Laraba.

Sanarwar ta ce Gwamna Inuwa Yahaya ya yanke wannan hukunci ne bisa ikon da dokar masarautu ta Gombe ta 2020 ta ba shi.

Ta kuma ce an naɗa Malam Sanusi ne saboda kyawawan halayensa da kuma cancantarsa, kamar yadda kwamishinan ƙananan hukumomi da masarutu Ibrahim Dasuki Jalo ya fada a yayin da yake miƙawa sabon Mai Tangalen takardar ba shi sarautar.

A makon da ya gaba ne aka tafka rikicin addini a ƙaramar hukumar Ɓilliri kan batun wanda za a naɗa a matsayin sabon Mai Tangale, bayan mutuwar tsohon sarkin Dr Abdu Buba Maisharu II.

Kotu a Kano ta ɗaure ɗan ƙasar Kamaru shekara 15 a gidan yari

Wata Babbar Kotun Tarayya a Jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta yanke wa wani ɗan ƙasar Kamaru hukuncin shekara 15 a gidan yari yau Alhamis bisa laifin safarar mutane.

Hukumar hana safarar mutane ta Najeriya wato National Agency for the Prohibition of Trafficking in Persons (NAPTIP), ita ce ta gurfanar da Hoth Simplice-Patrick mai shekara 36 wanda ke zaune a yankin Sabon Gari.

Kamfanin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito Mai Shari'a Sa'adatu Ibrahim-Mark tana bayyana hukuncin ba tare da bai wa ɗaurarren wani zaɓin biyan tara ba.

Ta same shi da aikata laifuka guda uku da aka zarge shi da su.

Mai shari'ar ta ce hukuncin zai fara aiki ne daga watan Yuli na 2020, lokacin da aka kama mai laifin kenan.

Tun farko, lauya mai shigar da ƙara Abdullahi Babale ya ce hukumar NAPTIP tare da haɗin gwiwar rundunar tsaron iyaka sun kama mutumin a watan Yulin 2020.

Lauyan ya ce Simplice-Patrick tare da wani abokin burminsa, wanda ya tsere daga gidansa na Sabon Gari, sun shigar da mata biyu da namiji ɗaya ƙasar Libya ta ɓarauniyar hanya daga Jihar Legas, inda suka biya ta Kano.

'Yan bindiga sun sace mutum 60 sun kona garin Ruwan Tofa a Zamfara

Al'ummar garin Ruwan Tofa na yankin karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara a arewa maso yammacin Najeriya, sun gamu da taskun 'yan bindiga, wadanda rahotanni suka ce sun kona rabin garin da dukiya mai dimbin yawa, kuma suka yi awon gaba da mutane fiye da sittin.

'Yan bindiga sun sace mutum 60 sun kona garin Ruwan Tofa a Zamfara

Hakan ya auku ne yayin da matsalar satar 'yan makaranta ta fara auka wa daliban makarantun jeka-ka-dawo a garin Runka na jihar Katsina.

Yanzu haka jama'ar garin sun tsere, "matsalar nan ta yi mana nauyi, ko shekaranjiya da jiya ma sun kawo mana hare-haren nan. Sun kone mana gari da motoci da shaguna da gidaje, kusan rabin garin sun kone shi," in ji wani dan garin da muka biye sunansa.

Ya ci gaba da cewa ba a samu asarar rai ba amma 'yan bindigar sun harbi wani kuma yanzu haka yana asibiti a kwance.

"Sun tafi da mata da yara da dama, akwai wani mutum mai mata hudu duk sun tafi da matan nasa ko daya ba a bar masa ba. Sun tafi da wakilin maigari da iyalansa," in ji shi.

'Yan fashi sun sake kashe mutum biyar a Kagara ta Jihar Neja

Jim kaɗan bayan sakin ɗaliban makarantar sakandare ta Kagara a Jihar Neja, 'yan bindiga sun sake kai hari yankin, inda suka kashe mutum biyar kuma suka tafi da mata ciki har da masu jego.

Lamarin ya auku ne da safiyar Asabar a daidai loƙacin da ɗliban da malamansu su 41 ke kan hanyar zuwa gidan gwamnatin jihar daga hannun masu garkuwa.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa BBC cewa 'yan bindigar fiye da 100 ne suka far wa ƙauyuka kusan shida a kan babura ɗauke da miyagun makamai a yankin da ke cikin Ƙaramar Hukumar Rafi.

Kazalika, 'yan fashin sun tafi da mutum aƙalla 22, a cewar mutumin wanda ba ya son a ambaci sunansa.

Maharan sun fara shiga ƙauyen Kundu sannan suka wuce zuwa Juwawa da Mai Lamba da Karaku da Unguwar Mai Gayya.

"An ɗan yi musu tirjiya a garin Karaku amma sun kashe mutum huɗu kuma suka tafi da guda ɗaya," a cewarsa. Wani kuma ya ce biyar aka kashe, uku daga ciki kuma 'yan gida ɗaya ne.

Sakataren gwamnatin jihar, Ahmad Matana, ya ce sun tattauna da 'yan fashin da ke aikata wannnan ta'asa "kuma sun shaida mana cewa indai aka yi sulhu da su ba za a sake sace kowa ba".

An kai wa ginin MDD hari a Borno

Majalisar Dinkin Duniya ta ce wasu da ake zargin mayakan jihadi ne sun kai hari kan wani gininta da ake amfani da shi wajen ayyukan agaji a Dikwa a jihar Borno arewa maso gabashin Najeriya.

Majalisar ta ce abin takacin ne ganin yada aka lalata asibiti da wuraren da ta ke ayyukan agaji bayan cinnawa wurin wuta.

Sannan maharan da suka kai harin kan manyan motoci sun wawushe kayan abinci.

Majalisar Dinkin Duniya tace harin zai shafi ayyukan agajinta ga mutane kusan dubu 100 da ke cikin bukatar gagagawa.

Ana dai zargin kungiyar IS ta yammacin Afirka da kai harin.