BBC Hausa of Thursday, 4 May 2023

Source: BBC

An kashe jarumar fina-finan Larabci a musayar wutan Khartoum

Tutar Sudan Tutar Sudan

Mutuwar shahararriyar jarumar fina-finai, da aka kashe a wata musayar wuta da ɓangarorin da ke faɗa da juna suka yi a arewacin Khartoum, ta tayar da hankulan mazauna babban birnin na Sudan.

Duk da haka, ita ɗaya ce kawai a cikin fararen hula masu yawa da har yanzu ke rayuwa a birnin kuma suke ji a jika daidai lokacin da ake ci gaba da gwabza faɗa duk da yarjejeniyar tsagaita wuta ta baya-bayan nan.

Zeinab Mohammed Salih 'yar jarida ce da ke zaune a Omdurman, kusa da babban birnin na Sudan - ta bayyana yadda rayuwar yau da kullum take ga mutanen da rikici ya ritsa da su.

Asia Abdelmajid, wadda ta cika shekara 80 a bana, ta shahara ne saboda rawar da ta taka a fagen wasannin kwaikwayo na daɓe - inda ta fara samun ɗaukaka a wani wasa da ta yi mai taken Pamseeka, cikin 1965.

An nuna wasan kwaikwayonta a babban zauren wasanni na ƙasa da ke Omdurman a lokacin bikin cika shekara ɗaya da juyin-juya-hali na farko a Sudan kan shugaban da ya yi juyin mulkin soja.

Ana ɗaukan ta a matsayin ta farko a fagen wasannin daɓe - kuma ƙwararriyar jarumar fina-finan daɓe ta farko a Sudan, kafin daga bisani ta yi murabus inda ta koma malamar makaranta.

Danginta sun ce an binne ta ne sa'o'i bayan an harbe ta ranar Laraba a filin wata makarantar yara da ta fi aiki a baya-bayan nan.

Babbar kasada ce a yi yunƙurin kai ta maƙabarta.

Babu fayyataccen bayani a kan wanda ya yi harbin da ya kashe ta a artabun da aka yi cikin unguwar Bahri da ke wajen babban birnin.

Sai dai mayaƙan rundunar RSF ta masu kayan sarki, waɗanda ke ƙoƙarin ɓoye sansanoninsu a unguwannin da ke faɗin birnin, na ci gaba da artabu da dakarun soji, waɗanda suka fi son kai hari ta sama.

Mayaƙan RSF sun ce sojoji sun yi ƙoƙarin tura jami'an rundunar 'yan sanda ta musamman a ranar Laraba - amma a cewarsu sun wargaza farmakin da suka kawo ta ƙasa.

Babban jami'in ba da agaji na Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi gargaɗin cewa "niyyar kawo ƙarshen faɗa har yanzu babu ita" bayan ya yi magana da shugabannin dakarun Sudan biyu masu gaba da juna.

Yayin da jirgin yaƙin sojoji ke shawagi a sama lokacin da nake rubutu, kuma saƙonnin Whatsapp ke shigowa da labarai marasa daɗi na ƙawaye da abokaina da rikici ya ritsa da su, muna ji a cikin ranmu cewa babu wani ɓangare da yake ƙoƙarin kawo mummunan artabun da gaske.

"Ina zaune da ɗan'uwana a falo a lokacin da muka ji amo mai ƙarar gaske na wata roka kuma ƙura ta taso ta turnuƙe daga ɗakin abinci - mun ɗauka cewa duka ganuwar gidan ce ta faɗi," abokina Mohamed el-Fatih, wani ɗan jarida ya shaida min.

An yi wa ginin gidan da yake ciki a unguwar Burri, gabas da shalkwatar sojoji a tsakiyar birnin Khartoum, luguden wuta ranar Litinin.

"Maƙwabtana na benen sama da kuma na ƙasana sun yi matuƙar firgita inda suka riƙa kwarma ihu, cikin gaggawa muka fita daga gidan zuwa wata unguwa."

Gaba ɗaya dakarun RSF sun mamaye unguwar da yake kuma a kai a kai ana harbo rokoki daga cikin shalkwatar sojoji, inda aka yi imani Abdel Fattah al-Burhan, babban hafsan sojin Sudan da muƙarrabansa na ciki.

Ita ma ƙawata Hiba el-Rayeh ta tuntuɓe ni cikin tashin hankali bayan an kashe mahaifiyarta Sohair Abdallah el-Basher, wata lauya mai mutunci da kawunnanta biyu ranar Alhamis da ta wuce a wani harin roka da aka harba daga wata gada ta tsallaka Kogin Nilu, inda harin ya nufi Fadar Shugaban Ƙasa. Suna zaune ne a kusa da wurin.

Kawunnanta sun je ne don su taimaka musu kuɓuta a lokacin da aka ayyana ɗaya daga cikin yarjejeniyar tsagaita wuta don ayyukan jin ƙai a makon jiya.

A wata unguwa da ke wajen babban birnin wadda ake kira Khartoum ta 2, yamma da shalkwatar sojoji, wani mai dillancin gidae Omer Belal ya yanke shawarar tsayawa ya tsare gidansa.

Magidancin mai shekara 46 ya aika iyalinsa zuwa wani lardi mai kwanciyar hankali daidai lokacin da shi da sauran maza ƙalilan a unguwar suka tsaya don kare kadarorinsu daga masu wawaso da 'yan fashin da ke yawan kai hare-hare a faɗin birnin.

Gidajen mutane da bankuna da masana'antu da kantunan sayar da kayayyaki da shagunan sayar da tufafi duk an yi musu ƙarƙaf.

Wani aboki, da ya nemi a sakaya sunansa, ya shafe tsawon kwana biyar a wani gidan abinci da ke unguwar Khartoum ta 2 lokacin da faɗan ya ɓarke ranar 15 ga watan Afrilu.

Da ƙyar ya iya kuɓuta a lokacin yarjejeniyar tsagaita wutar farko da ta yi ta tangal-tangal. Da farko ya tafi arewacin birnin kafin ya yanke shawarar fita zuwa ƙasar Habasha ta ƙasa, wata tafiya da ke ɗaukar tsawon kwana biyar.

Yanzu daga Addis Ababa, baban birninn ƙasar Habasha ne ya aiko min da saƙon cewa ya ga tsibi-tsibi na gawawwaki a lokacin da yake barin unguwar Khartoum ta 2.