Ana tantama kan makomar kociyan Wolves, Julen Lopetegui, sakamakon yanayin tattalin arzikin kungiyar in ji dan jaridar Sifaniya, Guillem Balague.
Lopetegui, mai shekara 56, ya sanar a makon jiya cewar abu ne mai wahala kungiya ta taka rawar gani a Premier ba tare da jari mai tsoka ba.
Tsohon kociyan tawagar Sifaniya da Real Madrid ya ja ragamar Wolves za ta ci gaba da buga Premier a badi, bayan da kungiyar ta fuskanci barin gasar a bana.
Wolverhampton ta nada kociyan a cikin watan Nuwamba a lokacin da take kasa-kasan teburin babbar gasar tamaula ta Ingila ta bana.
Wolves ta zama ta hudu a Premier League, wadda take ta karshe teburi a Kirsimeti, amma ta samu gurbin ci gaba da buga gasar badi duk da saura wasa uku a kare kakar nan.
Ya ci wasa tara daga 22 da ya ja ragama a kakar nan, inda kungiyar tana ta 13 a teburi kafin a buga wasan karshe na bana.
Lopetegui ya ce shugaban kungiyar Jeff Shi, ya sanar da shi halin da ake ciki, wanda bai sani ba a baya.