Gwamnatin Najeriya ta ce ya zuwa yanzu an yi wa 'yan kasar fiye da 250,000 allurar riga-kafin cutar korona.
Wasu alkaluma da Hukumar Lafiya a tamakin farko ta kasar ta fitar sun nuna cewa ya zuwa ranar 23 ga watan Maris, an yi wa mutum 215,277 allurar riga-kafin korona.
Hakan na nufin kashi 5.5 cikin dari na 'yan kasar aka yi w riga-kafin.
Alkaluman sun nuna cewa jihar Lagos ce a sahun gaba a yawan wadanda aka yi wa riga-kafin, inda aka yi wa mutum 58,461, kamar dai yadda ita ce ta fi kowacce jiha yawan wadanda suka kamu da cutar korona tun bayan bullarta a Najeriyar a bara.
Idan muka je arewacin kasar kuwa, jihar Bauchi ce kan gaba, an kuma yi wa mutum 23,827 allurar riga-kafin ta AstraZeneca.
Jihar Jigawa ke biye mata da mutum 20,800.
Sauran jihohin da aka yi riga-kafin sun hada da:
- Adamawa 7,407
- Akwa Ibom 127
- Anambra 132
- Bayelsa 552
- Binuwai 146
- Borno 653
- Cross River 948
- Delta 915
- Ebonyi 77
- Edo 2,645
- Ekiti 1,049
- Enugu 956
- Abuja 8,616
- Gombe 203
- Imo 1,908
- Kaduna 14,572
- Kano 3,903
- Katsina 10,002
- Kwara 12,016
- Nasarawa 6,801
- Ogun 19,257
- Ondo 4,205
- Osun 6,658
- Filato 883
- Rivers 1,951
- Sokoto 98
- Yobe 5,509
- Abia 0
- Zamfara 0
- Kebbi 0
- Niger 0
- Kogi 0
- Taraba 0
- Oyo 0