BBC Hausa of Thursday, 16 November 2023

Source: BBC

An sauya hoton Ronaldo da na Charlton a kusa da Old Trafford

Hoton alama Hoton alama

An zana wani hoto don tunawa da Sir Bobby Charlton a gefen wani mashaya kusa da filin wasa na Old Trafford na Manchester United.

Shahararren ɗan wasan na Red Devils, wanda ya buga wa ƙungiyar wasanni 758, ya mutu a cikin watan Oktoba yana da shekaru 86 a duniya.

An zana hoton a kan wani hoton tsohon ɗan wasan United Cristiano Ronaldo.

Girmamawar ta zo ne a cikin makon da aka yi bankwana da Sir Bobby a wurin jana'izarsa.

Manyan mutane daga ko'ina cikin duniyar ƙwallon ƙafa sun haɗu da dangin Charlton da abokansa a hidimar ranar Litinin.

An yaba da shi a matsayin ɗaya daga cikin manyan 'yan wasan Ingila, Charlton ya kasance jigo a nasarar da ƙasar ta samu a gasar cin kofin duniya a shekarar 1966.

A cikin shekaru 17 da ya yi yana taka leda a United ya lashe kofunan lig guda uku da na Turai da kuma na FA.

Daga 1958 zuwa 1970 ya buga wa Ingila wasa, inda ya buga wasanni 106, ya kafa tarihi a zura kwallaye 49, ya lashe kofin duniya a 1966, da kuma kyautar Ballon d’Or.