BBC Hausa of Monday, 12 June 2023

Source: BBC

An nemi jami'o'in Ingila su tashi tseye don hana ɗalibai kashe kansu

Tutar Ingila Tutar Ingila

An ƙalubalanci jami'o'in Ingila da su himmatu wajen ba da fifiko kan lafiyar ƙwaƙwalwa daga nan zuwa watan Satumbar 2024, in ji ministan ilimi.

Idan ba haka ba, Robert Halfon ya ce mahukunta za su yi yunƙurin mai da wannan himma ya zama dole domin jami'a ta kasance a matsayinta.

'Yan majalisar sun yi muhawara kan wata takarda da ta ce jami'o'i da kwalejoji su kasance da hakkin kula da dalibai.

Iyalan da 'ya'yansu suka kashe kansu a matsayin ɗalibai ne suka fara.

Fiye da mutane 100,000 ne suka rattaba hannu kan takardar koken, suna masu kira da cewa a fara yi wa ɗalibai irin kulan da ake yi wa ma’aikata.

Sai dai daga gwamnatin da ɓangaren ilimin sun ce ƙarin dokar ba za ta yi daidai ba.

A yayin muhawarar, 'yan majalisar sun ba da misali da yadda aka ce ɗalibai su bar jami'o'i ta saƙonin Email, da kuma iyayen da ba a sanar da su game da matsalolin lafiyar ƙwaƙwalwar 'ya'yansu ba.

Wani ɗan majalisar ya ce ɗalibai sun fuskanci “irin caca” idan aka zo batun ingancin samar da lafiyar ƙwaƙwalwa a faɗin ɓangaren.

Mista Halfon ya ce dokar aikin kulawa "na yiyuwa ba zai zama mafi inganci ba" amma "ba ya rufe kofa kan dokar ba nan gaba".

Ya ce ya rubuta wa jami’o’i wasiƙa inda ya buƙace su da su shiga cikin yarjejeniyar kula da lafiyar ƙwaƙwalwa – wani tsari ne da ƙungiyar Student Minds domin taimaka wa jami'o'i wurin ɗaukar lafiyar ƙwaƙwalwa da muhimmanci.

Mista Halfon ya ce jami'o'i 61 sun riga sun yi rajista, amma Jami'o'in UK (UUK) na da mambobi 140 kuma "lokaci ya yi da sauran su ma su shiga layi"

Ya ƙara da cewa: “Ina da yaƙinin cewa manyan makarantu za su iya fuskantar wannan ƙalubale, amma na bayyana sarai cewa idan wannan amsa bai gamsar ba zan wuce gaba in nemi ofishin ɗalibai ya duba cancantar sabon sharaɗin rajista a kan lafiyar ƙwaƙwalwa."

Jami'o'i a Ingila suna buƙatar yin rajista tare da OFS don kiran kansu "jami'o'i", su samu damar bayar da nasu digiri, da kuma samun taimakon kuɗi daga kafofi daban-daban, da ɗaukar alibai daga kasashen duniya.

Har ila yau, Mista Halfon ya ce wata sabuwar hukumar kula da musamman za ta gabatar da manufofin da jami'o'i za su bi, da kuma shirin taimaka musu wajen gano daliban da ke cikin hadari nan da karshen wannan shekara, tare da bayar da rahoton karshe nan da watan Mayun 2024.

Mr Halfon also said a new taskforce would propose targets for universities and a plan to help them better identify students at risk by the end of this year, with a final report due by May 2024.

Kuma ya ce za a yi nazari a kasa kan mutuwar daliban jami’a.

'Natsatsiya kuma mai kulawa'

Daga cikin wadanda suka je Landan domin muhawarar akwai Bob da Maggie Abrahart, ‘yarsu Natasha ta kashe kanta a Jami’ar Bristol, a shekarar 2018, a ranar da za ta ba da jawabi a wani babban wurin lacca.

Natasha ta kasance na ta fuskantar matsalar shiga jama'a wanda ya sa ta ke gudun magana a gaban bainar jama'a - kuma bayan mutuwarta, iyayenta sun kai karar jami'ar saboda rashin yin gyara.

Sun yi nasara a wani bangaren shari’ar tasu, a karkashin dokar daidaito, amma alkalin bai gamsu da cewa jami’ar ta biya hakkin kulawa da Natasha ba, yana mai cewa “babu wata ka’ida ko wata kafa da ta tabbatar da wanzuwar irin wannan aikin kulawa da jami’a ke baiwa dalibi".

Iyayen da ke zama a Nottinghamshire, sun ce Natasha ta kasance "mutum mai son kulawa sosai" wanda don hakan take son yin karatun kimiyyar a jami'ar. Kuma sun gamsu da batun "samar da ilimi cikin aminci", "na samun kulawan da ya kamata.''

Koken ya bukaci sanya duk daliban da ke da hakkin kulawa don kare wadanda ke kasa da shekara 18, da ma'aikata, daga "lalacewar da za a iya gani" ta hanyar rauni kai tsaye ko gaza daukan mataki.

Amma kungiyar UUK ta ce wannan abu ne da ba zai yiwu ba, kasancewa ba shi ne matakin da ya dace don kula da dalibai ba.

Wasu kungiyoyi masu iin wannan aikin na iya samun dalibai 50,000 da su k yi wa rijista, kuma yawancinsu ba a cikin jami'ar suke zaune ba, a cewar ta

Shugaban kungiyar UKK wanda shi ne har ila yau shugaban jami'ar yammacin Ingila, farfesa Steve West ya ce ya yi maraba da matakan da aka tsara, kuma ya kamata masu ba da ilimi su ci gaba da nuna ci gaba a kan lafiyar kwakwalwar dalibai da kuma yunkurin hana su kashe kan su.

"Shugabannin jami'o'i sun fahimci babban tasirin da kashe kai ke da shi ga iyalai, da kuma al'ummar jami'o'i, da kuma irin asarar da ma su shigar da koken su ka yi" in ji shi.

Lafiyar kwakwalwa

Kafin muhawarar, Ma'aikatar Ilimi ta ce masu ba da ilimi suna da babban aikin kulawa "don sadar da ayyukan ilimi da na kiwo" kuma karin wani doka "zai zama martanin da bai daidaita ba".

Yanzu an shawarci jami’o’i da su tuntubi manyan ‘yan uwa ko abokan arziki idan suna da matukar damuwa game da lafiyar kwakwalwar dalibi – ko da ba tare da izininsu ba.

Tabbabtatun alkaluma na sun nuna cewa dalibai 64 ne suka kashe kansu a Ingila da Wales a cikin zangon karatu na 2019-20, wanda ya yi kasa sosai fiye da yawan jama'a masu kusan shekaru iri daya.

Sai dai iyalan sun ce jami'o'i ba sa bayar da rahoton asalin adadin daliban da suka kashe kansu a shekara - kuma adadin ya fi haka.