BBC Hausa of Monday, 17 April 2023

Source: BBC

Ana binciken Barcelona ne don a kassara mu - Laporta

Joan Laporta Joan Laporta

Binciken da ake yi wa Barcelona kan zargin biyan rafli kudi, wata hanya ce aka dauka don a kassara mu in ji shugaba Joan Laporta.

Masu shigar da kara na tuhumar Barcelona da biyan Jose Maria Enriquez Negreira, tsohon mataimakin shugaban raflin Sifaniya kudi (£7.4m).

Barcelona ta ce ta biya kudin ne domin a yi mata bincike kan yadda alkalan ke gudanar da aikinsu, kamar yadda masu horar da kungiyar suka bukata.

''Wannan shine lokaci mafi muni da ake kokarin tagayyara mu,'' in ji Laporta.

''Ina da tabbacin cewar Barcelona ba ta aikata laifin da ya shafi cin hanci a fannin wasa ba. Ina fatan nan gaba gaskiya za ta bayyana.''

''Ina kira ga magoya bayan Barcelona mu ci gaba da hada kai don kare martabar kungiyar da kimar da take da ita a idon duniya a fannin taka leda.''

A watan jiya wata kotu ta tuhumi Barca da laifin cin hanci da cin amana da bayar da bayanan kasuwancin kungiyar na karya.

Itama hukumar kwallon kafar Turai, Uefa ta ce ta fara binciken Barcelona kan lamarin.

Laporta ya ce Barcelona tana ajiye da kididdigar kudin da ta biya tsakanin 2001 zuwa 2018.

''An yi mana wasu daga aikin da mauka bukata, komai yana rubuce. Muna da shaidar takardun aiki da ricitin biyan kudi, komai muna da shi. Ba wani batun cin hanci a ciki.

Laporta ya zargi shugaban La Liga, Javier Tebas da kokarin zubar da kimar Barcelona, ya kuma ce an fi bai wa Real Madrid fifiko, wadda ta ce za ta iya bayar da shaida kan zargin da ake yi wa Barca idan aka bukaci hakan.