Mahukuntan Premier League sun zargi Manchester City da karya dokar kashe kudi fiye da abin da ta samu, wato Financial Fair Play.
An kuma samu kungiyar ta Etihad da laifin ne, bayan wani bincike da aka gudanar mai tsawo kan yadda take hada-hadar kudi.
Cikin binciken ya zakulo cewar City ta karyar dokar ta Financial Fair Play tsakanin kakar 2009-10 zuwa 2017-18.
A shekarar 2020 aka hana City shiga wasannin Zakarun Turai kaka biyu, daga baya kotun daukaka kararrakin wasanni ta duniya ta soke hukuncin.
A lokacin hukumar kwallon kafar Turai, Uefa ta yanke hukunci ne, bayan da ta ce ta samu City da laifin karya dokar Financial Fair Play tsakanin 2012 zuwa 2016.
A wani jawabi da Premier League ta fitar ta ce ta samu City da karya dokar, bayan nazari mai zufi, bayan da ta bukaci sahihin cinikayyar kungiyar.
Cikin bayanan sun hada da kudin shiga da kungiyar ke samu da na tallace-tallace da wanda ta kashe wajen dawainiya.
Cikin karya dokar da kungiyar ta yi har da batun cikakken bayanan albashin mai horar da kungiyar.
Bayanan sun kama daga kakar 2009-10 zuwa 2012-13 a lokacin da Roberto Mancini ke jan ragama.
A bara City ta dauki Premier League na shida tun bayan da rukunin Abu Dhabi ya mallaki kungiyar a 2008.
Manchester City tana ta biyu a teburin Premier League da tazarar maki biyar tsakaninta da Arsenal mai jan ragama.
Ranar Lahadi, City ta yi rashin nasara da ci 1-0 a gidan Tottenham a gasar Premier League, wasan mako na 22.