BBC Hausa of Sunday, 11 June 2023

Source: BBC

An saki matar da aka ɗaure bisa zargin kashe 'ya'yanta huɗu bayan shekara 20

Kathleen Folbigg ta shafe shekaru 20 a gidan yari Kathleen Folbigg ta shafe shekaru 20 a gidan yari

An saki wata mata da aka taba yi wa lakabi da "Mafi munin kisa a Ostireliya" daga gidan yari bayan wasu sabbin shaidu da suka nuna cewa ba ta kashe 'ya'yanta huɗu ba.

Kathleen Folbigg ta shafe shekaru 20 a gidan yari bayan da wasu alkalai suka yanke hukuncin cewa ita ce ta kashe 'ya'yanta, biyu maza Caleb da Patrick, da kuma mata biyu Sarah da Laura.

Amma a wani bincike da aka gudanar a baya-bayan nan, an ji cewa masana kimiyya sun yadda cewa watakila yaran ba kashe su aka yi ba.

An bayyana shari'ar ta 'yar shekaru 55 da haihuwa a matsayin daya daga cikin manyan kurakuran shari'a a Ostiralia.

An daure Ms Folbigg, wacce a ko da yaushe ta dage kan cewa ba ta da laifi, na tsawon shekaru 25 a shekara ta 2003 saboda kisan uku daga cikin yaran, da kuma kisan gillar danta na fari, Kaleb.

Duka yaran sun mutu ne a tsakanin 1989 zuwa 1999, kuma dukansu na da tsakanin kwanaki 19 zuwa watanni 19 da haihuwa, inda masu gabatar da kara a gaban shari'arta suka yi zargin cewa ta danne su.

Ba a sami dalilin shakku ba a daukaka karan da aka yi a baya da kuma wani bincike na 2019 na daban game da shari'ar, amma ya kara bada ba da nauyi kan tabbataccen shaida na shari'ar ta na farko.

Amma a sabon binciken, wanda alkali mai ritaya Tom Bathurst ya jagoranta, masu gabatar da kara sun yarda cewa bincike kan sauyin kwayoyin halitta ya canza fahimtarsu game da mutuwar yaran.

A ranar Litinin, babban mai shigar da kara na New South Wales Michael Daley ya ce Mista Bathurst ya karkare da cewa akwai shakku kan cewa Ms Folbigg na da laifi.

Sakamakon haka, gwamnan New South Wales ya sanya hannu kan cikakkiyar afuwa, kuma ya ba da umarnin sakin Ms Folbigg daga gidan yari nan take.

"Ya kasance cikin mawuyacin hali na tsawon shekaru 20... Ina yi mata fatan samun kwanciyar hankali," in ji Mista Daley, ya kara da cewa tunaninsa yana tare da mahaifin yaran, Craig Folbigg.

A binciken na baya-bayan nan, lauyoyin Mista Folbigg sun yi nuni da "muhimmin rashin amincewarsu" yadda yara hudu daga iyali daya za su mutu hakan nan kawai kuma duka su na masu kasa da shekaru biyu da haihuwa.

Yafewar da aka yi ma ta ba tare da wani sharadi ba, ba zai soke hukuncin Ms Folbigg ba, in ji Mista Daley. Wannan zai kasance hukuncin ga kotun daukaka kara idan har Mista Bathurst ya yanke shawarar mika karar zuwa gare ta - tsarin da zai iya daukan tsawon shekara guda.

Idan aka soke hukuncin da aka yanke mata, to za ta iya kai karar gwamnati ta nemi a biya ta diyyan miliyoyin daloli.

An kwatanta shari’arta da ta Lindy Chamberlain, wadda a shekarar 1982 aka same ta da laifin kashe ‘yarta mai mako tara da haihuwa, duk da ikirarin da ta yi cewa wani karen daji ne ya dauki jaririn. An biya ta diyyar $1.3m (£690,000, $US 858,000) a 1992 saboda daure t da aka yi bisa kuskure.

Sai dai wasu masu fafutuka sun ce batun Ms Chamberlain, da aka daure na tsawon shekaru uku, ba komai bane idan aka kwatanta da na Ms Folbigg.

"Ba shi yiwuwa a fahimci raunin da aka yi wa Kathleen Folbigg - zafin rasa 'ya'yanta [da kuma] kusan shekaru 20 da ta ke tsare a gidajen yari" in ji lauyanta, Rhanee Rego.

Dole ne doka ta tafi tare da kimiyya

Shari'ar Ms Folbigg na shekara ta 2003 ya ta'allaka ne kan wadansu hujjoji, musamman ma littattafan da suka bayyana gwagwarmayarta yayin da ta zama uwa.

Mijinta na lokacin Mista Folbigg ne ya bai wa ‘yan sanda waɗannan littattafan a shekarar 1999, wanda daga baya ya yadda da cewa matarsa ​​na da laifi. Ma'auratan sun rabu a shaekara ta 2000.

Wadannan rubuce-rubucen - wanda a ciki ta yi ta nuna bakin ciki game da mutuwar 'ya'yanta kuma ta bayyana yadda "laifi abin da ya sme su ya na damu na" - shi ne ya kasance tushen shari'ar mai gabatar da kara.

Sai dai babu wata shaida ta zahiri da ta nuna cewa an danne yaran ko an jikkata su.

Wani yunkuri da wasu abokanta suka jagoranta ya sa aka shigar da kara domin a sake duba hukuncin da aka yanke mata bisa ga binciken da aka yi na binciken kwakwaf.

A binciken na baya-bayan nan, kungiyar likitocin rigakafi sun gano cewa 'ya'yan Ms Folbigg sun yi dfama da wani sauyin kwayoyin halita iri daya - mai suna CALM2 G114R - wanda zai iya sa zuciya ta buga kwatsam.

An kuma gano shaidar cewa ‘ya’yanta maza sun mallaki wani nau’in sauyin kwayan halitta na daban, wanda ke da alaka da farfadiya da ke kamuwa da beraye.

Farfesa Carola Vinuesa, wacce ta jagoranci tawagar binciken daga Jami'ar Kasa ta Ostireliya, ta ce jerin kwayoyin halittar da ba a saba gani ba nan da nan ya bayyana a cikin kwaoyin halittan na Ms Folbigg.

Mun yi gwajin farko kuma mun sami bambance-bambancen kwayoyin halitta wanda hakan ya sa mu shakku sosai … ko da a watan Nuwamba 2018, mun yi tunanin wannan babbar alama ce, idan aka same shi a cikin yaran, ya iya zama sanadi, " ta fada wa BBC.

Farfesa Vinuesa ta ce mutane 134 ne kawai a duk duniya aka taba jin sun yi fama da wannan ciwon zuciyan da sauyin kwayoyin hallita ke jawo shi.

Ta bayyana shawarar yi wa Ms Folbigg afuewa a matsayin "kyakkyawan lokaci" wanda zai iya baiwa sauran matan da ke cikin irin wannan yanayin kwari gwiwa.

“An tuntube mu game da matan da suka rasa ‘ya’yansu, ko kuma wadanda aka zarge su da cutar da su, kuma lamarin ya yi kama da cewa su ma kananan yara ne da ke dauke da wani irin sauyin kwayar halitta mai hadari,” in ji ta

Cibiyar Nazarin Kimiyya ta Ostiraliya ta ce lamarin ya nuna bukatar yin garambawul da zai sa tsarin shari'a ya zama "mai kula da kimiyya", kiran da shima lauyan Ms Folbigg ya jaddada.