BBC Hausa of Saturday, 10 April 2021

Source: BBC

An umarci shugabannin 'yan sanda a Najeriya game da sauya fasalin tsaro

Sufeton 'yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba Sufeton 'yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba

Sufeton 'yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, ya gana da kwamandojin tsara dabaru na 'yan sanda da suka hada da mataimakin sufeton 'yan sanda da kwamishinonin 'yansanda da mataimakan kwamishinonin 'yan sanda (ayyuka) na yankin kudu maso kudanci da yankin kudu maso gabashin Najeriya.

Taron wani bangare na kokarin da sabon shugaban rundunar 'yan sanda ya ke domin yin nazari a kan barazanar tsaro da ake fuskanta a yankin tare da kirkirar sabbin dabarun 'yan sanda da kuma matakin da za a dauka wajan shawo kan barazanar.

Sufeton 'yan sanda, wanda ya jaddada cewa shiyyoyin kudu maso kudanci da kudu maso gabashin Najeriya na da matukar muhimmanci ga daidaituwar tattalin arziki da ci gaban Najeriya, ya ce ba bu wani aikin leken asiri da aiki da kuma gudanarwa da za a bari don tabbatar da cewa an shawo kan kalubalen tsaro a shiyyoyin biyu.

Game da haka ne ya bada umarni ga kwamandojin a kan su sauya fasalin tsaro na shiyyoyinsu tare da aiki da masu ruwa da tsaki wajan dawo da doka da oda.

Ya kuma umarcesu a kan su aiwatar da matsayar da aka cimma a taron bayan sun koma shiyyoyin nasu musamman bangaren da ya shafi tattara bayanan sirri da tsaron lafiyar al'ummar yankin da dukiyoyinsu.