BBC Hausa of Friday, 5 May 2023

Source: BBC

Ana muhawara kan kalaman Ganduje na ‘rashin sanin wanda zai miƙa wa mulki’

Abdullahi Umar Ganduje, gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, gwamnan jihar Kano

A jihar Kano da ke arewacin Najeriya, ana taƙaddama a fagen siyasa, bayan gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ce ba shi da tabbaci kan jam’iyyar da zai miƙa wa mulki.

Ya bayyana haka ne duk da kasancewar babbar jam’iyyar adawa ta NNPP ce hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta ayyana a matsayin wadda ta lashe zaɓen gwamnan jihar.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana haka ne, yayin da ya ke ƙaddamar da ɗaya daga cikin hanyoyin da gwamnatinsa ta samar a cikin birnin Kano, inda ya ce Allah ne kaɗai ya san jam’iyyar da zai miƙa wa mulki a ranar 20 ga watan Mayun 2023.

Ya ce “Mun kirkiro manya-manyan ayyuka, mun kammala wasu ba mu kammala wasu ba, wanda ba mu iya kammala su ba muna fatan gwamnati mai zuwa ko gwamnati NNPP ko kuma ta APC, Allah ne kawai Ya sani. Mu na rokon su su cigaba da abin da su ka tarar.’’

Jam'iyyar APC ta gwamna Abdullahi Ganduje dai ta sha kayi ne a zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar ranar 18 ga watan Maris, a zaɓen wanda ya yi zafi tsakanin ƴan takara biyu da ke samun goyon bayan iyayen gida na siyasar jihar.

Tuni dai jam'iyyar APC ta gabatar da ƙorafi domin bin kadin sakamakon zaɓen.

NNPP ta mayar da maryani

To sai dai kalaman da gwamnan na jihar Kano ya furta ba su yi wa jam’iyyar NNPP, wadda ɗan takararta Abba Kabir Yusuf ya lashe zaɓen gwamna daɗi ba, inda ta ce kalaman na gwamna Abdullahi Ganduje ba su dace ba.

Umar Haruna Doguwa shi ne shugaban jam’iyyar na jihar Kano ya ce "idan gwamna Ganduje ya ce bai san wanda zai ba mulki ba, ai gaskiya ya fada, saboda ya rude, dukan ya kai dukan da bai kamata a ce an yi masa irin wannan dukan ba.”

Sai dai a bayanin da ya yi wa BBC, kwamishinan yaɗa labaru na jihar Kano, Muhammad Garba ya ce an yi wa kalaman na gwamna Ganduje bahaguwar fahimta.

A watan Mayun 2023 ne dai Abdullahi Umar Ganduje ke kammala wa’adin mulkinsa na shekara takwas, sai dai ana ta musayar kalamai da kace-na-ce tsakanin APC mai barin gado da kuma NNPP mai shirin karbar mulki, al’amarin da ke tayar da jijiyoyin wuya a fagen siyasar jihar.

A ranar 20 ga watan Maris ne dai Hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC ta ayyana Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Kano.

Abba Kabir, wanda ake yi wa da laƙabi da Abba Gida-gida ya samu nasara ne a kan abokin hamayyarsa na jam'iyyar APC mai mulki Nasiru Yusuf Gawuna.

Gawuna shi ne mataimakin gwmnan jihar Kano mai ci.

Babban jami'in tattara sakamakon zaɓen gwamnan Kano Farfesa Ahmad Doko Ibrahim ya bayyana cewa Abba Kabir ya samu ƙuri'u 1,019,602, yayin da Nasiru Gawuna ya samu ƙuri'u 890,705.