BBC Hausa of Wednesday, 15 November 2023

Source: BBC

An naɗa Walter Mazzarri a matsayin kocin Napoli

Walter Mazzari Walter Mazzari

Napoli ta kori kocinta Rudi Garcia bayan wasanni 16 kuma ta maye gurbinsa da tsohon kocinta Walter Mazzarri har zuwa karshen kakar wasa ta bana.

Zakarun Serie A sun naɗa ɗan ƙasar Faransa Garcia, mai shekara 59 a watan Yuni, amma ya bar ƙungiyar da maki 10 tsakaninta da Inter Milan wadda ke jagorantar gasar.

Mazzarri ya shafe kakar wasa ɗaya a gasar Premier a Watford a shekarar 2016-17 kafin kwantiraginsa ya kare.

Kocin ɗan ƙasar Italiya mai shekaru 62 ya taɓa horar da Napoli daga 2009 zuwa 2013.

Mazzarri ya ci wa ƙungiyar kofinta na farko cikin shekaru 20 a lokacin da Napoli ta lashe kofin Copa Italia a 2012 bayan da ta doke Juventus a wasan karshe.

Shekara ɗaya bayan haka, ya jagorance su zuwa matsayi na biyu a gasar Serie A - matsayi mafi girma da ƙungiyar ta kai a cikin shekaru sama da ashirin - kuma ya sami gurbin shiga gasar zakarun Turai.

An naɗa Garcia a matsayin kociyan Napoli a lokacin bazara bayan Luciano Spalletti ya bar ƙungiyar domin ya ɗauki lokaci daga wasan a kakar wasan da ta gabata bayan ya ci wa ƙungiyar kofin gasar Serie A na farko cikin shekaru 33.

A halin yanzu Napoli tana matsayi na huɗu a teburi, kuma Empoli mai matsayi na 17 ta doke Garcia a ranar Lahadin da ta gabata.